Xhaka ne sabon kyaftin din Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga David Ornstein
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
Kocin Arsenal Unai Emery ya bai wa dan wasan tsakiya na kungiyar Granit Xhaka mukamin sabon kyaftin din kungiyar na dindindin.
Xhaka ya maye gurbin Laurent Koscielny ne wanda ya koma kungiyar Bordeaux a bana.
Emery ya bayyana daukar wannan matakin ne a ranar Juma'a bayan ya gana da sauran 'yan wasan kungiyar.
Xhaka wanda dan kasar Switzerland ne, mai shekara 27, ya jagoranci kungiyar a wasa shida cikin takwas da ta buga a bana.
Wasan Arsenal na gaba shi ne wasan da za ta kara da Manchester United a Gasar Firimiya ranar Litinin.
Sai dai har yanzu Emery bai yanke shawarar kan wanda zai bai wa mataimakin kyaftin ba tsakanin Alexandre Lacazette da kuma Pierre-Emerick Aubameyang.







