Sarkin Bungudu: Wata ɗaya babu labarin Sarkin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru

Asalin hoton, Other
Al'ummar masarautar Bungudu a jihar Zamfara na ci gaba da jimami da jiran tsammani da rashin tabbas kan makomar Sarkin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru da ƴan bindiga suka sace.
Kusan wata ɗaya kenan babu labarin Sarkin mai daraja ta ɗaya a jihar Zamfara wanda aka sace kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.
Akwai ɗan sanda ɗaya da aka kashe lokacin da ƴan bindigar suka yi awon gaba da sarkin a ranar 14 ga watan Satumban da ya gabata.
A ziyarar da BBC ta kai fadar sarkin Bungudu, mutanen masarautar sun ce har yanzu babu wani labari game da Sarkin nasu.
Sakataren masarautar Bungudu, Alhaiji Usman Ibrahim ya ce suna cikin hali na kaɗuwa yadda babu wani labarin sarkin.
Ya faɗawa BBC cewa tun bayan faruwar lamarin ba su da cikakken bayani kan halin da Sarkin yake ciki, musamman ma saboda rashin sadarwa a wasu yankunan jihar.
Fadawan sarkin sun ce suna cikin tashin hankali saboda ba su san halin da sarkin yake ciki ba.
"Gaskiya ba mu cikin jin daɗi domin wani lokaci ko bacci ba mu iya yi domin mun san dadinsa, ba wani abin da muke tunani baya ga gare shi," in ji wani bafaden masarautar Bungudu.
Ya ƙara da cewa lamurra sun tsaya tun da aka sace sarkin - "fatanmu Allah ya dawo da shi lafiya."
Fiye da wata ɗaya kenan da aka datse layukan waya da hanyoyin sadarwa na intanet a sassan jihar Zamfara, ko da yake an buɗe layukan daga baya a Gusau babban birnin jihar.
Sakataren masarautar Bungudu ya ce wasu mutanen masarautar da ke inda ba a katse layukan salula ne kawai ke magana da sarkin.
"Cikinsu babu wanda ya dawo gida - amma a labarin da muka samu gare su yana nan a raye," in ji shi.
Ya kuma ce kwamishinan yan sandan jihar Zamfara ya jajanta masu, amma a cewar sakataren masarautar, 'ba wani bayani da muka ji daga gare shi."
Rashin tabbas
Ƴan uwan sarkin sun ce kullum suna cikin zullumi da tsammanin sarkin zai dawo, tunanin ƴan bindigar za su sake shi.
Wani na kusa da sarkin Bungudu ya ce suna da yaƙinin cewa yana raye lokacin da ake magana da waɗanda suka sace shi. "Domin ɓarayin sun yi alƙawalin za su saki sarkin idan har an kai masu wasu kuɗi da suka buƙata."
"Ga alama yana raye amma babu tabbas. kafin a kai kuɗi na farko ana magana da shi. Ana tsammanin za a sako sarkin amma yanzu babu labarin shi."
"Tun lokacin da aka kai kuɗin babu wani ɗan uwansa na kusa da ya sake magana da shi," in ji wani makusancin sarkin na Bungudu.
Ya ce suna tunanin sun kasa yin magana da sarkin ne sakamakon katse hanyoyin sadarwa da aka yi a wasu yankunan Kaduna inda aka sace sarkin.
Ba wannan ne karon farko ba da ake samun rahotannin sace sanannun sarakuna a arewacin Najeriya, amma wannan ne karon farko da aka sace Sarki mai daraja ta daya, aka kuma shafe wata daya ba amo ba labarinsa.











