Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon dan tseren duniya Bolt zai taka leda a Old Trafford
Tsohon zakaran tseren duniya Usain Bolt wanda ya yi ritaya zai yi wasan kwallon kafa a filin kungiyar da yake kauna Manchester United, Old Trafford.
Bolta wanda sau takwas yana cin lambar zinare a gasar Olympic zai jagoranci wasu fitattu ne ire-irensa da kuma 'yan kwallon kafa a matsayin kyaftin dinsu, a wasan neman tallafi na Asusun yara na majalisar din kin duniya, Unicef, da ake yi, Soccer Aid, ranar 10 ga watan Yuni.
Dan tseren na Jamaica, ya ce tun ainahi burinsa shi ne ya zama kwararren dan kwallon kafa. Saboda haka wannan dama ta yin wasa tare da wasu daga cikin tsoffin fitattun 'yan wasan ba karamin abu ba ne.
Mawaki kuma dan fim Robbie Williams shi ne zai zama kyaftin din daya tawagar, Ingila a wasan kwallon na Unicef.
Daman Usain Bolt ya taba yin maganar cewa yana son ya shiga wasan kwallon kafa na kwararru bayan ya yi ritaya daga tsere a shekarar da ta wuce.
Wasan tamolar na neman tallafi wanda za a yi a Old Trafford zai hada shahararru da tsoffin gwanayen 'yan wasan kwallon kafa na duniya, inda za su taka leda tare.
Ana wasan ne duk bayan shekara biyu, kuma tun bayan da aka fara shi a shekara ta 2006, an tara fam miliyan 24.