Mabiya addinin Baha'i a Masar: ‘’Muna son wurin da za mu rika binne mamatanmu’

- Marubuci, Daga Ahmed Shousha
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- An wallafa
Mabiya addinin Baha'i a kasar Masar sun shafe shekaru suna yin kira da a ba su 'yancin da za su rika samun wuraren binne mamatansu a garinsu na asali, Askandariya.
Kididdiga ta nuna cewa addinin na Bahaʼi, daya daga cikin kananan addinai a duniya, na da mabiya sama da miliyan shida a fadin duniya, da suka hada da birnin na biyu a girma a kasar Masar.
Amma kuma babu makabarta ta mabiya addinin na su a birnin na Askandariya.
Makabarta daya kacal ta mabiya addinin na Baha'i a kasar Masar tana wajen birnin Alkahira, wacce ba nisa kadai ba, amma tana da matukar cunkoso.
"A cikin littafinmu na dokoki, Kitab-i-Aqdas, a bayyana ta ke cewa ba a amince da a dauki mamaci a I tafiyar da ta wuce sa'a daya da shi ba,'' Hatem El-Hady, wani mai bin addinin na Bahaʼi ya shaida wa BBC.
Tuki daga birnin Askandaria zuwa birnin Alkahira na daukar akalla tsawon sa'oi uku.
"Muna karya dokokin addininmu ta hanyar daukar mamatanmu zuwa wuri mai nisa, idan aka hada da batun cewa makabarta daya kacal da muke da ita ba za ta iya daukar karin wasu mamatan ba,'' Hatem El-Hady ya ce.
Mahukuntan kasar Masar sun bayar da filayen makabartu a bisa la'akari da addini.
A hukumance, kasar Masar ta kawai san da zaman addinai masu dayanta abin bauta: Kiristanci, da Musulunci, da kuma Juda.
Katunan shaidar zama dan kasa, da abisa doka ana bukatar nuna addinin ko wane dan kasa, yana da kawai alamar (-) ga mabiya addinin Bahaʼi.
Taƙaddama a kotu
Baya ga neman makabarta, yin rajistar aure shi ma kan kasance wani babban kalubale ne.
Ko shakka babu, wasu al'umomin su kan yi amfani da shaidar addinin karya don bin tsare-tsare da ka'idojin gwamnati.
Babu tabbaci kan yawan adadin al'ummar mabiya addinin Bahaʼi a kasar Masar saboda babu rubutattun bayanai.

Asalin hoton, Reuters
Amma an kididdige cewa sun kai dubbai a fadin kasar. Gwamman iyalan Baha'i akasari na zaune ne a birnin Askandaria.
Shekara daya da ta wuce, wasu a'lumomin sun je kotu don neman gwamnati ta ba su filn da za su rika binne mamatansu, amma bas u samu galaba a shari'ar ta su ba.
A hukuncin da ta yanke, kotun ta ce ''dole a bayar da fifiko ga muradun al'umma da yawa fiye da na daidaikun mutane, kana cewa addinin Baha'i ya sab awa dokokin kasa, wacce ke bin tafarkin Shari'ar Musulunci.''
Sami da Laila, wasu ma'aurata mabiya addinin Baha'i a Askandariya, sun bayyana damuwarsu da sakamakon shari'ar.
Ƴancin al'ummomi ƴan tsiraru
"Ka yi tunanin yin bulaguron jeka-ka-dawo tsakanin birnin Askandariya da Alkahira, kashe kudi, da tsananin gajiya, da tafiya a mota….Zai fi mana sauki idan aka ce akwai makabarta a nan Askandariya.
Ni haifaffen kasar Masar ne, shin ba 'yanci na ba ne in samu makabarta kamar yadda addinina ya tanada?" Sami ya bayyana.
Laila ma ta amince da batun. Danuwanta ya rasu a karshen shekarar 2020.
"Mun tafi a cikin kwambar ayarin motoci zuwa Alkahira don yi masa jana'iza kamar yadda addininmu ya tanada. Mun sha wahala a ranar. Dole in yi irin wannan tafiya a duk lokacin da na bukaci kai ziyara kabarinsa.''
BBC ta tuntubi mahukuntan kasar don ji daga gare su, amma babu wani bayani ko sanarwa da ta fito.

Amma wani lauya dan kasar Masar Ayman Mahfouz, wanda ke kare matsayin gwamnati ya ce, dole mahukunta su ja layi.
"Muddin muka ce za mu bayar da kofa ga ko wane addini, kowa zai rika neman makabartu na kashin kan sa.
Hakan zai haifar da rarrabuwar kawunan a tsakanin 'yan kasar.
Makabartar mabiya addinin Baha'I daya kadai da ake da ita a birnin Alkahira zagaye ta ke da babban bango, wanda ke da wata alama da ke nuna cewa 'Kada Ka Tunkara' a kofar shigarta.
Hotunan da ke cikin makabartar a Alkahira da aka nuna wa BBC sun nuna cunkoson filin da ke da sauran wuri kalilan a tsakanin kabarurruka.
Addinin Baha'i ya samo asali ne daga birnin Bagadaza shekarar 1863, da wani mutum mai suna Baha'ullah , dan asalin kasar Iran da ake martabawa ya bullo da shi.
A rubuce-rubucensa, Baha'u'llah ya bayyana cewa '' binne mamaci da wuri, shi ya fi komai fa'ida da alkhairi''.
Dokokin addinin Baha'i sun tanadi cewa ya kamata a binne mamaci cikin lokacin da bai wuce sa'a day aba daga inda ya mutu.
Nuna wariya a kasar Iran
Kasar Masar ita kadai ve kasar da mabiya addinin Baha'i ke fadi tashin neman 'yancin jana'izar mamatansu ba, kana suke fuskantar nuna wariya.
A shekarar da ta gabata, mahukuntan kasar Iran sun bayar da umarni fa al'umomin da su binne mamatansu fursunonin yaki da aka aiwatar wa da hukuncin kisa a shekarar 1988, gabaki daya cikin babban kabari.
Kasancewar su mabiya addinai 'yan tsiraru mafi girma a kasar, mahukunta na daukar mabiya addinin na Baha'I a kasar Iran a matsayin masu akidar bidi'a da ke fuskantar cin zarafi.
Mayaka 'yan tawayen Houthi a kasar Yemen sun kulle fitattun mabiya addinin Baha'I shida a Sana'a babban birnin kasar har na tsawon shekaru da dama, da tuni aka sako su a shekarar 2020.
Al'ummar Baha'i sun bayyana cewa dalili daya kacal da ya sa aka kulle shi ne 'addininsu'.
Idan muka dawo birnin Askandariya, har yanzu Sami da Laila suna kan bakansu na fatan da suke yi sus amu makabarta a birninsu.
Sun shaida wa BBC cewa za su daukaka kara zuwa Kotun Kolin kasar.
"Muna so mu rika binne mamatanmu a makabartarmu kuma a bisa al'adarmu,'' Sami ya bayyana.

Menene addinin Bahá'í?
- Baha'ullah dan asalin kasar Iran da ake martabawa ne ya kafa shi a birnin Bagadaza a 1863.
- Addinin Baha'i ya yarda da duka addinai cewa suna da asali da gaskiya.
- Babban ra'ayin addinin Bahá'í shi ne dayanta dan adam.
- Sun yi Imani da yin aiki tare don samun cigaba mai amfanin dan adama na bai-daya.
Cagil Kasapoglu contributed to this article











