Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Sirrin gyaran fata ba tare da shafe-shafe ba
Latsa hoton da ke sama domin sauraren ashirin:
Kwararrun likitocin fata sun bayar da shawara kan wasu hanyoyi da mata za su bi domin kyautata fatarsu ba tare da sun sauya launinsu ba.
Wasu daga cikin illolin da amfani da kayan shafe-shafe ke haifarwa sun hada da ciwon koda da hawan jini da ciwon suga da kuma cutar daji ta fata.
A cewar masana, fata halitta ce da ke daukar duk abin da aka shafa mata zuwa cikin mutum, ciki har da koda da kwakwalwa.
Yawancin mayukan shafe-shafen da ke sanya fata fari suna dauke da sinadarai masu guba, kamar su mercury da hydroquinone da sauransu.
Mata bakaken fata musamman mazauna nahiyar Afrika na amfani da mayuka da sabulai da wasu hanyoyi don sauya fatarsu zuwa fara.
Irin illolin da ke tattare da shafe-shafen ne ya sa wasu gwamnatocin kasashe a nahiyar, suka haramta shiga da wadannan kayan shafe-shafe kasashensu.
Kasashen sun hada da Tanzania da Afrika ta Kudu da Najeriya da Kenya da Ivory Coast da kuma Ghana.
Amma kusan za a iya cewa wannan doka ba ta kawo wani sauyi na azo a gani ba.
Domin ana ci gaba da sayar da kayan shafe-shafen a shaguna da kasuwanni, wasu wuraren kuma a bayan fage.
Mata a wasu kasashen yankin Asia, kamar a kasar Indiya suna amfani da kayan shafe-shafen duk kuwa da hadarin da ke tattare da hakan.