Lafiya Zinariya: Yadda ayyukan yau da kullum ke shafar lafiyar mata

Bayanan sautiShirin Lafiya Zinariya; tattaunawa kan matukar gajiya da galabaita ga mata
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:

Ayyukan da mata ke yi wadanda suka hada da hidimar gida, aikin ofis, kasuwanci da dai sauransu, kan galabaitar da su a wasu lokutan.

Yanayin da idan ba a dauki matakan da suka dace ba, ta kan kai ga hakan ya taba lafiyar kwakwalwa ko na jiki da mu'amala da iyali ko makusantansu.

Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS, ta raba alamomin galabaita gida uku, wadanda suka shafi jiki da wadanda suka shafi kwakwalwa da kuma wadanda ke sauya yadda mutum ke mu'amala.

  • Alamomin da suka shafi jiki sun hada da ciwon kai da jiri da ciwon jiki da matsalolin da suka shafi ciki da ciwon kirji da bugawar zuciya da kuma matsalolin da suka shafi jima'i
  • Ta bangaren kwakwalwa kuwa alamomin da mutum zai iya gani sun hada da rashin samun nutsuwa da yawan damuwa da yawan mantuwa da wahala wajen yanke shawara da kuma jin cewa abubuwa sun sha kanka
  • Su kuwa alamomin da suka shafi mu'amala sun kunshi hantara, saurin jin haushi da yawan barci ko karancinsa, cin abinci da yawa ko cin kadan, gujewa wasu mutane ko wurare da kuma shan barasa ko taba sigari

Hukumar ta kuma bayar da misalan wasu abubuwan da ta ce za su iya janyo mutum ya galabaita.

Wadanda suka hada da fuskantar matsin lamba a wajen aiki ko kuma rashin aikinyi ko kuma rayuwa bayan yin ritaya.

Haka kuma iyali su ma za su iya zama wani dalili na galabaitar mutum, wato idan dangantaka ta yi tsami ko sakin aure ko kuma kula da wani.

Matsalolin da suka shafi kudi suma suna daga cikin dalilan da ke sa wa a galabaita.

Kamar misali idan bashi ya y iwa mutum yawa ko bukatu suka yi yawa.

Kiwon lafiya da suka hada da ciwo ko mutuwar wani makusanci su ma kan jefa mutum cikin yanayi na galabaita.

Hukumar ta kuma kara da cewa wasu muhimman abubuwa a rayuwar mutum suma ka iya zama dalilai ko samun karuwa.

Sai dai hukumar ta bayar da shawarar cewa yana da kyau idan mutum yana cikin wannan hali ya tattauna da wani, don hakan zai taimaka.