Wurin cin abincin da ke taimakawa wajen yaki da nuna wa kurame wariya a Kenya

An wallafa

A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, Ismail Einashe ya ziyarci wani wurin cin abinci a kasar Kenya da ke kokarin sauya tunanin mutane masu fama da nakasa.

Wurin cin abincin da ke bayan wata kofar shiga cikin unguwa mai hada-hada a Nairobi babban burnin kasar Kenya, wurin cudanyar jama'a ne da ke nuni da yadda rayuwar kurame za ta iya sauyawa

Ta hanyar daukar ma'aikata kurame da suka fuskanci nuna wariya a kusan duka harkokin rayuwarsu, wurin cin abinci na Pallet Cafe ya nuna yadda harhada mutane daban-daban wuri guda kan yi amfani.

Yayin da suke kai-komo a tsakanin tebura da tukwanen furanni masu tarin yawa a wannan kayataccen wurin cin abincin na wurin shakatawa, ma'aikatan sabis na karbar sakonnin kostomomi na irin abincin da suke bukata.

Suna kuma amfani da alama da yatsu cikin harshen kasar Kenya, ko wata hanyar da sadarwa ba tare da magana ba.

Akwai manyan allunan hoto da aka kakkafa dauke da alamu na maganar kurame.

Amma alal misali, sabis din za su iya nuna alamar makyarkyatar sanyi su tambayi ko wani na bukatar kwalbar ruwan sanyi, kana kostoma zai iya tabbatar da hakan ta hanyar daga babban dan yatsansa sama.

Ko kuma idan aka bukaci kwai, idan kostoma na son dafaffen kwai su kan yi amfani da alamar farko ko kuma karkara 'yan yatsu idan ba a son kwan yad ahu da yawa.

Edward Kamande, wanda ya fara aiki lokacin ba a dade da bude wurin cin abincin na Pallet Cafe a 2019, ya fara a matsayin sabis amma yanzu shi manaja ne a wurin.

Mai shekaru 26, wanda ya bude wurin cin abincin, dan kasuwa Feisal Hussein," ya aminta da daukata aiki. Ya ga alamar cewa ina zan iya yin wani abu.''

Dan kasuwa, kuma tsohon ma'aikacin agaji, ya kudiri bude wani wuri da ba kawai zai rika sayar da nau'ukan abinci masu dadi kamar su miyar ƙwai ta Benedict da shakshuka (ta yankin Arewacin Afirka mai cike da kayan kamshi) ba, amma har da taimaka wa nakasassu samun guraban aiki.

"Burina shi ne in taimaka wa al'ummar kurame,'' ya ce game da kasuwanci da yanzu ke da rassa uku.

A wannan reshen - in Lavington - ma'aikata fiye da 20 cikin 40 na da matsalar rashin ji sosai ko kuma kurmanta.

Mista Kamande ya yi amanna ana martaba shi kan abubuwan da zai iya yi. ''Babu nuna wariya a kamfaninmu, akwai 'yanci a nan,'' ya bayyana.

Shekaru uku da suka gabata, lokacin da y afara aiki a wurin, Mista Kamande mai jin kunya ne, maigidansa ya bayyana, amma yanzu ya zama fitacce wurin tafiyar da harkar kasuwancin.

Mista Kamande ba kwai kula da ma'aikata yake yi kadai ba, har ma da lura da harkokin kudi da kuma sayen kayyakin amfani.

Yana kaunar aikinsa, ya bayyana, kana yana matukar jin dadi a duk lokacin da kostomomi suka yaba da ma'aikatansa kan yadda suke tafiyar da aikinsu.

Akasarinsu bas u taba yi aiki a wani wuri ba don haka aikin wani sauyin rayuwa ne a gare su.

Da farko, Mista Hussein ya yi ta faman neman mutanen da zai dauka aiki amma yanzu bas ai ya sha wahala ba saboda a koda yaushe mutane na shigar da takardun neman aiki, ya ce.

Ko shekka babu, wurin cin abincin ya kasance cike da nasarori da ya sa sauran kafanoni ke tambayar ko zai taimaka musu wajen daukar kurane aiki.

Kamar yadda Mista Kamande ya bayyana, babban cikas din da kurame ke fuskanta a kasar Kenya shi ne samun guraban aiki.

"Akwai kurame da dama da ba su samu damar samun guraban aiki ba," ya ce.

An bayyana cewa akwai kurame akalla 600,000 a kasar, kana duk da cewa dokar kundin tsarin mulki ta haramta nuna wariya da masu nakasa, suna cigaba da fuskantar manyan kalubale a fanonin kiwon lafiya, da ilimi da kuma samun guraban aiki.

Ba sosai ake fahimtar alamar maganar kurame ba na kasar Kenya kuma har yanzu akwai karancin sanin shi tsakanin ma'aikatan kasar.

Kana akwai karancin masu tafintar alamar maganar kurame a Kenya, kana babu wani tsari da ya amince da yin rajista ko duba cancantar masu yin tafintar a kasar.

Duk da cewa ya kamata a ce shirye-shiryen talabijin su rika saka alamar zancen kurame a cikin shirye-shryen, kada ne ki yin hakan.

Mista Kamande na iya yin magana yadda za a fahimce shi, amma abokan aikinsa da dam aba su kai wannan matsayi ba.

"Muna bukatar ilimi [game da abubuwan da suka shafi kurame] a kasar mu," ya bayyana.

Ya bayyana min abubuwan da wani abokinsa ya fuskanta a birnin Nairobi lokacin da 'yansanda suka rika tsayar da shi suna tambayarsa ya nuna katin shaidarsa.

"Sun yi barazanar kai shi gidan yari. Amma ya kasa ba su amsa."

Mista Kamande ya yi kokarin samun isa inda abokin nasa yake kana ya yi wa 'yansanda bayanin cewa shi kurma ne.

Abubuwa irin wadannan sun koya masa darasi cewa dole kurame su tashi tsaye wajen taimaka wa junansu a wuraren da ke da barazana a gare su.

Baya ga bai wa Mista Kamande dama da kuma yanayi na kariya wajen cimma burin sana'arsa, wurin cin abinci na Pallet Cafe wuri ne kuma da ya samu kan sa cikin tarkon soyayya.

Ya hadu da matarsa Jacqueline, wacce ita ma kurma ce, a lokacin da tana aiki a matsayin sabis.

Yanzu suna da jariri mai watanni 11 da suka saka wa suna Godwin, wanda shi ba kurma ba ne.

Cikin alfahari yana ta nuna hotunan dan sa a cikin wayar salularsa.

"Saboda wurin cin abincin,'' y ace,'' na cigaba zuwa mataki na gaba a rayuwata.''