Ku san Malamanku tare da Malam Hamza Adam

An wallafa

Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

An haifi Malam Hamza Adam a ranar 2 ga watan Agusta 1960.

Ya yi karatun allo a hannun Malam Muhammad, wanda ya fara koyar da shi haruffan Arabiyya, har ya fara karatun Al-Kur'ani gwargwadon iko. Wasu ma sun dinga kiran sa da suna Hafiz, amma ba su san bai haddace Al-kur'ani ba.

Daga bisani ya sake yin karatu a wurin wani malami mai suna Yunus Muhammad. Su ne malaman da suka koyar da malamin Al-kur'ani a Jeka da Fari.

Mahaifinsa Sheikh Adam Abdulhamid wanda ya yi karatun Fiƙihu, shi ne ya koya masa littafan Ƙawa'dul Islam, da sauran litattafai kamar: Kawa'idi, Ahalari, Iziyya, Ashmawi, Risala.

Lokacin da aka kafa kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus Sunna karkashin jagorancin Sheikh Isma'il Idris a shekarar 1978 a birnin Jos na jihar Filato, Malam Hamza na daya daga cikin wadanda suka amsa kira da abin da suka sani na Al-kur'ani da Fiƙhu.

Neman ilimi

Ya ci gaba da karatu a makarantar ATC Gombe, inda suka kammala a shekarar 1987.

Daga nan ya nemi shiga Jami'ar Bayero da ke Kano amma bai samu karatun ba, sai Ambasada Aliyu Hassan ya zama jakadan Najeeriya a kasar Libya.

A cewar malam: "Sai aka samu damar karo karatu a can na mutum uku. Sai na je Libya na karanci fannin kira zuwa ga addinin Musulunci. Bayan dawowa daga Libya, ban nemi aiki da gwamnati ba, sai na fara Da'awa da wa'azi.

"Dama kuma shi ne na'ibin limamin masallacin Gombe da sauran makarantun Islamiyya karkashin kungiyar IZALA."

Matakin kungiyar IZALA ya ba shi damar ci gaba da wa'azi har zuwa kasashen waje.

Daga bisani ya zama shugaban malaman jihar Gombe karkashin kungiyar IZALA a shekarar 2011.

Malamin ya ce ranar da ba zai taba mantawa da ita a rayuwarsa ba ita ce ranar da ya gan shi a filin jirgin sama na birnin Turabulus na Libya da sunan neman ilimi.

Ranar da mahaifiyarsa ta rasu ita ce "mafi muni" a tarihin rayuwarsa da ba zai taba mantawa ba.

Abincin da Malam Hamza ya fi so shi ne tuwo da miyar kuka.