Bashir Tofa: Abu biyar da ba ku sani ba game da masanin kimiyyar samaniya

"Kowane rai sai ya ɗanɗani mutuwa!" Kamar yadda Allah Ya fada a Al-ƙur'ani mai girma.
A ranar Litinin 3 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2022 ne Allah Ya karbi rayuwar Alhaji Bashir Othman Tofa, tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar NRC a shekarar 1993.
Rasuwar tasa ta ɗimauta da yawan mutanen Najeriya, saboda irin rashin gwarzo da suke cewa ƙasar ta yi.
Mutane da dama tun daga kan shugaban ƙasar Muhammadu Buhari har zuwa masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ta miƙa saƙon alhini da ta'aziyyar wannan "gwarzo."
A shafin Facebook kaɗai an yi amfani da sunan Bashir Tofa fiye da sau 33,000, ciki har da neman ƙarin bayani kansa da gidansa da batun rasuwar tasa.
Can a shafin matambayi ba ya ɓata na Google kuwa, sunan Bashir Tofa ne abu na uku da aka fi dubawa, inda ake nemi bayani a kansa fiye da sau 20,000.
Mutane da dama sun san Bashir Tofa ne a matsayin gogaggen ɗan siyasa kuma ɗaya daga cikin dattawa masu faɗa a ji a arewacin Najeriya.
Sai dai marigayin yana da wasu abubuwan da ba lallai kowa ne ya san su ba, kuma ya yi shuhura a waɗannan fannoni.
A wannan maƙalar, BBC Hausa ta yi duba kan wasu abu biyar da wataƙila masu karatu ba su sani ba a game da Marigayi Bashir Othman Tofa.

Masanin Kimiyyar Sararin Samaniya
Malam Bashir Tofa gogaggen masanin kimiyyar sararin samaniya ne, wanda ya dinga bincike da rubuce-rubuce a kan wannan ɓangare.
Ba a bincike da rubutun kawai ya tsaya ba, masanin ya dinga ƙoƙarin bayyana kimiyyar sararin samaniyar a tsarin Al-ƙur'ani tare da fito da al'ajuban da ke tattare da hakan.
A wani littafinsa mai taken "Kimiyyar Sararin Samaniya", akwai wajen da ya ɗauki mai karatu ya zagaya da shi a sararin samaniya, tun daga Unguwar Rana, wato Solar System har Birninmu na Milky Way Galaxy da ma wajen birnin zuwa Virgo Supercluster.
Wannan zagaye na ƙirƙira da ya yi da mai karatu bisa la'akari da abin da bincike ya gama ganowa dangane da sararin samaniya da halittun cikinta.
Zai yi matuƙar wahala ka karanta littafin nan na Kimiyyar Sararin Samaniya da ke cike da bayanai kan tsarinta da dokokinta da halittun cikinta ba tare da ka ƙara miƙa wuya ga Allah SWT ba, da kuma ƙaruwar Tauhidi.
Wasu labarai masu alaƙa

Marubuci
Malam Bashir Tofa marubuci ne sosai, kuma yawanci rubuce-rubucensa da Hausa ya yi su, sai dai akwai na turancin ma.
Ya rubuta littattfai tun daga abin da ya shafi addinin Musulunci da na ban dariya da ban mamaki da labarin Aljanu.
"Ya yi rubutu a harkar addini sosai," in ji Alhaji Ahmad Aminu, wani amininsa tun na ƙuruciya.
Daga cikin littatafansa akwai:
- Kimiyyar Sararin Samaniya
- Kimiyya da Al'ajuban Alƙur'ani
- Tunaninka Kamanninka
- Rayuwa Bayan Mutuwa
- Takaitaccen Tarihim Islam
- Mu SHa Dariya
- Gajerun Labarai
- Amarzadan A Birnin Aljanu
- Amarzadan Da Zoben Farsiyas
- Fatuhu Dan Aljan
- Mutane da Gurare A Islam
- Muna Ta Dariya, da sauransu.

Latsa hoton da ke ƙasa domin kallon bidiyon wata tsohuwar hirarmu da Bashir Tofa:
Babarbare
Kamar yadda yake a sunan marigayin, ɗan garin Tofa ne a jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar. Sai dai aminin nasa Alhaji Aminu ya ce asalin kakanninsa Barebari ne "amma shi da iyayensa duk haifaffun kuma mazauna ƙasar Kano ne a garin Tofa.
"Kakan kakansa Ɗan Adalan Tofa ne, sannan wani ɗan Baffansa ma mai suna Tsoho Tofa ya riƙe muƙamin, kafin daga baya sarautar ta bar gidansu."
Wannan dalili ne ya sa aka yi masa tsagen Barebari a fuska kamar yadda aminin nasa ya ce.
Ya kara da cewa "da yawa daga cikin ƴan gidansu kamar yayarsa da ƙanwarsa mai bin sa da wasu ƙannensa da ma wasu daga cikin ƴaansu duk an yi musu zanen."
Karin labaran da za ku so

Karatu
Alhaji Bashir ya yi karatunsa na firamare a Shahuci Firamare, sannan ya je ƙaramar sakandare ta Gwale daga can ya tafi babbar sakandare a Kwalejin Rumfa duk a garin Kano.
Amininsa ya ce daga nan ne sai ya tafi Ingila ya yi karatun digiri na ɗaya da na biyu a fannin Tattalin Arzikin Kasuwanci.
"Ya zauna a Ingila tsawon lokaci, har ma a lokacin mukan je ofishin BBC wajen abokanmu ma'aikatan sahsne Huasa ƴan Najeriya don yin zumunci. To daga baya mu ma (har da shi marigayin), muka dinga yin aikin wucin gadi na ɗan lokaci a BBC Hausa ɗin.
Kazalika Alhaji Bashir ya yi karatun addini sosai tun yana ɗan shekara bakwai kama daga kan Alƙu'ani da Hadisai da Shari'a har kan Nahawu a cewar aminin nasa.
Iyalansa
Marigayin wanda ya rasu yana da shekara 74, ya bar mace ɗaya da ƴaƴa shida, mata uku da maza uku. Sannan ya bar tarin ƴan uwa.
Aminin nasa ya kuma bayyana shi a matsayin mutum mai matuƙar son tsafta da ƙawa, "shi ya sa ma ko yaushe za a ga gidansa kamar sabon gini ake yi, amma ba haka ba ne yawan gyara ne kawai da yake sa wa a yi."












