Zamantakewa: Girki ga mace a aure, wajibi ko zaɓi?

An wallafa

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 21 din, shirin ya yi duba ne kan batun girki a aure. Dole ne mace ta yi ko kuwa ba dole ba ne?

A kwanakin baya an yi ta wata muhawara a shafin Facebook tsakanin matasa a cikin al'ummarmu kan batun girki a cikin aure.

Kai ya rabu biyu, wasu na ganin girki a aure wajibin mace ne, wasu kuma suka dage cewa zabinta ne.

To da yake muna batun zamantakewa ne, lallai girki a zaman aure wani ginshiki ne.

Iyayenmu da kakannimu girki ya zame musu wani ado kuma abin tunkaho. Malama Tasallah Nabulusi Bako ta ce girki a wajen ƴa mace ado ne, kuma abin alfahari ne sosai.

"Gaskiya ni ban yarda girki zaɓi ba ne, kyautatawa ce kuma wajibi ne mace ta yi wa mijinta, tun da shi ya fita ya nemo to ita kuma ai kamata ya yi ta dafa, kin ga an samu maslaha kenan.

"Mace na iya mallake zuciyar mijinta tsaf ta wajen yin girki," in ji Malama Tasallah.

Shi kuwa wani magidanci Muhammad T Shehu ce min ya yi a ganinsa girki ba wajibi ne a kan mace ba.

''Idan aka yi la'akari da yanzu zamani ya canja dole a dinga ɗagawa juna ƙafa, musamman yanzu akwai mata masu zuwa makaranta da aiki da sauran hidimomi, to ya kamata a ce ana samun maslaha tsakanin mata da miji kan hakan."

Girkin mace a gidan aure - Fahimtata ban ce lallai iyakar gaskiya kenan ba

A ganina wannan maslaha ta shafi mutum biyu ne kawai da kuma yadda suka tsara ta a tsakaninsu.

Kowa da irin tsarin gidansa da yadda yake tafiyar da abubuwa. Don haka babu bukatar musu, sai a bar ko wadanne ma'aurata su tsarawa kansu rayuwa yadda suka fi sonta.

Misali, wani maigidan a tsarinsa so yake matarsa ta zama tsantsar 'yar hutu sai dai ta wanke goma ta tsoma biyar. Irin wannan mijin zai iya dauko mata ƙwararren mai girki da sai dai in an gama abinci a jere a teburi in ta gama a kwashe kwanuka.

Wani kuma yana da irin wannan tsarin amma a gargajiyance ta yadda masu tuwon ba na zamani ba ne amma sun ƙware a abinci, haka za su dafa a juye a kwanuka a kawo gaban Hajiya.

Akwai kuma gidan da ko da halin daukar masu girki ita matar mai tsananin sha'awar girki ce. Ta fi so kawai ta ganta a kitchen tana dafawa tana saukewa, ko da don sha'awa ba don lada ba, kuma ko da mijinta ya fi son ta a 'yar hutu. Irin wannan mafi a'ala shi ne mijin ya bar ta da tsarinta.

Akwai wacce ita kuma hutun take so amma kuma mijin bai da halin da zai daukar mata mai yi mata wannan hidimar, shi kuma dole zai fita ya nemo.

To a bisa sulhu mai kyau dole matar ta yi hakuri ta karbi ragamar dafawa ta kuma ta yi masa addu'ar samun budi har wata rana ya kawo masu dafawa ya ce "to darling yau ga ranar hutunki ta zo."

Sannan akwai ma'auratan da bisa tsari su daga matar har mijin sun yarda cewa shi ne mai nemowa ita kuma mai dafawa. To kun ga a nan sai a bar su da tsarinsu babu ta da jijiyar wuya.

Wasu kuma saboda tsarin aikinsu gaba daya sai suka yi tsarin shiga kitchen din tare su dafa abinsu ko a wasu lokutan su fita gidan cin abinci. To wadannan ma sai a bar su kan turbarsu.

A karshe, a al'adance kasar Hausa abu ne mai kyau mace ta iya girki. Idan har ta yi aure aka yi sa'a tsarinsu ita da mijin shi ne ta dafa abincin to ka ga babu mi'ara koma baya.

Idan kuma ya kawo mata masu dafawa shi kenan huta roro sai ta mike kafa ta ci duniya da tsinke kuma ta yi fatan hakan ya dore.

Girki duk sonka da shi akwai shi da cin rai sosai a wasu lokutan.

Idan kin san ba ki son girki to tun kafin ku yi aure ki gaya masa, idan ya ga tsarin ya masa shi kenan. Idan bai gamsu ba sai a rabu kowa ya lalubo mai irin tsarinsa.

Sai mako na gaba kuma inda za mu hadu a batun mata masu hadewa maza kai.

Wasu na baya da za ku so