Wasan kwamfuta na China: Gwamnatin kasar na kokarin hana yara zama kwararrun masu wasan kwamfuta ne?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Pablo Uchoa and Business Daily
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
China kasa ce da ke son wasan kwamfuta, to amma a yanzu tana takaita lokacin da yara za su dauka suna wasa a intanet zuwa sa'a uku kawai a mako.
Tana da masu wasn kwamfuta kusan miliyan 740, wato sama da rabin al'ummar kasar. Ana sa ran cinikin da ake samu a kasuwar wasannin kwamfutar ya kai na dala miliyan dubu 55, kamar yadda wani kamfani Niko partners ya bayyana. Kuma kasar ta mamaye duk wata gasar wasannin kwamfuta a duniya.
To sai dai duka wadannan abubuwa na fuskantar cikas domin jam'iyyar Kwaminisanci ta kasar na kokarin sanya doka a kan wanda zai yi wasan na bidiyo da kuma lokacin da zai yi.
A shekarar da ta wuce gwamnatin kasar ta kara tsaurara dokokin takaita wasannin, inda ta ce mutanen da ke kasa da shekara 18 za su wasan kwamfutar ne a tsakanin 8 na dare da 9 na dare, ranar Juma'a da Asabar da Lahadi - da kuma karin sa'a hudu a ranakun hutu na kasa.

Asalin hoton, Getty Images
Kuma babban kamfanin fasaha na Tencent, wanda ke yin fitattun wasanni irin su Honour of Kings (known as Arena of Valor internationally) da Peacekeeper Elite, ya bayyana cewa ya bullo da fasahar gane fuskar mutum domin tabbatar da yara 'yan shekara goma sha ba sa yin wasan a tsakanin 10 na dare da 8 na safe.
Matakin ya janyo ce-ce-kuce tare da harzuka mutane a shafukan sada zumunta da muhawara na China, inda wani mai amfani da shafin Weibo ya ce, shi ya rasa ma abin da zai ce, ya kara da cewa: ''Yanzu wasan ya zama kamar zuwa aiki.''
Wani matashi mai shekara 17 wanda ke wasannin na kwamfuta ya tura sako ne da gatse yana cewa : "Babu wani na wasannin a yankunan karkara, to ke nan za mu yi wasa da kasa ne ?"
Shi kuwa wani matashi wanda ya soki shawarar sanya dokokin ya ce: "Ina mamaki, mutane sun tashi ran daya ne kawai 'yan tsakanin shekara 17 da 18 suka samu kansu a cikin wadannan wasanni? Za a fake ne da wasan kwamfuta kawai a zarge shi kan gazawar iyaye ta ilmantar da 'ya'yansu."

Asalin hoton, Getty Images
‘Abin da ke dauke hankali'
Gwamnati ta kuduri aniyar takaita yin wasannin na kwamfuta ne, saboda ta dauke su a matsayin wani abu da ke bata lokaci da dauke hankali daga muhimman abubuwn da suka kamata , in ji Steve Tsang, darektan cibiyar nazarin harkokin China ta Jami'ar London (London School of Oriental and African Studies (SOAS)).
Malamin ya ce gwamnatin China na ganin wannan matsala a matsayin wani kalubale ba ga matasan yau ba har ma ga al'ummar kasar da ta gaba.
Ya ce gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping na son, kamar ka ce ta kirkira wani sabon mutumin China, wanda yake da dukkanin wasu dabi'u da suka dace da kuma jajircewa.

Asalin hoton, Reuters
A kwanan nan hukumomi suka hana fitattun mawaka 'yan daudu da masu kalamai na batsa ko wadanda suka saba wa al'ada daga tarukan nishadi
Dan jarida Josh Ye, wanda yake aiki da jaridar Hong Kong ta South China Morning Post, ya ce gwamnati tana sanya dokokinta a dukkanin abubuwan da suka shafi wasanni da nishadi.
Ya ce, a yanzu hukuma na sanya ido sosai a kan kafofi da dama na wasanni. An sanya doka a kan abubuwan da ake yi kai tsaye. An hana tallata wasannin kwamfuta na waje, wadanda ba a yarda a yi a China ba, in ji shi.
To amma kuma wasannin kwamfuta a China babbar harka ce, to mai zai kasance tasirin wadannan matakai?

Asalin hoton, Getty Images
‘Mutane da yawa suna yin wasannin'
Charlie Moseley wanda ke kirkiro wasannin kwamfuta na wani kamfani mai bayar da tallafi na Amurka, American Games, wanda ya yi aiki sama da shekara goma a Chengdu, daya daga cikin birnen da aka fi yin wasannin kamfuta a China, ya ce wasan kwamfuta ya bunkasa sosai a China, inda miliyoyin mutane suke kallo.
Ya ce a yanzu, kamfanin Tencent na gina filayen wasanni na biliyoyin dala domin kallon wasannin kwamfuta kawai.
Kuma ya ce mutanen ma da za ka dauka ba su da wata alaka da wasannin ma a yanzu sun yi nisa a ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Mosley ta ce a sau da dama China na karbar nauyin gasar wasannin kwamfuta na duniya, kuma ta zama kusa a duniya a wannan fage.
Ya kara da cewa 'yan kallo da yawa wadanda ba ma sa wasan sukan kama tashoshin da ake yi kai tsaye suna kallon wasannin.
Ellie Gibson, 'yan jarida da ke zaune a Birtaniya, ta ce sanya ido da dokokin da China ke yi a kan wasannin wanda abu ne da ya shafi al'adar rayuwar mutane ka iya zama daya daga cikin abubuwan da suka janyo wa wasannin farin jini.
kuma hakan ka iya zama dalilin da ya sa wasannin na kwamfuta na kwararru suka zama manyan wasanni ta hanyar da ba ba a dauka ba ma a kasashe da yawa.

Asalin hoton, Ellie Gibson
'Abin da ba shi da kyau'
Ta ce ina ganin abu ne mai kyau, mutane za su rungumi wasannin kwamfuta saboda kawai an ce abu ne da ba su da kyau, kuma an yarda ka yi su ne kawai na dan lokaci.
Dukkaninmu muna jin dadin yin abin da ba shi da kyau a wurinmu, kamar yadda ta sheda wa BBC.
Ta ce tana ganin wannan wata hanya ce da za ta ma sa wasannin su kara daukar hankali da jan ra'ayin jama'a
Gibson na ganin wadannan matakai za su iya sauya alakar China da yin wasannin.
Ta kara da cewa: "Ba a barin yara su shiga gasa sosai a China. Saboda haka abin shi ne, idan ba sa yin wasanni sosai lokacin da suke kanana har tsawon shekaru, wasannin ba za su zama wasu abubuwa da za su kasance na rayuwarsu ba.
Ta ce to wannan ke nan zai sa a samu wani rukuni na masu gasar wasanni ke nan? Wasannin za su mutu ke nan, saboda an daina domin yara ba sa yi sosai?
Maurice Stückenschneider, wani kwararre a wasannin kwamfutar kuma mai koyar da wasan ( League of Legends) yana ganin sabbin matakan za su yi tasiri a kan ci gaba da kasancewar China gwarzuwa a fagen, saboda a cewarsa wasannin kamar sauran wasanni ana renar gwanayensu ne tun suna kanana, wato dai ba a fafe gora ranar tafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Ya ce, ana yin wadannan wasanni a matakin 'yan koyo da kuma na wadanda ba cikakkun kwararru ba a Turai da kuma nahiyar Amurka ta Arewa. To amma a China abin ya fi samun karbuwa da tsari mai kyau.
Kungiyoyi da yawa na China ba kawai suna da tawagar 'yan wasa ta biyu ne ba kadai har ma ta uku da kuma ta kananan 'yan wasa suna da ita, sun ba wa abin muhimmanci sosai.
Matasan 'yan wasa da yawa suna farawa ne tun daga shekara 14 zuwa 15, amma kuma a Turai yawanci suna farawa ne daga shekara 16 zuwa 17.
Stückenschneider ya ce kungiyoyin China sun kasance zakaru a gasar a wasanin duniya kusan shekara hudu, inda suke nuna bajinta a wasannin.
Ya yi amanna cewa za a ga tasirin wannan mataki nan da shekara biyu ko uku, lokacin da gwanayen wasan na yanzu wadanda yawanci 'yan shekara 16 zuwa 17 ne sun yi gaba sun kai matakin kwararru.

Asalin hoton, Getty Images
‘Chinata daban’
To amma kuma wasu iyayen sun goyi bayan matakan takaita wasannin; iyayen da suka damu da yadda 'ya'yansu ke zama masu yawan yin wasan da damuwa da lafiyar idanun 'ya'yan da lokacin da suke kasancewa a waje, in ji Gibson
Kamfanonin fasaha na China, wadanda suma matakin zai shafe su, kusan sun goyi da bayan matakin jam'iyyar duk da yadda abin zai iya shafarsu.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Tencent ya fada a wata sanarwa cewa: "Mun yi amanna da yin wasanni masu amfani ga lafiya, kuma muna daukar duk abin da ya shafi lafiyar jiki da kwakwalwa ta kananan yara da muhimmanci.
Sanarwar ta kara da cewa, "muna maraba da dokoki da ka'idojin da hukumomin da ke sa ido za su kawo, kuma za mu yi aiki tukuru domin kiyayewa da dokokin da suka shafi wasannin na yara.''
Amma kuma Moseley ya ce, yanayin da ake ciki a fannin kamfanonin ba me dadi ba ne, kuma rashin tabbacin daidaiton matakan ka iya sanya kamfanonin su karkata kasuwarsu zuwa wasu kasashen.

Asalin hoton, Getty Images
'Burin Akida'
To amma Moseley na daga cikin kwararrun da suke ganin China ta sauya manufa dangane da alkiblarta ta tattalin arzikinta.
Ya ce: “A da bunkasar tattalin arziki ita ce abar da gwamnatin kasar ta fi ba fifiko. Yanzu kuma ta karkata ga manufa ta akida.
Abin tambaya ga gwamnatin shi ne: za mu bar tattalin arzikin ya ci gaba da bunkasa ta hanyar da muka yi amanna ba ta da kyau ga kuma hadari ga matasa? Amsar hakan ita ce a'a.
Moseley ya ce : “Wannan ba ita ce Chinar da na zo ba. China ta doshi wani wuri daban yanzu.”
Tsang ya yarda cewa a yanzu burin jam'iyyar Kwaminisancin na kankane iko da komai ya sha gaban batun tattalin arziki.
Ya ce: “Xi Jinping ya yanke shawarar cewa tattalin arzikin kasar ya yi karfi da girman da zai iya dawo da ikon gwamnati ta yi yadda take so.

Asalin hoton, Getty Images
* This story was originally aired on the BBC World Service Business Daily programme. BBC Chinese’s Yitsing Wang contributed to this report.






