Wordle: Wasan game din da saurayi ya ƙirƙiro wa budurwarsa don faranta ranta ya samu karɓuwa a duniya

Asalin hoton, BBC News
- Marubuci, Daga Harriet Orrell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
A 'yan makonnin nan wani wasan kwamfuta wato game na haɗa kalmomi ya bai wa shammaci duniya kuma a yanzu jaridar New York Times ta yi wuf da shi a kuɗin da ba a bayyana ba.
Game ɗin Wordle da ke ƙalubalantar masu yin sa su yi hasashen kalma cikin yunƙuri shida, ya ja hankalin jama'a saboda sauƙinsa da kuma sharaɗin yinsa sau ɗaya a rana.
Wanda ya ƙirƙiri wasan mazaunin New York, Josh Wardle, ya ce ya yi matuƙar mamaki da yadda ake ta magana kan wasan nasa tun bayan ƙirƙirarsa a watan Oktoban 2021.
"Tun bayan ƙaddamar da Wardle nake ta mamakin abin da masu amfani da shi ke cewa," kamar yadda wallafa a Twitter. "Wasan na ƙara girmama fie da yadda neke zato - wanda ban zaci zai yi yawa ba saboda na yi shi ne saboda mutum ɗaya kacal."
Wordle (wanda sunan mahaifinsa ne) ya haɗa wasan ne saboda masoyiyarsa, Palak Shah, wadda take matuƙar son wasan haɗa kalmomi don ta rage lokaci yayin dokar kullen annobar korona.
Bayan abokai da 'yan uwansa sun nuna sha'awarsu sai ya sake shi ga jama'a wata uku da suka wuce, kuma a yanzu yana da miliyoyin masu amfani da shi a faɗin duniya da ke shiga don yin irin abin da suka yi jiya.
Masu kwaikwayo a wasu harsuna daban-daban na ƙoƙarin ƙirƙirar Wardle, amma yaya za su yi da daɗin da yake da shi wanda ya sa mutane suka maƙale masa?
Turawa
"Ina tura wa ɗan uwana da ke New York makina da safe," a cewar Anindita Ghose, wani marubuci kuma ɗan jarida a Bombay. "Ya yi min ƙorafi cewa wasan na hana shi barci kamar yadda ya saba saboda sai tsakar dare ake fito da sabuwar jarrabawa.

Asalin hoton, Anindita Ghose
"Muna gab amma irin wannan jarrabawar da ake yi iri ɗaya kullum na ƙara mana annashuwa.
"Ba kasafai ake faɗuwa ba saboda mafi yawan mutane na dacewa cikin yunƙuri shida, amma ba sai wani ya faɗi ba kafin kai ka yi nasara."
Haka ma Sam Lake, wani ɗan Birtaniya da ke zaune a Hon Kong, ya ce wasan ya karɓu sosai tsakanin abokansa.
"Mutane da yawa na nuna makinsu a nan kullum, saboda haka ina tunanin dukkansu wasan ainahi na harshen Ingilishi suke amfani da shi," a cewarsa.
Nau'i daban-daban
Ganin yadda wasan na harshen Ingilishi ya yi nasara, ba abin mamaki ba ne don masu ƙirƙira sun shiga fafutikar ƙirƙirar wasan a wasu harsuna.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, wani jerin sunaye ya nuna cewa akwai nau'in wasan guda 222 cikin harsuna 79.

Asalin hoton, Getty Images
Wani ƙwararre kan ƙirƙirar manhaja a Chennai na Indiya ya ƙirƙiri wani nau'i na wasan a harshen Tamil amma ya cire iyakar yunƙuri shida da ake sakawa a ta asalin.
Son ilimantarwa
Haka shi ma Lau Chaak-ming, wani ƙaramin farfesa a ɓangaren harsuna na Jami'ar Kyarwa ta Hong Kong, ya daɗe yana bincike kan harshen Canton na China, kuma shi ma ya ƙirƙiri wani nau'i na Wordle (ta hanyar amfani da harufan Rumawa kuma ya yi rubutu a Canton).
"Na fara amfani da wasan Wordle sati uku da suka wuce kuma zamar min jiki," ya faɗa wa BBC. "Tuni ina da jerin wasu kalmomi na Cantoneese da nake aiki a kai, saboda haka faɗuwa ce ta zo daidai da zama."
Ya fito da nasa wasan a ƙarshen watan Janairu amma tuni an fara amfani da shi sau 100,000.

Asalin hoton, Getty Images
Irin wannan muradi na son ilimantarwa ya yi wa Lau da Sanker tasiri, kuma hakan na ƙunshe cikin wasannin daban-daban a faɗin duniya.
Wani uba a Wales na son 'ya'yansa su koyi harshe Walsh sai ya ƙirƙirar musu wasan kwamfuta.
Shi ma wani ƙwararre a British Columbia, Canada ya ƙirƙiri nau'in Gitxsan da ke ɗauke da aikinsa na jami'a don samar da wani ƙamus na harshen mutanen yankin.










