Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kamfanin KFC ya fuskanci suka kan karancin dankali a Kenya
A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, a wannan karon 'yar jarida Waihiga Mwaura ta rubuto maƙala kan sabuwar taƙaddammar da ake fuskanta a Kenya kan dankalin kamfanin abinci na KFC wacce ke da alaka da yin noma a Kenya.
Yawancin mutane kamar ni sukan je KFC idan suna neman abincin gaggawa mai cika ciki idan ba su da lokacin yin girki.
Cin dankali mai zafi zai iya janyo tunani kan shekarun da aka yi ana kasuwancin haɗaka tsakanin kasashen duniya. Amma ban taɓa tunanin cewa kasuwancinsa na da alaƙa da wata siyasa ko hada-hadar kayan da ake nomawa da kuma matsayar Kenya a cikin zancen ba.
A wannan makon, an yi ta ce-ce ku-ce kan hada-hadar kayan abinci a duniya bayan da KFC ya ce ba zai iya bai wa kwastamominsa dankali ba saboda yadda ya kasa shigo da dankalin da ya saba amfani da shi daga ƙasar Masar.
Maimakon dankalin, yanzu ana bai wa kwastamomi wani abincin Kenya da ake yi da masara, wannan dai ba abin da mutane suka saba ci a KFC ba ne.
Kamfanin na KFC ba ya sayen dankali a ƙasar Kenya duk da cewar akwai shi a ƙasar kuma manoma na sayar da shi a farashi mai sauki.
Dankalin da ke da dadin ci
A Kenya, dankali shi ne abinci na biyu bayan masara da aka fi nomawa a kasar.
Matsalar ita ce, masu samar da kayan abinci a kasar ta Kenya ba su karanta daya daga cikin dokokin KFC mai tabbatar wa kwastamominsa cewa ''zai samar da abincin da bai da matsala ga lafiyar kwastamomi ba," in ji shugaban kamfanin mai kula da reshen Gabashin Afirka Jacques Theunissen a lokacin da yayi hira da Jaridar Standard.
Amma dai ya ce akwai wasu abubuwa da suke saya a Kenya, kamar burodi da fulawa da askirin kuma kamfanin ya ce yana kokari wajen karfafa dangantaka wajen sayen kayan Kenya.
Lamarin da ya sa ake ta zagin kamfanin a kan shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa kamfanin ya fitar da sanarwar cewa zai nemo inda zai sayo dankali a Kenya.
Yayin hakan sai sauran kamfanoni masu sayar da abinci irinsu Chicken Inn suka fara fitar da sanarwa inda suke nuna wa duniya cewar suna da isashshen dankalin da suke siya daga Kenya.
Burker King ma ya ce yana da isashshen dankali.
Idan dai wadannan sauran kamfanonin za su iya sayan dankalinsu a Kenya, har yanzu ba a gane dalilin KFC na kin sayan dankali a Kenya bayan shafe shekara 11 yana sayar da abinci a kasar.
Shugaban masu noma dankali a gundumar Nyandarua, Frances Kimemia ya tofa albarkacin bakinsa kan batun inda ya ce manomansa na samar da ingantaccen abinci.
Ya ce matsayar KFC ba ta kyautawa manoma ba. Fushin mutane ya fara sauka amma wannan takaddamar ta tona wasu matsaloli a cikin yanayin hada-hadar kayan abincin Kenya kuma yadda ba a yi wa manomanmu na gida adalci.
Dogaro ga kayan abincin kasashen waje
Yanayin samar da kayan abincin da muke amfani da shin a da alfanu kuma yana da illolinsa.
Amma idan Kenya ta rufe iyakokinta na wata daya kawai, yawancin abubuwan da muka fi son ci, ba zamu same su ba.
Alal misali, a shekarar da ta gabata kawai an kashe dala Miliyan 250 wajen shigo da kayan abinci daga kasar Uganda.
Abubuwa da dama da muke amfani ana shigowa da su ne ne kuma a sayar bayan saka riba, abubuwan kamar kwai da zuma da masara da wake da dankali da kayan madara da dai sauransu.
Masana sun ce kayan abinci da dama sun fi sauki a Uganda idan aka kwatanta su da yadda ake sayar da su a Kenya.
Amma kuma za a iya alakanta matsalar da yadda mutane suka kallon noma. A Uganda mutane da dama sun karbi aikin noma amma a Kenya mutane sun fi son yin aikin ofis.
A lokacin da nake yin rahotanni kan zaben da aka yi a Uganda na tattauna da manyan mutane sosai wadanda yawancinsu ke zama a wajen birnin Kampala inda suke noma abincin da suke ci. Idan wadannan 'yan siyasar suna zaune a Kenya ne, za su zauna ne a unguwar masu kudi da ke da gidajen zamani.
Abu daya ne idan ka kalli kwatanta yanayin noman Kenya da ta makwabciyarta Tanzania.
Rashin son yin noma tare da kuma matsalar rashawa da cin hanci na cikin abubuwan da suka sa mutane ba sa yin mamaki idan aka ce musu an sayo kifi daga China ko suga daga Brazil ko kuma taba daga Turkiyya.
A yanzu dai Kenya ba za ta iya bayar da farashin da ya fi na sauran kasashe ba.
Amma a nan gaba akwai yiwuwar cewa Kenya za ta iya zama cibiya inda ake samar da ingantacen kayan abinci. Samar wa KFC irin dankalin da take so, hanya ce ta zama wannan cibiyar.
Sai dai a wurare da dama a Kenya inda ake samar da kuma shirya kayan abincin, kamfanoni mallakar kasashen waje ne da alhakinsu, hakan na nufin kudin da ake samu zai fita kasar Kenya ne a karshe.
Yanzu da lokacin zabe ya fara tunkarowa a watan Agusta mai zuwa, masu neman takara na ta yin alkawarin ayyuka amma har yanzu bamu ji yadda suke da niyyar gyara yanayin noman kasar Kenya.
Zai yiwu a ce wasu daga cikin 'yan siyasarmu na da burin amfani da abubuwan da suka kawo ci baya a kasar wajen kawo gyara.
Ba lallai a samu sauyi cikin gaggawa ba, amma a yanzu idan na ci dankalina daga KFC dole sai tunanin yanayin hada-hadar kasuwancinmu ya cika kai na.
Wasu labaran masu alaka: