Arsenal vs Tottenham: Arsenal ta kauce wa abin kunya

Arsenal vs Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan ce karawa ta 186 tsakanin kungiyoyin
An wallafa

Arsenal ta kauce wa abin kunya a filin wasa na Emirate inda ta farke kwallo biyu da Tottenham ta zura mata a wasan mako na hudu na Premier ta bana, inda wasa ya tashi 2-2.

Christian Eriksen ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal din a minti na 10 bayan Bernd Leno ya dawo masa da kwallon da Lamela ya dada masa.

A minti na 40 kuma Harry Kane ya kara ta biyu a bugun fanareti bayan Xhaka ya bige Son a cikin yadi na 18 din Arsenal.

Ana daf da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma Lacazette ya farke kwallon farko. Pepe ne ya ba shi kwallon shi kuwa ya take ta kuma ya shimfida ta raga.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya farke ta biyun a minti na 71 bayan Guendouzi ya cilla masa kwallon ta saman 'yan bayan Tottenham, cikin sauki ya taba ta kuma ta zurare ta gefen Lloris zuwa raga.

Ganin cewa kungiyoyin biyu 'yan arewacin birnin Landan ne, ana yi wa wasan lakabi da North London Derby wato wasan hamayyar arewacin Landan.

Arsenal ta matsa zuwa mataki na 5 da maki bakwai yayin da Tottenham ta matso zuwa mataki na 9 da maki biyar.

Game da wasan

Mauricio Pochettino da Unai Emery

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mauricio Pochettino na Tottenham da Unai Emery na Arsenal

Sau biyu kacal Tottenham ta taba cin wasan Premier a gidan Arsenal a cikin wasa 27 da suka gwabza - 1993 da kuma 2010

Tottenham din ce ta ci 2-0 a Emirate a Disambar da ya gabata a wasan League Cup.

A dukkanin haduwa da suka yi sau daya Tottenham ta ci wasa a gidan Arsenal sau biyu a jere - a 1925 zuwa 1926

An fi zura kwallaye ta hanyar fanareti a wasa tsakanin Arsenal da Tottenham da kuma wasa tsakanin Everton da Newcastle United.

Wannan shi ne wasan hamayyar arewacin Landan na 186, inda Arsenal ta yi nasara sau 77 Tottenham kuma ta ci 58 kuma aka yi canjaras sau 51.

Har wa yau

Arsenal ta ci wasanni (60) na Premier League a watan Satumba sannan kuma suna da hasashen cin wasa (kashi 61%) sama da kowace kungiya a Premier.

Tottenham ba ta yi nasara a wasan waje ba a Premier cikin bakwai da ta buga, wannan shi ne tarihi mafi muni tun Dismabar 2011 zuwa Afrilun 2012.

Everton vs Wolves

Wasa daya ne kawai aka yi a yau bayan na Arsenal da Tottenham, shi ne tsakanin Everton da Wolves a filin wasa na Goodison Park - Everton 3-2 Wolves.

Sakamakon wasannin Asabar

Southampton 1-1 Manchester United

Chelsea 2- 2 Sheffield United

Crystal Palace 1-0 Aston Villa

Leicester City 3 - 1 AFC Bournemouth

Manchester City 4 - 0 Brighton & Hove Albion

Newcastle United 1 - 0 Watford

West Ham United 2 - 0 Norwich City

Burnley 0 - 3 Liverpool