Ya ya za ka ji idan Donald Trump ya dauki hoto da kai?

Dalibai sun yi layin karbar abinci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tabichi ya bar aiki a wata makarantar kudi ya koma makarantar sakandare da Keriko inda yawanci 'ya'yan takalawa ne
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Peter Tabichi, dan kasar Kenya wanda ya samu kyautar gwarzon malami na duniya, ya bayyana wa BBC matsalolin da dalibansa ke fama da su, a yayin ake karrama shi a kasar Amurka.

Sunan Tabichi, malamin kimiyyya, kuma dan kungiyar addini ta Franciscan, ya mamaye shafukan sada zumunta a kasar Kenya, bayan an wallafa hotonsa yana gana wa da shugaban Amurka Donald Trump a ranar Litinin.

A ranar Talata, Tabichi ya bude zaman majalisar dokokin Amukda a birnin Washington, da addu'ar Franciscan ta neman zaman lafiya, wanda ya bayyana a matsayin kararama:

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Tabichi ya sheda wa BBC cewa dalibansa a makarantar sakandare ta Keriko, inda yake koyar da darussan lissafi da ilimin fiziks, na yin tafiya mai nisa kafin su je makarantar.

Malamin ya ce yawancin lokuta daliban na zuwa makaranta da yunwa a cikinsu.

Ya kara da cewa daliban su 400 na kuma fama da cinkoso a azujuwa da karancin malamai. Malamai bakwai ne ke koyarwa a makarantar, kuma a kowane aji akwai dalibi 60 zuwa 80.

"A wasu lokutan daliban kan zo makaranta suna jin yunwa ta yadda mutun zai yi saurin gane cewa ba sa mayar da hankalin saosai a kan abin da ake koyar da su," kamar yadda ya bayyana wa BBC.

Peter Tachi a tare da shugaban Amurka Donald Trump a ofishinsa

Asalin hoton, White House

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi kabuncin malamin dan kasar Kenya

"At school we have the challenge of facilities and at times learning becomes very tricky. As teachers we sometimes try as much as possible to be creative to use what's within our reach."

"Matsalar rashin kayan koyarwa na da rudarwa a wasu lokutan. Amma a matsayin malamai mu kan yi kokari da kuma amfani da dabarunmu mu lallaba mu koyar da su da iya abun da ya samu.

Tabichi ya sadaukar da kashi 80 cikin 100 na albashinsa domin taimakon matalauta.

"Ba ni kadadi ke yin wannan aikin ba. Muna da hazikan malamai. Ni a matsayina, na kan yi bakin kokari in yi abin da nake yi tare da sha'awar yin hakan.

"Abin da ke bani kwarin gwiwar shi ne ni irin matsalolin da ni ma na shiga a lokacin da nake tasowa. Kuma ba na so dalibaina su sha irin wahalhalun da na sha a baya."

Kafin komawarsa Kenya, Tabicbi zai gabatar da jawabi a gaban zauren Majalisar Dinkin Duniya, da ke gudana a birnin New York.