Real Madrid ta haye teburin La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga na bana, bayan da ta doke Osasuna da ci 2-0 a wasan mako na shida da suka fafata a Santiago Bernabeu ranar Laraba.
Hakan ya sa har yanzu Real ba ta yi rashin nasara ba a kakar La Liga ta shekarar nan, inda ta ci fafatawa hudu da canjaras biyu, ta kuma ci kwallo 12 aka zura mata shida a raga.
Koci Zinedine Zidane ya ajiye wasu manyan 'yan wasansa da ya hada da Gareth Bale a shirin da yake na fafatawa da Athletico Madrid a wasan gaba na La Liga da zai fuskanta.
Osasuna ta saka kwazo sosai, sai dai Real ta zura kwallon farko ta hannun Vinicius Junior, kuma na farko da ya ci wa kungiyar a kakar bana.
Madrid ta kara kwallo na biyu ne ta hannun Rodrygo da hakan ya ba ta maki ukun da take bukata a wasan.
Real ta koma ta daya a kan teburi da maki 14, bayan cin wasa hudu da canjaras biyu, za kuma ta ziyarci Atletico Madrid a wasan mako na bakwai a gasar ta La Liga ranar 28 ga watan Satumba..






