Cristiano Ronaldo ya isa Juventus don a gwada lafiyarsa

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya isa Juventus domin a gwada lafiyarsa bayan da ya amince ya koma kulob din a kan fam miliyan 99.2.
A ranar Talata ne dan kwallon, wanda ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Real Madrid, ya amince ya koma Juventus, inda zai sa hannu kan kwantiragin shekara hudu.
Hakan ya sa ya kasance cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.
Ronaldo ya lashe kofin zakarun Turai sau hudu da kuma kofin La Liga biyu a Madrid.
Juventus ta wallafa hotunan dan kwallo, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or sau biyar, a lokacin da ake gwada lafiyarsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Yana bacci yana karbar miliyan 12
A rana Ronaldo zai karbi kusan fan 73,000, kwatankwacin naira kusan miliyan 36.
Ronaldo wanda ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Real Madrid, yana cikin 'yan wasa hudu da suka fi kowa tsada a duniya.
Yana bayan Neymar da Mbappe na PSG da kuma Coutinho na Barcelona.
A mako Ronaldo zai karbi sama da fan miliyan £510,483 wato sama da naira miliyan 258.
Duk awa daya zai karbi fan 3,038 wato kusan naira miliyan daya da rabi, yayin da a duk minti daya zai karbi £50.64 wato sama da naira dubu 24.
Hakan na nufin kimanin awanni takwas da Ronaldo zai shafe yana bacci a dare zai karbi sama da fan 24,000 kwatankwacin sama da naira miliyan 12.
Bajintar Ronaldo
- Ronaldo ya ci kwallaye 450 a wasanni 438 a Madrid
- Ya ci kwallaye 105 a gasar Zakarun Turai
- Kwallaye 311 a gasar La Liga
- Kofi 16 a Real Madrid da suka hada da La liga biyu da Zakarun Turai hudu da gasar duniya ta kungiyoyi
- Ya ci kwallaye uku-uku (hat-tricks) shi kadai sau 44, kuma sau 34 a La Liga
- Sau takwas yana cin kwallaye fiye da hudu a Real Madrid
- Ya taba cin kwallaye 61 a kakar 2015-16 a dukkanin wasanin da ya buga
- Hakan ya hada da kwallaye 48 a La Liga
- Kwallaye 659 ya ci a rayuwarsa - biyar a Sporting Lisbon, da 118 a Manchester United da 451 a Real Madrid da 85 a Portugal
- Sau biyar yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Ballon d'Or











