Shagon Ali bai ji dadin wasa da Taufik ba

Bayanan bidiyo, Shagon Ali Kanin Bello bai ji dadin Taufik Dogon Ebola ba
An wallafa

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

An dambata a wasanni da dama a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei-Dei Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Tun da fari an sa ran zuwan Sarkin dambe Garkuwan Cindo da Shagon Bahagon 'Yansanda, domin su yi wasa na naira 150,000 a tsakaninsu, amma ba a gansu a gidan ba.

Na kuma tambayi Ali Zuma shugaban kungiyar damben Abuja, kan dalilin rashin zuwan 'yan damben Dei-Dei? inda ya ce ''lokaci ne na damuna, kuma 'yan wasan biyu suna jihar Katsina buga damben mota.''

Ya kara da cewar ''zai yi iya kokarinsa domin ganin ya kawo 'yan wasan su dambata a Abuja, kamar yadda masu sha'awar kallon dambe suka bukata''.

Sai dai an dambata a wasanni da yawa ciki har da wanda Taufik Dogon Ebola ya buge Shagon Ali Kanin Bello.

Wasannin da aka yi kisa a damben safiyar Lahadi a Abuja:

  • Shagon Nura ya buge Shagon Abata Mai
  • Bahagon Dan Jimama ya doke Bahagon Zayyanu
  • Shagon Bahagon Gombe ya yi nasara a kan Garkuwan Shagon Musan Kaduna
  • Shagon Audun Tunga ya buge Shagon Autan Faya
  • Shagon Shagon Lawwalin Gusau ya doke Shagon Fatalwa
  • Dan Mutan Karmu ya buge Dogon Shagon Sisco
  • Dogon Na Sigari ya sumar da Shagon Aya

Wasannin da aka yi canjaras kuwa:

  • Shagon Matawalle da Shagon Alhazai
  • Garkuwan Autan Faya da Autan Mai Takwasara
  • Shagon Buzu da Dogon Na Sigari
  • Bahagon Dan Ali da Shagon Bahagon Dan Fandam
  • Garkuwan Autan Faya da Shagon Shagon Lawwalin Gusau
  • Garkuwan Shagon Alabo da Shagon Bahagon Buma