R. Kelly: Mawakin Amurka da aka samu da laifin lalata da yara mata

R. Kelly wearing sunglasses and a coat with a furry hood

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

"Rikakken manemin mata wanda ya yi amfani da shahararsa da kuma kudin da yake da wajen lalata kanana yara, da marasa gata da karfin fada a ji domin biyan bukatunsa.

Manemin mata ya yi amfani da damar da ya samu wajen cin zarafin mata kananan da manya da matasa a tsawon shekaru a wani salon lalata da muzgunawa."

Waɗannan su ne kalaman mukadashiyar Antoni Janar na yankin gabashin New York, Jacquelin Kasulis, bayan samun mawakin R&B R.Kelly da cin zarafi ta hanyar lalata.

Shaidu 11 - mata 9 da maza biyu - sun bada bahasi a shari'ar da aka shafe mako shida, suna bada bayanai kan irin cin zarafi da suka fuskanta a hannun mawakin.

Bayan kwanaki biyu ana tafka muhawara, alkalai sun samu Kelly da laifi kan dukkanin tuhume-tuhume 9 da aka gabatar a kansa. A ranar 4 ga watan Mayu za a yanke masa hukuncin da ka iya zama hukuncin dauri har karshen rayuwarsa.

Kelly, wanda cikakken sunansa Robert Sylvester Kelly, an same shi da amfani da ɗaukakansa da arziki wajen yaudarar mutane ta hanyar alkawarta musu samun dama haskawa a bidiyon wakokinsa. Da dama sun ce suna da karancin shekaru lokacin da aka yi lalata da su.

Kelly ya musanta duk wadannan zarge-zarge da aka gabatar a kansa.

Mawakin ya yi suna sosai a shekarun 1990 da wakarsa ta "Bump and Grind" da "Ignition". Sannan wakarsa da ta yi fice a duniya ya yi ta ne a 2004 "I Believe I Can Fly".

R Kelly

Asalin hoton, Getty Images

A lokacin da yake bada tarihinsa, R Kelly ya shaida cewa shi da kansa ya taba fuskantar cin zarafin lalata.

An kuma samu Kelly da karya dokar da ta haramta fataucin mata domin lalata a fadin Amurka.

An kuma sami shi da jogorantar gungun masu aikata irin wannan laifi, laifin da aka fi samu manyan kungiyoyin masu aikata manyan laifuka. Amma a wannan shari'a alkalai sun same shi da jagorantar lalata da mata da yara domin bukatun kansa.

A lokacin shari'ar, masu gabatar da kara sun shaida yada manajojinsa, jami'an tsaro da sauran mukarabansa suka rinka taimaka masa wajen aikata manyan laifuka.

Alkalan sun kuma saurari yadda Kelly ya samu wasu kundayen bayanai ta haramtattun hanyoyi domin auren mawakiya Aaliyah lokacin da take da shekara 15. Ta mutu sakamakon hadarin jirgi a watan Agustan 2001.

Iko da mutanen da ya lalata

A loakcin shari'ar, shaidu sun bayyana yadda mawakin ya rinka iko da juya rayuwar wadanda ya ke lalatawa, yana sa ido kan hada-hadarsu a Chicago da Atlanta da hana su tuntubar mutane a waje.

Yara ne kanana masu burin zama mawaka a rayuwa.

R Kelly durante un concierto

Asalin hoton, Getty Images

Wani rahoto shafin intaney na Buzzfeed a 2017 ya zargi cewa mata da ke fadawa cikin akubar Kelly na samun horo daga wata mata mai shekara 31 cikin mukarabansa, da ke koya musu yada ake kwanciya da namiji.

Kelly na kiran matan "babies" kuma yana umartarsu da kiransa uba wato "Daddy", a cewar Buzzfeed.

Sannan wadannan mata dole su nemi izini daga gareshi kafin su bar gidan da ya killace su, sannan Kelly ke iko, ko ke bada umarni iri suturar da za su sanya da kwace wayoyinsu. Idan suka bijire masa, ana azabtar da su a matsayin ladabtarwa.

Laifukan baya

Wannan ba shi ne karon farko da ake samun R Kelly a badakalar lalata da yara ba.

A baya, ya sha fuskantar zarge-zarge kan cin zarafin kananan yara mata.

Aaliyah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An raba aure bayan gano cewa Aaliyan ba ta kai shekaru 18 ba, kuma takardun da aka gabatar na shekarunta jabu ne - shekarar ta 15

A 1994, lokacin da R Kelly ya ke da shekaru 27, ya aure Aaliyah da suke waka tare.

An raba aure bayan gano cewa Aaliyan ba ta kai shekaru 18 ba, kuma takardun da aka gabatar na shekarunta jabu ne - shekarar ta 15.

R Kelly ya kuma wanke kansa a kotu daga zarge-zargen da mata da dama suka gabatar kansa na zargin laifuka.

Daya daga cikinsu Tiffany Kawkins, wacce ta yi ikirarin cewa ta wahala sosai saboda tsananin cin zarafi a shekaru 3 da ta kwashe na soyayya da mawakin, wanda ya soma lokacin yana shekara 24, ita kuma shekarar ta 15.

Akwai wata matashiya kuma, Tracy Sampson, da ta shigar da karar Kelly kan koya mata dabi'un lalata tana da shekara 17.

Tuhumar 'yan sanda

A shekara ta 2002, 'yan sanda a Chicago sun tuhumi Kelly da hada ko mallakar bidiyon da ke nuna ana lalata da yara.

R Kelly singing during a concert

Asalin hoton, Getty Images

Bidiyon da aka naɗa, wanda ya hada da hotunan lalata da sauran nau'ikan cin zarafi, sun kunshi tuhume-tuhume 10 da aka gabatar kan sa. 'Yan sanda sun zargi mamawakin da naɗan bidiyon.

Sai dai an wanke shi daga duk wadanan tuhume-tuhume bayan shekaru shida: alkalai sun ce babu shaidar da ke nuna cewa matar da aka haska a bidiyon yarinya ce.

A lokacin da yake jawabi bayan yanke hukuncin, mukadashin Antoni Janar na gabashin New York, Jacquelin Kasulis, ya ce "Ga mutanen da wannan abu ya shafa, an saurari kokenku kuma an yi muku adalci."