Cristiano Ronaldo ya isa Juventus don a gwada lafiyarsa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Cristiano Ronaldo ya isa Juventus domin a gwada lafiyarsa bayan da ya amince ya koma kulob din a kan fam miliyan 99.2.

A ranar Talata ne dan kwallon, wanda ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Real Madrid, ya amince ya koma Juventus, inda zai sa hannu kan kwantiragin shekara hudu.

Hakan ya sa ya kasance cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.

Ronaldo ya lashe kofin zakarun Turai sau hudu da kuma kofin La Liga biyu a Madrid.

Juventus ta wallafa hotunan dan kwallo, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or sau biyar, a lokacin da ake gwada lafiyarsa.

Yana bacci yana karbar miliyan 12

A rana Ronaldo zai karbi kusan fan 73,000, kwatankwacin naira kusan miliyan 36.

Ronaldo wanda ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Real Madrid, yana cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.

Yana bayan Neymar da Mbappe na PSG da kuma Coutinho na Barcelona.

A mako Ronaldo zai karbi sama da fan miliyan £510,483 wato sama da naira miliyan 258.

Duk awa daya zai karbi fan 3,038 wato kusan naira miliyan daya da rabi, yayin da a duk minti daya zai karbi £50.64 wato sama da naira dubu 24.

Hakan na nufin kimanin awanni takwas da Ronaldo zai shafe yana bacci a dare zai karbi sama da fan 24,000 kwatankwacin sama da naira miliyan 12.

Bajintar Ronaldo

  • Ronaldo ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Madrid
  • Ya ci kwallaye 105 a gasar Zakarun Turai
  • Kwallaye 311 a gasar La Liga
  • Kofi 16 a Real Madrid da suka hada da La liga biyu da Zakarun Turai hudu da gasar duniya ta kungiyoyi
  • Ya ci kwallaye uku-uku (hat-tricks) shi kadai sau 44, kuma sau 34 a La Liga
  • Sau takwas yana cin kwallaye fiye da hudu a Real Madrid
  • Ya taba cin kwallaye 61 a kakar 2015-16 a dukkanin wasanin da ya buga
  • Hakan ya hada da kwallaye 48 a La Liga
  • Kwallaye 659 ya ci a rayuwarsa - biyar a Sporting Lisbon, da 118 a Manchester United da 451 a Real Madrid da 85 a Portugal
  • Sau biyar yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or