Ku san Malamanku tare da Sheikh Abubakar Kyari Muhammed

An wallafa

Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Kyari Muhammed, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata sura a Al-Ƙur'ani.

Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC cikin shirin nan mai taken "Ku San Malamanku".

Ya ce surar da ta fi ba shi wuya ita ce Suratul An'am, wadda ita ce sura ta shida daga sama a cikin littafi mai tsarki.

Sai dai ya ce Allah ya sahale masa ayar da ta fi bai wa mafi yawan mahaddatan Kur'ani mai girma wuya, wato ayar rabon gado ta .... Yusi kumullahu, wadda take a cikin Suratul Nisa'i.

Malamin ya ce babu abin da yake faranta masa rai a rayuwa irin ya ga mutum ya musulunta kuma ya yi riko da addinin yadda ya kamata.

Abin da kuma ya fi bakanta masa rai shi ne "yadda mutane ke wasa da ilimi, yadda ake ba da fatawa bisa kuskure ba tare da damuwa kan abin da zai faru ba".

A lokuta da dama malamai kan yi fatawoyin da suke ingiza mutane su je su rika yi wa shugabanni tawaye ko wani abu mai kama da haka.

Tarihin rayuwarsa

Daga sunansa, mai karatu zai iya hasashen cewa Sheikh Abubakar Kyari Muhammad ya fito ne daga Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

An haifi malamin ne a shekarar 1963, inda ya tashi a Borno kuma ya fara karatu a hannun wani malami da ake kira Malam Danjuma, wanda yake koya wa Sheikh harufan Larabci da Hausa.

Idan ya koma gida sai iyayensa su koya masa abin da ya koya da harshen Kanuri.

Daga baya mahaifinsa ya kai shi wata makarantar allo ta wani malami abokinsa, wanda dan asalin Fataskum ne amma yana zaune a Maiduguri.

Ya hadu da manyan malamai irinsu Baba Sayinna da irinsu Malam Babagana, "kafin daga bisani a ba ni damar komawa makarantar Sheikh Muhammad Abba Aji".

Ya ce sun karanta littatafai da yawa a makarantar irinsu Muwadda Malik da Fiqhussuna da dai sauransu.

Malamin ya ce iyayensa ba su sa shi makarantar boko ba amma shi ya kai kansa wajen da ake koyar da bokon, kuma har yanzu yana cin gajiyar karatun.

Daga baya ya koma Kano tare da wani uban gidansa a shekarun 1980, ya kuma shiga makarantar S.A.S. da ke Kano inda shi ma ya samu kammala karatunsa a nan.

Ya yi jarrabawar wani zauren koyarwa da ake kira daura wadda ake kai mutum Saudiyya idan ya yi nasara, wadda Jami'ar Madina ke shiryawa.

"A lokacin na samu nasarar cin jarrabawar kuma Dr Aminundeen Abubakar ne ya yi alfahari da hakan a 1992," in ji shi.

'A 1994 na yi Aure'

Malamin ya ce a shekarar 1994 ya yi aure, kuma Allah ya azurta shi da 'ya mace, amma kuma daga baya Ya amshi kyautarsa.

Amma a yanzu yana da mata ɗaya da kuma ɗa guda.

Shehin malamin ya ce babban burinsa kamar na kowanne Musulmi ne na fatan a cika lafiya.

'Abin da aka fi tambaya ta'

Sheikh Abubakar Kyari Muhammed ya ce an fi yi masa tambaya a kan sihiri, ko a karatun da yake yi ko kuma ta hanyar tura masa wasika.

Mutane suna yawan magana a kan an yi musu sihiri, abin da yake janyo haka kuma shi ne rashin tawakkali.

Ya ce: "Yanzu baki ya yi yawa mutane in suka ga abin da ya yi musu kyau ba sa cewa Tabarakallah sai kaga da sun yi magana sun ɓata abin."

Hakan ya janyo Malamin yake fitar da kananan bidiyo a intanet domin wayar da kan mutane da kuma nuna musu illar kambun baka.

Ya ce suna koyar da addu'o'in da mutane za su rika karantawa domin kare kansu da iyalansu daga irin wadannan matsaloli.