Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An jaddada hana Atletico sayen 'yan wasa
An wallafa
Atletico Madrid ba za ta sayi yan wasa ba a bana, bayan da kotun daukaka karar wasanni ta tabbatar mata da hukuncin da aka yanke tun farko.
Hukumar kwallon kafa ta duniya ce ta dakatar da ita shekara biyu daga daukar 'yan wasa zuwa kaka biyu, bayan da aka same ta da laifin karya ka'idar hukumar a Yunin 2016.
A watan Disamba ne kotun ta rage hukuncin da aka yi wa Real Madrid zuwa shekara daya, wadda aka dakatar tare da Atletico.
Atletico Madrid ta ce 'hukuncin babu adalci ya kuma kawo nakasu ga kungiyar.
Sai dai kuma kotun ta rage kudin tarar da aka ci kungiyar daga fam 719,793 zuwa 439,873.