Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta dauki Nicolas Pepe
Arsenal ta kammala daukar dan wasan tawagar kwallon kafar Ivory Coast, Nicolas Pepe daga Lille ta Faransa.
Gunners din ta dauki dan wasan a matsayin mafi tsada a tarihi kan fam miliyan 72.
Mai shekara 24, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a Emirates, bayan da likitoci suka duba lafiyarsa ranar Talata.
Pepe mai buga gefe daga gaba ya ci kwallo 35 a wasa 74 da ya yi a Lille, wadda ta dauko shi daga Angers a 2017.
Dan kwallon ya zama na hudu mafi tsada da aka saya a Premier bayan 'yan wasan Manchester United, Paul Pogba kan fam miliyan 89 da Romelu Lukaku kan fam miliyan 75 da kuma Virgil van Dijk na Liverpool kan fam miliyan 75.
A kakar da aka kammala ta 2018-19 a Ligue 1, dan kwallon Paris St Germain, Kylian Mbappe ne ya dara Pepe cin kwallo da taimakawa a zura a raga.
Arsenal ta bai wa dan wasan riga mai lamba 19.