Ku San Malamanku tare da Malam Modibbo Tukur
Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Muhammad Mahmud Modibbo Tukur Gombe.
An haifi malamin a shekarar 1966 a garin Gombe kuma ya fara karatu a hannun mahaifinsa Modibbo Tukur, wanda shi ma malami ne.
A shekarar 1973 zuwa 74 mahaifinsa ya kai su makarantar Islamiyya a garin Manzo tare da 'yan uwansa.
A hirasa da BBC, malam Muhammad Mahmud ya bayyana cewa ya fara karatun allo da Alkura'ni mai girma lokacin yana da shekara bakwai.
Neman ilimi
"Na yi karatun Alkur'ani a gaban mahaifina, amma a wasu lokutan idan almajirai suka yi masa yawa yakan hada mu da wasu malamai su rika lura da mu,'' in ji shi.
''Shehu Manzo babban malami ne kuma abokin mahaifinmu ne da suke aikin da'awa tare, inda daga bisani Shehu Ibrahim Khaulaha y aba shi izinin kafa makarantar Islamaiyyar a nan garin Gombe."
Bayan bullo da shirin nan na bayar da ilimin firamare kyauta da ake kira UPE lokacin mulkin Obasonjo a shekarar 1976, malamin ya ce shi da yayansa aka kai makarantar firamare da ake kira Jan kai, inda suka fara karatu har ya zuwa shekarar 1981 lokacin da suka kammala firamare.
Malam Muhammadu Modibbo ya ci gaba da karatun addini na cikin gida tun daga Kawa'idi, da Ishimawi da Iziyya zuwa Risala, da su Kurdabi da Hadisi da kuma Taudihi wanda ya ce duk a gaban mahaifinsu suka koya.
Kazalika, mahaifin nasu ya sake hada su da wasu malamai daban don ci gaba da daukar karatu.
"Malaman sun hada da Alhaji Umaru Gojude wanda limamin masallaci ne, akwai kuma Alhaji Bashir Modibbo Jobbo, sai malam Ibrahim Khalil.
Abin bakin cikin da na farin ciki
Malamin ya kuma ce babban abin bakin cikin da ba zai taba mantawa da shi ba shi ne mutuwar mahaifinsa wanda shi ne ke rike da kowa.
"Tunanin rana tsaka muka rasa shi, yadda abubuwa za su mike bayan rasuwarsa ba karamin tashin hankali ba ne a gare mu. Lallai wannan babban abin bakin ciki ne da ba zan manta da shi ba.''
Amma kuma, babu abin da malamin ya ce ke dadada masa rai irin ya ga matasa suna karatu, suna kuma sana'ar da za su dogara da kan su.
Haka nan in ji malamin, samun cikawa da imani na cikin manyan burikan da yake da su a rayuwa.
Malamin ya kuma ce yana matukar son abincin nan na Bare-bari wato burabusko.
Ta bangaren iyali kuma, yana da mata, da 'ya'ya mata bakwai da maza biyar.












