Labarai biyu na kisan mata – da kuma nuna son zuciya daga kafafen watsa labarai

An wallafa

Kafafen watsa labarai sun gwammace su bayar da labarai na wasu matan da aka hallaka a kan wasu - an yi wa daya labarin adalci wajen yada shi sosai, a yayin da kuma aka yi saurin kawar da batun shi. Amma aikata laifin kisan mata - lokacin da aka kashe mace saboda jinsinta - ka iya kasancewa an kula da shi daidai-wa-daida, muddin Majalisar Dinkin Duniya za ta iya jan hankalin kasashen duniya su yi amfani da tsarin da aka fadada kan gano su.

Alexandra

A ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2021, kwana daya kafin a kashe ta, Alexandra Inshina ta fada wa kawarta cewa ta fada tarkon soyayya.

A wannan rana ta Asabar da tsakar rana, a yayin da take kwance don shan hasken rana tare da kawarta Yulia a kusa da bakin tafki a Beryozovsky, wani karamin gari a gabashin tsaunukan Ural a kasar Rasha, Alexandra na cike da annashuwa.

Shekaru kadan tun bayan rabuwar aurenta, kuma Alexandra mai shekaru 35 ta cigaba da tafaiyar da rayuwarta a matsayin uwa ita kadai ga danta mai shekaru 10.

Akwai abubuwa da dama na yin farin ciki a kai. Jagora ce a wani bangare a masana'antar kera kayayyakin gyaran motoci inda ta yi aiki, kuma kwanaki biyu kafin nan, ta biya kudin tafiya yawon bude ido zuwa kasar Masar ita da danta.

Kuma ya zama wani sabon babi ne na soyayya. Wani mutum daga birnin Yekaterinburg mafi kusa, wanda za ta hadu da shi don tattauna soyayya a wannan yammaci, na kara sa rayurwata cikin matukar farin ciki.

A yayin da take magana, wayar salularta na ta samun wasu sakonnin kar-ta-kwana. Shi ne ya aiki, amma ba labari ne mai dadin ji ba. Bai tabbatar ko zai iya zuwa ba. Sakon kar-ta-kwanan ya kasance kamar wani abu da goge komai.

"Abin ya bata mata rai," in ji Yulia. Matar ta sha zama har ya zuwa karfe takwas na dare kafin su koma gidajensu, tare da yin alkawarin tuntubar juna kamar yadda aka saba bayan wayewar gari.

Alexandra ta dawo ita kadai cikin gida, bayan da danta zai yi hutun karshen mako a wurin iyayenta.

Daga bisani, Alexandra ta yanke shawara. Za ta tafi Yekaterinburg zuwa wani wurin dabdala na dare da ake kira Rosy Jane. Da misalin karfe daya da rabi na dare ta kira hayar tasi. Hoton kyamarar tsaro ta CCTV ya nuna cewa zuwa karfe uku na dare tana cikin kulob din ita kadai. Alexandra ta yi wa saurayinta sakon kar-ta-kwana tana mai gayyatarsa ya same ta a can.

Mene ne femicide?

  • Hukumar Lafiya ta Duniya ta fassara femicide a matsayin "kisan mata saboda kawai su mata ne" kuma ga Majalisar Dinkin Duniya hakan na nufin "kisa mai nasaba da jinsin mata da 'yan mata."
  • Kasashe goma sha takwas na yankin Latin Amurka da Caribbean sun amince da dokoki na musamman da ke daukar kisan matan a matsayin aikata babban laifi.
  • A kasashe da dama ba a amfani da kalmar sosai, amma masu fafutika na kara amfani da ita a kan yaki da cin zarafin mata.

"Gaskiya ba ni da kirki," daga bisani ya fada wa Yulia, cikin rashin jin dadi saboda tsarguwa.

Da misalin karfe biyar na asuba Alexandra ta tafi, kuma wani mutum a cikin mota wanda ke nuna cewa shi direban tasi ne ya tunkaro ta.

Da farko ta ki amincewa ta shiga, kamar yadda hotunan kyamarar tsaro ta CCTV suka nuna, daga baya ta sauya ra'ayi.

"Ina ga a lokacin da ta ga ta riga ta gaji ne. Tana son ta tafi gida ne kawai," in ji Yulia.

Bayan minti talatin aka hallaka Alexandra Inshina ta hanyar daba mata wuka har sau shida, hannunta a daure a bayanta. An shafe kwanaki biyu kafin a gano gawarta a cikin surkukin daji da itatuwa mai nisan kilomita 25 daga gida.

"Wani irin mummunan kisa na nuna kiyayya ne," abokiyarta, Marina ta shaida wa BBC.

Olga

Shekaru shida kafin a hallaka ta, Olga ta shaida wa kawayenta cewa tana son zama tauraruwar talabijin.

Shekarunta 21, kyakkyawa ce, kuma ba ta dade da komawa babban birnin kasar Rasha daga birnin Bryansk da ke yammaci ba, inda ta bar 'yarta wacce ta haifa tun tana da shekaru goma sha a karkashin kulawar mahaifiyarta.

A birnin na Moscow, kyau da kuma kwarjinin Olga sun dauki hankulan masu sonta. Ta yi aikin wucin-gadi na tallan kayan kawa kuma ta kara gyara kamanninta, da sauya launin bakin gashinta zuwa launin ruwan gwal.

Ta shaida wa makwabcinta Dmitry, cewa tana son fitowa a shirye-shiryen gidan talabijij na Dom-2, da ake yi kamar na shirin nan na Big Brother.

"Olga mutuniyar kirki ce. Ba ruwanta da hayaniya," in ji Dmitry. "Ba za ka taba tsammani abin da zai faru da ita gaba a rayuwarta ba."

Dmitry bai sake haduwa da Olga ba tun bayan da ta bar yankin da yake zaune, amma bayan shekaru biyu, a watan Yulin shekarar 2020, ya ci karo da wasu hotunan Olga da aka saka a Vkontakte, wani sanannen shafin sada zumunta na kasar Rasha.

"Tsoho ya hallaka karuwa mai shekaru 27 a kusa da birnin Moscow," ya karanta a kan labarin.

Babu wani tabbaci kan yadda aka yi Olga ta koma yin karuwanci - ba bangaren rayuwarta ba ne da ta taba magana a kai da kawayenta.

BBC ta tattauna da uku daga cikinsu, da suka tabbatar da cewa karuwanci ne hanyar da ta bi don samun zama tauraruwar talabijin, me yiwuwa wani ne ya yi mata tayin hakan a tsakanin masu fada a ji na masu tallan kayan kawa.

Sun yi tunanin cewa lallai wani ne ya ja ra'ayinta cewa aikin bin masu kudi ne zai sa ta samu hanyar zama tauraruwar masana'antar nishadantarwa, wanda shi ne burin da take da shi.

Daya ta bayyana ta a matsayin mai kirki, kana amintacciya da kuma kasancewa rashin wayewa.

A ranar da aka kashe ta, 20 ga watan Yulin shekarar 2020, Olga na da shafin yanar gizo na masu rakiyar manyan masu kudi inda ta sauya sunanta zuwa Margo.

Oleg Tochilkin mai shekaru 53 kuma wanda aka taba daurewa - da aka sako a bisa alkawari, bayan shafe shekaru 20 a gidan yari kan aikata laifukan da suka hada da kisan kai, da cin zarafi a cikin gida - ya shiga ya bude shafin Olga ya kuma gayyace ta zuwa gidansa da yake haya a Mytishchi, wani birni a arewa maso gabashin Moscow. Takardun kotun da BBC ta gani daga Kotun Birnin Mytishchi sun nuna cewa bayan wata cacar-baka ne Tochilkin ya yi wa Olga duka tare da makure ta. Ya kuma jefar da gawar ta tsirara a wajen shiga cikin ginin inda aka gano ta bayan wasu sa'oi.

Labarai biyu

Wanda ya hallaka Alexandra, Marat Imashev, shi ma tsohom mai laifi ne, da aka sako bayan shafe shekaru 28 a gidan yari kan aikata manyan laifuka da suka hada da fyade, da fashi da makami, da zamba da kuma kai wa mata fiye da goma hari.

Ya dauki tsawon makonni kafin 'yan sanda su gano shi, kana kuma sun yi nasu kokarin wajen ganin cewa labarin ya karade, in ji kawayen Alexandra.

Kawayenta sun tattara masu farautar neman ta, bayan da Alexandra ta yi batan-dabo, lokacin da aka ga ba ta koma daukar danta daga wurin mahaifiyarta ko zuwa wurin aiki ba.

Lokacin da aka kama wanda ya yi kisan, da farko ya bayyana cewa ya sauke Alexandra a wani kanti, amma daga baya ya bayyana kwace mata abin wuya da 'yan kunnaye sannan ya daba mata wuka. Yanzu yana gidan yari yana jiran a yi masa shari'a.

Abu mai sauki ne bayar da shahararren labarin Alexandra, in ji Anastasia Rovnushkina, wata ma'aikaciyar kafar yada labarai ta E1 News a kasar Rasha, saboda ta zauna lafiya da jama'a.

Labarin ya shahara sosai a shafin intanet, kana ya watsu cikin sauri a shafukan sada zumunta.

"Alexandra yarinyar mace ce, kuma uwa, za ta iya kasancewa daya daga cikinmu."

Ita ma Olga yarinyar mace ce, kuma sanannya, kana kuma uwa da karamar yarinyar da shekara daya ta bai wa dan Alexandra. Ita wani mutum ne da ya yi zaman gidan yari na tsawon shekaru kan aikata cin zarafin mata ya hallaka ta.

Amma kuma mutuwarta ba ta ja hankali ko samun tausayawa sosai daga jama'a ba.

Mahaifiyar Olga ta shaida wa BBC cewa rahotannin da aka yada sun haifar wa da iyalan bacin rai, musamman ma da diyar Olga mai shekaru 11.

'Yar jarida Anastasia Rovnushkina, wacce ta dauki rahoton kisan Alexandra Inshina wa kafar yada labarai ta E1 News, ta bayyana cewa sanadiyyar mutuwar Olga ta nuna yanayin banbaci a yada labaran.

"Kafafen yada labarai na yin la'akari da nuna darajar masu sauraro ko kallo ne. Kuma idan aka zo batun masu karuwanci, tunanin na tafiya ne a kan cewa idan ka zabi hanyar aikata laifi, to zabinka ne. Saba wa doka ne a Rasha kuma ana tunanin cewa kan saka kan ke cikin barazana a wannan aiki,'' ta ce.

"Amma idan kai ba sananne ba ne kamar mu, to in aga kalmomin da ake amfani da su a kafafen yada labarai a kan ka daban ne. Kowa a cikinmu zai iya samun kan sa cikin wannan hali da Alexandra ta fada, amma ba zai taba tunani kasancewa irin halin da karuwa ta shiga ba.''

Ta kuma ce tana fatan hakan zai zama darasi wajen samun daidaito ga matan da aka kashi, tare da fitar da su daga irin labaran da ake fada a kan su a kafafen yada labarai.

"Ya zamo cewa ko wace mace ana saka ta a jerin wadanda lamarin ke shafa, koda kuwa uwa ce, ko karuwa, ko kuma wani matsayin da suke da shi na zamantakewa da tattalin arziki.''

Mata na mayar da martani

Yanzu haka an tuntubi kasashe 95 da su rika amfani da sabon tsarin, da suka hada da Birtaniya, da Brazil, da Korea ta Kudu da kuma Rasha.

Idan suka yi hakan, zai nuna yadda kasashen ke daukar matakai masu inganci ko akasin haka game da matsalar.

Sai dai kuma a nan batun zai tsaya. Ba zai bai wa kasashen shawarar sauya dokokinsu ba.

"Kisan mata babbar matsala ce a fadin kasar Rasha, da ke shafar matan kasar Rasha," Lyubava ta bayyana, "kana gwamnati ta ki takula da cewa wannan matsala ce."

Kisan mata a kasar Rasha

  • Kamar yadda alkaluman Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan aikata laifuka da shan migaun kwayoyi da kisan kai suka nuna , a shekarar 2018 ma'aurata ko iyalai ne ke da alhaki wajen 0.7 na kisan matan a kan ko wane mata 100,000 a Birtaniya, da 2.2 a Amurka, kana 4.1 a kasar Rasha.
  • Kasar Rasha ba ta da dokoki kan cin zarafi a wuraren aiki kana a karon farko an rage kaifin laifin aikata cin zarafi daga aikata babban laifi zuwa rashin gaskiya a shekarar 2017, muddin dai wanda aka zalunta bay a bukatar zuwa asibiti a duba shi.
  • Kamar yadda rahoton Bankin Duniya ya bayyana, Mata, da Kasuwanci, da kuma Doka ga shekarar 2021, kasar Rasha ba ta samu komai a fagen yin dokoki kan kare hakokin mata saboda ba ta da wani tadanin kasafin kudi na kare mata daga cin zarafi.

Wata lauya mazauniyar birnin Moscow - Mari Davtyan ta amince, tare da nuna cewa a dokar kasar Rasha akwai dokar wucin gadi ko kuma horar da maza kan jurewa da saurin fushi ga maza da ke nuna alamun aikata cin zarafi.

"Babban abin tsoron duka shi ne cewa babu wanda ke sa ido ko hana mazan da ke da tarihin cin zarafin jinsin. Wadannan maza kan fita su kara aikata irin wadannan muggan laifuka sai da dama.''

Wannan gakiyar lamari ne ga wadanda suka kashe Alexandra da Olga. Duka an taba kulle su a gidan yari, duka an sako su, kana duka sun sake aikata kisan kan.

Sun zauna a birane daban, da kuma buri daban, amma kamar yadda abokansu suka bayyana Alexandra da Olga na da halayya iri daya. Duka masu son mutane ne, da ban dariya, Suna da ataimako da kuma amana. Sun fi farin ciki a lokacin da suke tare da 'yayansu - da duka ke zaune tare da kakanninsu mata.

Kana abokan duka matan biyu sun nuna cewa a lokacin da 'yayansu suka girma kana suka nemi amsar tambayoyi, duk da cewa an rubuta a kafafen yada labarai, za sus ani aga wadanda suka sani suke kuma kaunar iyayensu mata, cewa mata na fuskantar matsalolin zamantakewa, kana ba a dora musu laifin mutuwarsu ba.