Mohamed Salah: Tawagar Masar ba ta zabe shi gwarzon Fifa ba

Mohammed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Salah ya goge sunan tawagar kwallon Masar daga shafinsa na Twitter
An wallafa

Hukumar kwallon kafar Masar ta bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa da ta yi mata cikakken bayani kan dalilan da ya sanya ba a saka kuri'ar da wakilanta suka kada wa gwarzon kwallon duniya na bana ba.

Hukumar ta ce mukaddashin kocin tawagar Masar Pharoah, Shawky Gharib tare da kyaftin dinsa Ahmed Elmohamady sun kada kuri'unsu ne ga Mohamed Salah.

Sai dai a wasikar da hukumar ta aike wa Fifa ta ce ba ta ga kuri'un da wakilanta suka kada wa Salah ba cikin wadanda aka wallafa sunayensu a shafinta na internet.

Hakan na nuni da cewa ba a kirga kuri'ar wakilan hukumar ba cikin wadanda suka kada kuri'unsu.

Jim kadan bayan ayyana gwarzon dan wasa na bana Mohamed Salah ya goge sunan tawagar kasarsa ta Pharoah daga shafinsa na Twitter.

Abin da ke rubuce a shafin nasa na Twitter yanzu haka shi ne: "Dan wasan Liverpool."

Kazalika ya wallafa a shafinsa na cewa: "Duk abin da suke aikatawa domin sauya kaunar da nake yi wa kasar Masar ba za su samu nasara ba."

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ne ya lashe gwarzon Fifa, inda ya sha gaban dan wasan gaban Juventus Cristiano Ronaldo da kuma na Liverpool Virgil Van Dijk.

A zaben da aka gudanar na shekarar 2018, Mohamed Salah ne ya zo a mataki na uku ya kuma ya lashe kyautar Puskas - kwallon da aka ci mafi kayatarwa.

Kowacce kasa dai an ba ta damar gabatar da mutum uku da za su kada kuri'a, wadanda suka kunshi kocin kungiyar kwallon kafar kasar da kyaftin dinta da kuma jami'in yada labarai guda.

Hukumar kwallon kafar ta Masar dai ta ce Gharib da El-Mohamady Mohamed Salah suka zaba a matsayin zabinsu na farko.

Sai dai wakilin kafofin yada labaran kasar ta Masar Hany Danial Sadio Mane ya zaba a zabinsa na farko da kuma Cristiano Ronaldo a matsayi na biyu, inda ya zabi Salah a matsayi na uku.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Mohamed Salah ke nuna fushinsa ga hukumar kwallon kafar kasarsa ba.

Ko a shekarar bara dan wasan ya yi barazanar daina taka mata leda.