China: Me ya sa wasu ke ganin kananan ido ba sa cikin siffofin kyau?

Asalin hoton, Weibo
- Marubuci, Daga Waiyee Yip
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
"Shin ban cancanci zama 'yar China ba, kawai saboda ina da kananan idanu?"
Wannan ita ce tambayar da mai tallata kayan kawa 'yar China Cai Niangniang ta wallafa a kwanaki a shafin sada zumunta, bayan wani tsohon hoton tallan da ta yi ya sake wadari a shafukan.
An kwashe kwanaki ana ta sukarta da kalaman da ba su dace ba, da batanci kuma da gangan, kawai saboda ta yi tallan kayan kwalam da wani kamfanin China ya yi mai suna Three Squirrels.
Mene ne laifinta? Kananan idanu.
Wasu daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta caccakar ta, hakan ya sanya dole kamfanin ya cire tallan tare da bai wa abokan hulda hakuri a kan abin da suka kira "daga mana hankalin da aka yi."
Sai dai Mis Cai ta ce ita ba ta san mene ne laifinta ba da ake cin zarafinta a shafukan sada zumunta, alhalin aikinta kawai take yi a matsayin mai tallan kayan kawa.
"A wajen iyayena na samo kamannina," in ji Ci, mai shekara 28, a sakon da ta wallafa a shafin Weibo na kasar.
"Shin na wulakanta China ne a ranar da aka haife ni da irin kamannin da nake da su?"
'Kasashen turai ba su da sauran abin fada'
Ainihin tallan da aka dauka a shekarar 2019, wasu masu sa ido ne suka bankado shi, a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan yadda ake yi wa 'yan China wulakanci a shafukan sada zumunta saboda kamanninsu.
A watan Nuwamba, wata shahararriyar mai daukar hoto a China, ta nemi afuwa kan abin da ta yi bayan bullar hotunan kayan kamfanin Dior na Faransa, bayan an caccake ta. Ta fito a matsayin mai talla 'yar China da kananan idanu.
A baya bayan nan an samu wani abu makamancin haka, kan tallan motar zamani samfrin Marsandi-Benz da wani na kamfanin Gucci da su ma suka yi amfani da mata masu kananan ido.

Asalin hoton, Chen Man/Dior
Wasu na ganin me ya sanya ba a dauko wasu daga cikin 'yan China da suka fi Cai manyan idanu dara-dara da farar fata ba, wadanda su ne shika-shikan cikar kyawu a China.
A baya bayan nan gidan talbijin na China ya yi sharhi kan hakan, tare da fadada bayanin cewa akwai gagarumin bambanci tsakanin yadda kasashen turai ke siffanta kyawun mace, a yanzu sun daina duba wadannan abubuwa. Musamman amfani da mata masu kananan idanu wanda a baya ba sa yin hakan.
"Kasashen turai ba su da wani karfin fada a ji a yanzu," in ji wani rubutu da aka yi kan hakan.
"'Yan China ba sa bukatar su bi wannan tsarin, kan abu kaza ne ake gane mace mai kyau da shi.''
Ya kamata kamfanin Three squirrels na China ya san cewa abokan huldarsu ba sa saurarawa kan abubuwa irin hakan.

Asalin hoton, Getty Images
A masana'antar fina-finai ta Hollywood, an dauki hoton fitacciyar jaruma Fu Manchu da kananan idanu sirara inda ta fito a matsayin "yellow peril", wani salon nuna wariya da al'adar mutanen yankin Asiya ke yi wa turawa barazana.
"Tabbas akwai tsohon tarihin amfani da masu knanan idanu 'yan yankin Asiya a tallan kayan kawa," in ji Dr Liu Wen na cibiyar koyarwa a Taiwan a hirarsa da sashen BBC China.
Sai dai kafewar da 'yan China suka yi na amfani da wata kyakkyawa daya tilo a tallan kayan kawa na kasuwar duniya, ya ci karo da muhawarar da ake tafkawa a wannan lokaci kan fitowarr mutanen yankin Asiya a kafafen yada labarai.
Masu sanya ido na ganin yayin da aka fahimci wasu abokan hulda ka iya jin haushi, a wani bangaren kuma ana muhawarar ba sai an yi amfani da wani sashe na 'yan China ba.
"Yin watsi da masu kananan ido abu ne mai matukar hadari, saboda tamkar an yi watsi da halittarsu ne," in ji Dr Luwei Rose Luqiu, malama a jami'ar Baptist da ke Hong Kong.
Kwararru sun sake nuni da cewa bisa al'ada, ana kallon mata masu kananan idanu a matsayin kyawawa a China, ana kuma yi musu alfarma fiye da kowa. Misali, wani zane da aka yi amanna da cewa lokaci ne da China ke tashe ta fannin zane-zane da al'adu wato lokacin Tang Dynasty daga shekarun 618 zuwa 907 AD, ya nuna mata masu dogo da kananan idanu.
"Duk da cewa akwai mata daban-daban, an fi kaunar mata masu kananan idanu a China fiye da sauran mata," in ji Dr Jaehee Jung, wani kwararre a jami'ar Delaware.
Duban da ake yi wa masu dara-daran idanu a halin yanzu a matsayin siffofin kyawawa, ta yiwu kasashen yamma ne suka kawo salon. Wasu kwararru na ganin an fara samun sauyi a siffofin kyawawa a shekarun 1970, lokacin da China ta budewa kasashen duniya kofar shiga a dama da su.
Dr Jung ya ce mata a China na amfani da sigogin kyawun mace da kasashen yamma ke amfani da su, wajen kambama kyan macen musamman a shafukan sada zumunta.
A wannan zamanin, kasuwar mata masu manyan zagayayyun idanu ce ke daukar hankali a China, lamarin da ya ke sanyawa wasu matan yin tiyatar kara kyau, domin a kara fito musu da idanu, ciki har da kirkirar wani layin a cikin ido domin ya yi dara-dara.
Sai dai ga Mis Cai, mai tallan kayan kawar da ke tsakiyar cece-kucen na yanzu, ta na fatan mutane za su sassauta su zamto masu kara da kyautatawa, su daina jefarta da kalaman da ba su dace ba, ko da kuwa kamanninta ba su gamsar da su ba.
"Haka nan aka halicce ni da kananan idanu, kai a zahiri idan ka ganni sun fi wanda ake gani a hotuna na kankanta, kowanne dan adam ya na baiwar da aka halicce shi da ita!"
Karin bayani daga Sylvia Chang ta BBC Chinese.









