Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sauye-sauyen da Gasar Tseren Mota ta F1 za ta kawo a Saudiyya
- Marubuci, Daga Christian Hewgill
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Newsbeat
- An wallafa
Ana shiri gudanar da gasar tseren mota mafi girma a duniya. Za dai a sha kallo fiye da irin wanda ake gani a fina-finan da ake gani a manhajar Netflix.
Akwai abubuwa da yawa da za a so a tseren Formula 1. Kai abubuwan da za su faru a wannan gasa sun shallake tunani, ba kuma safai ake ganin su ba.
Amma tseren da za a yi a kasar Saudiyya na dauke da abubuwa daban-daban.
"Na tafi ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba," in ji dan jarida Hazel Southwell mai aika rahoto kan wasannin tseren mota a hirarsa da shirin Radio 1 Newsbeat.
Wannan ne karon farko da ake wasan tseren mota na F1 a kasar Saudiyya, mako guda da dakatar da wasan a Qatar - yawanci dai ana nuna damuwa kan yadda kasashen biyu ke shan suka kan zargin take hakkin dan adam, musamman ga mata.
Saudiyya dai na sahun gaba cikin kasashen da ke zartar da hukuncin kisa a duniya. An yi kiyasin an yanke da zartar da hukuncin kisa ga mutum 40 daga watan Junairu zuwa Yuli, kamar yadda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana.
Sai dai Hazel na daga cikin masu tunanin tseren motoci zai kawo sauyi a kasar Saudiyya.
"Abu ne mai matukar wuya shirin hakan. Ya zo da kalubale daban-daban, abubuwa da dama sun gifta a raina," in ji Richard Morris, fitaccen dan Luwadi a Birtaniya da baya boye abin da yake yi, kuma mai wasan tseren mota a hirarsa da Newsbeat.
Tuki domin kawo sauyi
A kasar Saudiyya, ana hukunta 'yan Luwadi da Madigo da bulala ko zaman kurkuku.
"Muna bukatar karbar yadda lamura ke gudana," in ji Richard.
Richard yana tunanin ta yiwu yin wasan tseren F1 a Saudiyya, ka iya sauya abubuwa musamman idan ana batun lamarin da ya shafi hakkin dan adam.
Tuni akwai misalan da ke nuna watakil hasashensa ya tabbata.
Misali kamar Sebastian Vettel.
Direban na Aston Martin ya bayyana kansa a matsayin babban amini, da ba ya jin shakkar nuna goyon baya ga 'yan luwadi da madigo.
Aikawa da saƙo
A tseren motoci na Hungary zakaran tseren Lewis Hamilton ya soki matakin Hungary na gudanar da ƙuri'ar raba gardama kan dokar da ta ƙunshi haramtawa ko kuma nuna goyon baya ga masu neman jinsi ɗaya ko sauya jinsi ga ƴan ƙasa da shekara 18.
Lewis da kansa ya yi bikin nasara a Qatar ɗauke da tuta a hular kwano. Kuma zai yi haka a wannan ƙarshen makon - yana amsa cewa ba ya jin daɗin tsere a Saudiyya - yana bayyana cewa rayuwar ƴan maɗigo da luwadi a ƙasar "na da ban tsoro."
Shugaban Formula 1 shi ma kansa ya yi fatan cewa wasanni za su iya haddasa sauyi a waɗannan wuraren.
Kuma Richard Morris shi ma ya amince.
"Wannan ya aika sako ga masu goyon bayan maɗigo da luwaɗi kamar Lewis, Sebastian da tawagar Aston Martin su tafi su yi tsere a yanki kamar Saudiyya.
Wasu masu suka kamar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam - suna ganin yin tseren mota a Saudiyya, F1 kamar nuna goyon baya ne ga yadda ake tafiyar da abubuwa a ƙasar.
Amma Richard ya ƙi yarda.
"Na yi matukar farin ciki a wajen babban jami'in wasanni a wani taron manema labarai."
Ƴan jarida mai aiko da rahotanni kan tseren motoci Hazel Southwell ta yi aikin aiko da rahotannin gasar Formula E, gasar fasaha, da aka fara a Saudiyya daga 2018.
"Martanina ya kasance cikin fushi a makance," kamar yadda ta faɗawa Newsbeat.
A 2018 mata a Saudiyya sun kasa tuƙi kuma an hana su zuwa kallon wasanni.
Amma Hazel, yar maɗigo ce da ta fara zuwa yin aiki amma lokacin ra'ayinta ya fara sauyawa.
"Ina shekara 32 lokacin da na fara zuwa wurin taro a ƙasar. Ban sani ba, amma wannan shi ne adadin shekarun wani ɗan Saudiyya da zai tafi wuri irin wannan.
Amma duk da Saudiyya tana cikin ƙasashe masu arziki a yankin, saboda arzikin mai, amma miliyoyin ƴan ƙasar na fama da talauci.
"Akwai mutum miliyan 34 a Saudiyya. Ba mu san abubuwa da yawa game da su ba," in ji Hazel tana mai cewa yanayin rayuwa "na da matsala"
Tana ganin kawo manyan wasanni a ƙasar zai taimaka wajen inganta haƙƙin ɗan adam da kuma habaƙa wasanni.
"Domin karɓar bakuncin gasar tseren mota ta FIA, Saudiyya ta bar mata suna tuki," a cewar Hazel.
Reema Juffali tuni ta zama ƴan Saudiyya ta farko da ta kasance ƴar tseren mota a matakin ƙwararru. Yayin da wasanni ba za su taɓa sauya komi ba, Hazel na ganin za su yi.
"Ya komi a rufe yake a Saudiyya, babu abin da ya sauya a tsawon shekara 40," in ji ta.
"Akwai zuwa wani lokaci, sauye-sauye na faruwa domin idon duniya."
Hazel ta kuma fito da cewa ana tseren Formula 1 a wasu ƙasashe da masu fafutikar kare haƙƙi ke adawa.
"Akwai wasu yara a keji a Amurka. Suna tsare kuma su kaɗai," in ji ta.
"Amma mun san yawancin Amurkawa da al'adunsu. Don haka mun fahimci dalilin da ya sa za mu kai gasar tseren motoci a can," a cewarta.
"Amma ba mu san komi ba game da Saudiyya. Ba ma kallon fina-finan Saudiyya a ko da yaushe."
Hazel ta ce tana da ƙawaye a Saudiyya waɗanda za su ji daɗi suna ganin duniya na kallonsu.
"Duk lokacin da na je Saudiyya, nakan ji daban a matsayina ta ƴar maɗigo. Amma kowa na buƙatar wasanni. Kowa na son nishaɗi."