'Na yi karatun lauya don jagorantar shari'ar wadanda suka kashe mahaifina'

Shagufta Ahmed

Asalin hoton, Salman Saeed

Bayanan hoto, Shagufta Ahmed
An wallafa

Shagufta Tabassum Ahmed ta amince ta karanci aikin lauya bayan shawarar da iyayenta suka ba ta duk da cewa ba ta da niyyar zama lauya. Sai dai wannan lamari ya sauya bayan an kashe mahaifinta.

Ta shaida wa wakiliyar BBC Megha Mohan yadda aka shafe shekara 16 ana neman kwato hakkin mahaifinta bayan an kashe shi.

Abubuwan da nake tunawa game da ranar da aka shaida mani cewa an kashe mahaifina har yanzu ina tuna komai.

Na tuna ɗakin amma ba na iya tuna wanda yake a ciki. A ranar Juma'a ne amma ba zan iya tuna lokacin ba. Na tuna lokacin da nake jin wayar tarho tana ƙara amma ba zan iya tuna ko wane ne a cikin iyalaina ya ɗauki wayar ba.

Yayana ne ya kira.

"Sun gano shi. An kashe shi."

Ba zan iya tuna ko wa ya faɗi kalaman yayana ba amma a wannan lokacin sai rayuwata da na sani ta zo ƙarshe.

Nan take mahaifiyata ta fashe da kuka. Sai muka zauna muka yi shiru a lokacin da muka ji cewa an gano gawar mahaifina a cikin wani tanki a Jami'ar Rajshahi inda ya yi aiki a matsayin farfesa a Tsangayar Koyar da Ilimin Sinadaren kasa da hako ma'adinai.

Duka danginmu sai suka taru a gidan yayana a Dhaka babban birnin Bangladesh. Ba ya tare da mu a ranar da ya yi tafiyar sa'o'i shida da mota zuwa birnin Rajshahi a kusa da iyakar Bangladesh da India.

Sai iyalaina suka soma tattaunawa a lokacin, inda suke musayar yawu.

Ta yaya? Me ya sa?

Wa yake so ya kashe shi?

Mahaifina, wanda ya kasance mai ilimi wanda ya gwammace ya yi tafiya cikin jama'a ko kuma ya shiga motar haya a maimakon ya sayi mota mai ƙyalƙyali, ya kasance farfesa a jami'a wanda ɗalibansa ke matuƙar son sa, ya kasance mahaifin da nake riƙe hannunsa idan zan tsallaka titi har lokacin da nake da shekara 18... Wa zai so irin wannan mutumin a ce ya mutu?

Wannan tambayar ce za ta kasance tamkar wani mafarki mai ban tsoro.

Short presentational grey line

Kwana biyu kafin lokacin, a ranar Laraba 1 ga watan Fabrairun 2006, mahaifina ya shiga motar haya ƙirar bas daga Dhaka zuwa Jami'ar Rajshahi.

Yana son yadda cikin Jami'ar ke cikin walwala wanda wurin ya kasance wurin da na yi ƙuruciyata. Mun zauna a cikin wani ƙaramin gida wanda Jami'ar ta ba mu kuma duk wani abu da ake buƙata muna samu a kusa.

Ɗan uwana Sanzid da ni na tafiya makaranta da safe inda muke shafe dare da sauran yaran malaman jami'o'i a wuraren wasa da ke kusa. Mun san kowa da ke cikin jami'ar.

Photographs of Shagufta and her father in the family album

Asalin hoton, Salman Saeed

Duk da cewa ni da Sanzid mun bar makaranta mun koma Dhaka. Sanzid sai ya soma aiki a ɓangaren kula da ma'aikata a wani kamfani.

A shawarar da ya bayar, wadda shawara ce mai kyau, sai na yi karatun aikin lauya. Ba ni da niyyar karatun aikin lauya. Na yi tunanin cewa bayan karatun digirina, zan yi aiki da wata ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasa da ƙasa ko kuma na zama malama.

Sai dai mahaifina ya riga ya san abin da ya fi alkhairi ga iyalinsa ko a lokacin, na soma karatun jami'a a 2006 inda mahaifiyata ta zo ta zauna da ni a Dhaka.

A makon da ya rasu, mahaifina ya zo Dhaka ya ziyarce mu na ƴan kwanaki inda ya kama hanyar zuwa Rajshahi da safiyar Laraba, 1 ga watan Fabriarun 2006. Ya kira mahaifiyata inda ya shaida mata cewa ya isa lafiya sai kuma bayan sa'o'i kaɗan kafin karfe tara na dare sai ya sake kiranta.

Sai mahaifina ya koma Rajshahi domin ya ziyarci wata tattaunawa kan makomar ɗaya daga cikin makomar abokin aikinsa wato Dakta Mia Mohammad Mohiuddin.

Dakta Mohiuddin ya kasance ɗaya daga cikin abokin arziƙin iyalaina, sai dai dangantakar da ke tsakaninsa da mahaifina ta yanke ba da daɗewa ba.

Mahaifina ya gano satar fasaharsa sosai da Dakta Mohiuddin ya yi a ayyukansa kuma ya kai ƙarar wannan lamarin a jami'ar.

An shirya tattaunawa domin tattauna kan yadda za a shawo kan wannan matsalar.

Short presentational grey line

Na ɗan wani lokaci, sai idanun duniya suka koma kan gidanmu. Mutuwar mahaifina ta kasance wani babban labari, ta kasance mutuwa mai abin mamaki. An nuna fuskar mahaifina a talabijin kuma aka buga ta a jaridu. Kafafen yaɗa labarai na duniya da na ƙasa da ƙasa sun ta neman labarai kan wannan lamarin.

Abin da ya faru da gidanmu sai ya zama wani babban abin tattaunawa a ɗakunan watsa labarai. Wa zai kashe farfesa na jami'a? Wata gaba ce ta musamman?

Masu bincike sun gano cewa sai da aka doki mahaifina kafin aka kashe shi. A lokacin da ake cikin wannan zafi, ni da yayana da mahaifiyata mun shiga cikin ruɗani. Duk sun shiga cikin bincike. Mahaifiyata ta haɗa hannu da yayyana a Rajshahi domin taimaka wa yan sanda gudanar da bincike kan duka waɗanda ake zargi.

A cikin yan makonni, Dakta Mia Mohammed Mohiuddin - wanda shi ne mahaifina ya zarga da yi masa satar fasaha a jami'a, mai kula da wuraren zama na jami'a Jahangir Alam da sauran mutum huɗu ciki har da kuma surukin Alam na daga cikin waɗanda aka kama bisa zargin kashe mahaifina.

Portrait of the Ahmed family

Asalin hoton, Salman Saeed

A lokacin shari'ar, Jahangir Alam da sauran ƴan uwansa sun tabbatar da cewa Mohiuddin ya ja ra'ayinsu da su kashe mahaifina da zummar zai biyasu kuɗi da ba su kwamfuta da aiki a jami'a.

Mohiuddin ya musanta waɗannan zarge -zargen. A 2008, wata karamar kotu a Rajshahi ta samu duka mutanen huɗu da laifin aikata kisa inda kotun ta yanke musu hukuncin kisa inda ta sallami mutum biyu.

Ya kamata a ce maganar ta mutu amma ba ta mutu ba. Mutanen huɗu sun daukaka ƙara inda aka mayar da lamarin zuwa babbar kotun Bangladesh.

Mahaifiyata da yayana suna ta ƙoƙari domin ganin an yi hukunci ga waɗanda suka kashe mahaifina. A yadda abubuwa ke tafiya, sai na ji ba ni da amfani. A lokacin da ƙaramar kotu ta yanke hukuncin, ban daɗe da shiga shekara ashirin da wani abu ba, a lokacin ban gama girma ba.

Iyali na sun rinƙa lura da ni duk da bayan rasuwar mahaifina babban abin da suke so shi ne su ga na kammala jami'a. Sun rinƙa ba ni goyon baya ta hanyar kuɗi da kuma kula yau da kullum.

Na ci gaba da dagewa a karatun aikin lauya, amma duk da haka ba ni da tabbacin me zan yi da rayuwata. A 2011, batun kisan mahaifina ya kai babbar kotu. Kotun ta bayar da beli ga Mohammad Mohiuddin, wanda shi ne mahaifina ya zarga da satar fasaha kuma an sake shi a lokacin da ake gudanar da shari'ar.

Ya yi hayar sama da lauyoyi goma inda suke ci gaba da kare shi. A lokacin ne na fara tunanin mai zan yi da rayuwata a nan gaba. Na san me zan yi da rayuwata. Zan iya amfani da digirin da na yi na lauya domin taimakawa wajen ganin an yi hukunci ga waɗanda suka kashe mahaifna.

Ina da dama sosai, zan iya aiki da ƴan ƴan uwana. Na san yan sanda na san mahaifina kuma na san mutum biyu da ake zargin.

Shagufta Ahmed in a legal suit

Asalin hoton, Salman Saeed

Na kammala digirin lauya a 2012 inda nan take na soma taimaka wa manyan lauyoyi wurin aiki a kotu. A Bangladesh babu mata sosai waɗanda suke aikin lauya a kotu amma kowa ya ga amfani na kuma an yi maraba da ni. A nan ne na soma yin ayyuka sosai na bar duk wani aiki na mayar da hankali kan nemar wa mahaifina haƙƙinsa.

A 2013, wata babbar kotu ta yanke hukunci inda ta amince da hukuncin da karamar kotu ta yanke na kisa ga Dakta Mia Mohammad Mohiuddin da kuma Jahangir Alam. Sai dai sauran mutanen guda biyu an rage musu hukunci idan aka yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai.

Alƙalin ya bayyana cewa su mutum biyun sun taimaka ne wurin kisan amma wadanda suka kitsa abin Mohiuddin da Alam ne .

Amma duk da haka lamarin bai zo ƙarshe ba

Mista Jahangir Alam da yan uwansa sun amince suna da hannu a kisan mahaifina inda duka suka bayyana cewa Mista Mohiuddin ya biya su, amma lauyoyin Mista Mohiuddin sun sake kai ƙara Kotun Koli.

Shagufta and her mother looking at newspaper clippings recording their legal struggle

Asalin hoton, Salman Saeed

Dakta Mohiuddin yana da arziki matuƙa kuma ya san mutane sosai kuma surukinsa ɗan siysasa ne mai tasiri a Bangladesh. Yana da kudi da tarin lauyoyi kuma lauyoyin duka sun kafe a kan cewa ba shi da hannu a kisan mahaifina kuma babu wata hujja a bayyane da ke nuna cewa yana da hannu.

Sai dai bara Kotun Kolin ta yanke hukunci kan batun shari'ar mahafina ganin cewa akwai shari'a da dama a gabanta.

A ranar 5 ga watan Afrilun 2022 ne alkalan Kotun Kolin ƙarƙashin jagorancin Hasan Foez Siddique da wasu alkalai biyar suka yanke hukuncin cewa Dakta Mia Mohammad Mohiuddin na da hannu a kisan mahaifina inda suka yanke masa hukuncin kisa.

Bayan nan ne na fitar da sanarwa a madadin iyalina inda na ce na ji dadi sosai da wannan hukuncin inda na kuma ce ban san kalmar da zan yi amfani da ita ba domin misalta shekara 16 da suka gabata a dangin mu.

Mun shiga cikin ƙunci. A wani lokacin ina tunani kan ko zan samu zaman lafiya a zuciyata bayan yadda mahaifina ya rasu.

Kokarin da muka yi domin ganin cewa mun samu an yi hukunci ga wadanda suka kashe mahaifina ya mamaye rayuwata inda rayuwata ta nemi ta taya.