Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shekara saba'in na mulkin Sarauniya: Dan Najeriya da ya nemi zama ma'aikacin Sarauniyar Ingila Elizabeth
A cikin jerin wasikun da muke samu daga Afrika, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani ta yi duba ne dangane da ko ana murnar cikar Sarauniyar Ingila shekara 70 kan karagar mulki a Najeriya.
Najeriya ce ƙasa mafi girma da Ingila ta mulka a zamanin mulkin mallaka kuma ƙasa ce mai tasiri a cikin ƙasashen rainon Ingila.
"Abu mai muhimmanci a gare ni shi ne har yanzu sarautar bata mutu ba," in ji Chuka Mordi, wanda ya nemi ya zama dogarin Sarauniya shekarun baya da suka wuce bayan ya tafi London daga Benin da ke kudancin Najeriya domin ya yi karatu.
A yanzu da yake cikin shekarunsa na 50, wanda kuma ya kammala King's College da ke London, shugaban wani kamfanin zuba jari ne a Legas, kuma ya yi waiwaye kan neman aikin da ya yi da kuma takardar ƙin amincewa da ya samu daga fadar Sarauniya.
"Ina tunanin na yi wani abu na shashanci da na tambayi albashi mai gwaɓi sakamakon irin cancantar da na yi fiye da kima," in ji shi.
Ijay Uwakwe-Okoronkwo, wadda mai aikin tuntuɓa ce a ɓangaren ilimi a Abuja, ta saka hoton Sarauniya Elizabeth a matsayin hotonta na Whatsapp.
"Abu ne mai kyau da na ga Sarauniya a cikin ƙoshin lafiya," in ji shi.
An haifi Ms Uwakwe-Okoronkwo shekara 50 da suka gabata a lokacin da iyayenta ke karatu a Ingila. Ta dawo da iyalanta Najeriya a cikin shekarun 1970 kuma tun daga lokacin ta koma ƙasar haihuwarta ne ba sosai ba domin hutu.
"Bari mu gani, na samu tagomashi sakamakon haihuwata da aka yi a Ingila," in ji ta. " Ina da fasfo ɗin Birtaniya, a wannan lokacin da muke samun matsalolin siyasa a Najeriya, babu wanda ya damu.
Muna fama da matsalolin wuta da ƴan bindiga, ana yin garkuwa da mutane kuma kuma ana maganar cika shekara 70?"
Mutanen Duke town da ke kudancin Najeriya a birnin Calabar na da alaƙa mai ƙarfi da iyalan gidan sarauta, wanda wannan alaƙa ta samo asali ne tun daga ƙarni na 19 a lokacin da ɗaya daga cikin sarakan yankin ya shiga kasuwanci da Sarauniya Victoria.
Akwai kwafi na takardun kasuwancin da aka yi a tsakanin Sarauniya Victoria da Sarki Eyamba da Sarki Honesty waɗanda suna nan ajiye a gidan tarihi na Calabar, wanda gidan tarihin a baya ya kasance hedikwatar gudanarwa ta Birtaniya a kudancin Najeriya.
Kuma a kodayaushe akwai kujerar da babu kowa da aka ajiye wa sarki ko sarauniyar Birtaniya idan za a yi naɗin sarki a Calabar wanda aka fi sani da Obong.
Sai dai batun cika shekara 70 ya kasance wani abu da ya yi nisa da zukatan mutane.
"A gaskiya, babu wasu shirye-shirye," in ji Charles Effion Offiong-Obo, wanda shi ma babba ne a garin Duke.
"Najeriya na da abubuwan da take fama da su. Muna cikin shirin sauya sabuwar gwamnati ba da daɗewa ba. An kaɗa gangar siyasa kuma jama'a sun zaƙu su ga abin da zai biyo baya kuma ba su cika mayar da hankali kan nishaɗi ba," in ji Charles, inda yake nufin jam'iyyun da ke zaɓen waɗanda ke takarar shugabancin ƙasa a zaɓen baɗi.
Ko dai ƴan Najeriya sun damu ko ba su damu da batun cikar Sarauniya shekara 70 kan karagar mulki ba, ƙarsarmu na da alaƙa mai ƙarfi da ita.
Birtaniya tana da ƙasashe 54 waɗanda ta rena. An kafa ƙungiyar ƙasashen renon Ingila a 1931, ƙungiya ce da aka kafa a zamanin mulkin mallakar Birtaniya.
Shiga cikin ƙungiyar zaɓi ne, akwai wasu ƙasashe masu ƴancin kai na Afrika 18 da suke cikin ƙasar har da Najeriya.
Ƙasashen da suka shiga ƙungiyar daga baya sun haɗa da Rwanda da Mozambique kuma ba su da wani tarihi da ya haɗa su da Birtaniya, kuma sun nemi su shiga ƙungiyar inda aka bar su kuma suka shiga.
Ana jinjina wa Sarauniya Elizabeth da shawo kan shugabannin farko na Afrika bayan samun yancin kai da su shiga ƙungiyar renon Ingila.
Shekara biyu bayan da Ghana ta zama ƙasar Afrika ta farko da ta samu ƴancin kai daga Birtaniya, Sarauniya ta kai ziyara ƙasar a 1961.
A ƙarshen ziyarar da ta kai ta kwanaki 11, an bayyana cewa shugaban Ghana na lokacin kuma ɗan gwagwarmayar neman ƴancin Afrika wato Kwame Nkrumah ya alaƙanta ƙungiyar ƙasashen rainon Ingila a matsayin ƙungiya mai ɗauke da ƙasashe da ke da akidu iri ɗaya da alƙibila wadda za ta taimaka wa burinsa na yaƙar wariyar launin fata da kuma rashin adalci.
A lokacin sai lamarin ya zama abu mai sauƙi ga shugabannin Afrika su bi sahunsa. Haka kuma tsoffin shugabanni sun yi amfani da ƙungiyar wurin yaƙi da wariyar launin fata a Afrika Ta Kudu.
Duk da cewa shugabancin ƙungiyar ba wani abin gado bane, Amma Sarki George VI shi ne shugaban ƙungiyar na farko haka kuma Sarauniya Elizabeth ita ce ta karɓi jagorancin daga gare shi.