CHAN: Ghana za ta kara da Nigeria

Magoya bayan Ghana na sa ran doke Nigeria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Ghana na sa ran doke Nigeria
An wallafa

Ghana za ta kara da Nigeria a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika ta 'yan wasa masu buga kwallo a gida bayan da ta yi nasarar 1-0 kan DR Congo.

Kungiyar Black Stars din ta samu nasarar ne sakamakon fenaritin da Kwabena Adusei ya buga a minti na 69 da take wasa a filin Free State da ke garin Bloemfontein.

A daya wasan daf da na kusa da na karshen da aka buga ranar Lahadi, Libya ta doke Gabon 4-2 da fenariti bayaan da aka kammala wasa da karin lokaci 1-1.

Yanzu haka dai Libya za ta kara da Zimbabwe, wacce ta casa Mali ranar Asabar.

Ranar Laraba 29 ga Janairu za a gudanar da wasannin kusa da na karshen.