Ku San Malamanku tare da Sheik Usman Babaliman; Alkali Omo
Malamin wanda shi ne shugaban bangaren da'awa da wa'azi na kungiyar Jama'atu Nasril Islam, ya shaida wa BBC cewa a aikinsa na alkalanci ya yi shari'u da yawa masu wuya a Gombe da kuma Misau, musamman ma a Misau. Daga ciki yana iya tuna wadda ya yi da ta shafi Dan-madamin Misau.
''Wadda ta shahara sosai don Dan-madamin Misau mutum ne mai jin kansa Allah Ya karbe shi, ya rasu daga baya, don an ce ba a ma kiransa a kotu. Na ce a'a ni a Misau ba wanda ba zan kira ba sai Sarkin Misau. Sarkin Misau ne idan abu ya shafe shi na shari'a zan je fada in saurari jawabinsa in ya shafi sheda, in wani ya ce shi ne shedansa, in karbi bayaninsa amma duk kowa daga baya zan kira shi kotu kuma zai zo,'' in ji shi.
Ya kara bayani da cewa, ''Da na aika masa sammaci ya ki karba ya ce sai dai a aika ma lauyansa.
''Da bai amsa kiran kotu ba, a ranar da muka zauna shari'ar sai aka ce ai ya zo ya ce zai yi bankwana zai tafi Abuja.
To da na fito na bada umarni a tsare shi.''
''To wannan shari'a ta ja hankulan mutanen Misau sosai ba wanda bai sani ba wasu ma a sanadin shari'ar suka san ni, cewar wani dan Gombe ne ya zo ya tsare Dan-madami,'' in ji shi.
Tarihin Rayuwarsa
A hirarsa da BBC, malamin ya ce an haife shi a garin Gombe-Abba da ke jihar Gombe a yanzu a ranar 31 ga watan Disamba a 1948, amma a lokacin a tsohuwar jihar Bauchi
Ya ce ya fara karatu na Islamiyya a wajen mahaifinsa, wanda a lokacin shi ne limamin Gombe, Mallam Muhammadu.
''A wajensa na yi karatun Al'Ƙur'ani na fara littattafan ilimi, har lokacin da na dawo Gombe a 1967 wajen kakannina,'' in ji shi.
Ya kara da cewa kakanninsa su ne limamin Gombe Abdullahi sannan kuma da Alkalin Pindiga, Alkali Ahmadu wanda ya ce ya yi ritaya daga Pindiga.
''A nan ne na rika karatun littattafai su fikihu da hadisai da Kur'ani da tafsiri, har zuwa 1971 da na tafi Kano,'' in ji malamin.
Ya je Kano ne domin ya shiga makarantar School for Higher Islamic Studies, wato Aliya domin karatun Grade II.
A 1972 ya ce ya sake komawa domin karatun difiloma, inda ya shiga Kwalejin Abdullahi Bayero, wato Jami'ar Bayero a yanzu, wadda a lokacin tana karkashin Jami'ar Ahmadu Bello, ABU Zaria.
Bayan shekara uku ya kammala a 1978, inda ya samu sakamako mafi daraja (distinction), da kuma kyautuka na yabo.
Bayan ya koma gida ne sai ya kama aiki da Ma'aikatar Shari'a ta jihar Bauchi a matsayin mataimakin magatakarda, wato rijistara.
Daga nan ne kuma ya sake komawa Kano domin karatun digiri, wanda a lokacin kwalejin ta Abdullahi Bayero ta zama, jami'a wato Bayero University, BUK, inda bayan shekara uku, a 1982 ya gana karatun digirinsa.
A wannan lokacin ma ya samu sakamako mafi kyau, inda ya zama gwarzan dalibi na sashensu da kuma na tsangayar gaba daya.
Bayan da aka kirkiro Jihar Gombe daga Bauchi a 1996, sai ya zama Khadi a kotun daukaka kara ta Shari'a.
Yana wannan matsayi ne har zuwa 2011 ya zama Grand Khadi, wanda bayan shekara biyu a 2013 kenan watan Disamba ya yi ritaya.
Gwagwarmayar Karatu
Mahaifina shi ne babban mai tasiri a rayuwata kasancewar shi ne ya dora ni a wannan hanya ta karatu da ilimi, sai lokacin da na koma Gombe, wajen Alkali Ahmadu, wanda babban malami ne, wanda da shi ne ke tafsiri a kofar gidan sarki.
''Sannan kuma Kano da na je a gidan Sheikh Nasiru Kabara na zauna wanda shahararren malami a Najeriya wanda ba irinsa a lokacin a wajensa na zauna, kuma makarantar da na shiga ta Aliya din tasa ce shi ya kafa ta, da kuma tasirin karance-karancensa na gida,'' in ji shi
Yadda ya samu suna ''Alkali Omo''
A shekara ta 1984 aka mayar da shi Kumo aiki, inda a lokacin ya tarar ba a barin mutane su je sauraren sharia. Sai ya ce a'a ai shari'a darasi ce ya bayar da dama a rika zuwa ana sauraren abin da yake sa kotun ta cika makil.
To kuma a duk ranar Alhamis ranar kasuwa, sai 'yan kasuwa su rika kasa kaya a kan titi suna toshe hanya. Ganin haka sai ya je wajen babban jami'in 'yan-sanda na Kumo a lokacin wanda Hamma Misau ne DPO a lokacin, sai ya ba shi 'yan-sanda ya rika bi a bude hanya, duk wanda bai kwashe kayansa ba, ya sa a kama shi a kai shi caji ofis.
''Dole mu bude hanya. To daga nan aka ce lalle an samu 'Omo mai wanke Kumo'. To daga nan ne aka sa min wannan sunan,'' in ji shi.
Babban burinsa a rayuwa yanzu
Ya ce babban burinsa a rayuwa yanzu tun da ya yi ritaya shi ne ya mutu da imani. Ya fita daga aiki bai tuna wani hakki da suka danne ba, wanda suke tsoro kar a tono shi. Saboda haka ya gode wa Allah. Idan akwai abin da suka yi wanda ba su sani ba bisa kuskure ''muna fatan Allah Ya gafarta mana,'' in ji shi
Iyali
Malamin ya ce, ''To mata a yanzu dai ina da biyu ne, biyu ne nake da su da 'ya'ya kuma ko goma sha bakwai ne.''












