Firimiyar 2019-2020: Man United za ta fara karawa da Chelsea

An wallafa

An bayyana jadawalin gasar Firimiya ta Ingila ta kakar 2019-2020 inda Manchester United za ta karbi bakuncin Chelsea a ranar Lahadi 11 ga watan Agusta.

Za a bude gasar ne a ranar Juma'a 9 ga watan Agusta, inda Liverpool za ta kece raini da Norwich City wacce ta dawo Firimiya a bana bayan lashe gasar Championship.

Masu rike da kanbun gasar Manchester City za su fara na su wasan ne a West Ham United.

Aston Villa da Sheffield United, wadanda duka sabbi ne a gasar, za su fafata da Tottenham da kuma Bournemouth.

Arsenal, wacce ta kare a mataki na biyar a kakar da ta gabata, za ta yi tattaki ne zuwa Newcastle domin buga wasanta na farko.

Latsa nan domin karanta cikakken jadawalin na wata-wata.