Zamantakewa: Yadda za ki hada aikin ofis da kula da miji da 'ya'ya ba tare da matsala ba
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 14, shirin ya yi duba ne kan rayuwar mace mai aure kuma ma'aikaciya, kan dabarun da za ta bi don sauke kowane nauyi ba tare da matsala ba.
A matsayina na matar aure kuma ma'aikaciya, na san mutane da dama na mamakin yadda nake iya hada kula da iyalina da kuma sauke nauyin aikina na ofis.
Ba ni kadai ce a wannan sahar ba, akwai miliyoyin mata irina da ke wannan fadi tashin, kuma suna ci gaba da tafiya da karfin jiki da na zuciya ba tare da sun fadi ba.
Watakila ke ma a yau kin samu aiki kuma kina tunanin ta yaya za ki hada wadannan al'amura biyu.
Wannan makala za ta yi miki bayanin yadda a kalla ko ba ki samu daidaito a lamurran biyu ba, to za ki saita hidimominki yadda za ki samu kwarin gwiwa.
A shekarun baya can ba a dauki aikin mace da muhimmanci ba musamman a yankin arewacin Najeriya, ba kamar yanzu ba da aka kara samun yawaitar ilimi tsakanin mata.
Sai dai duk da haka lamarin na zuwa da kalubale ganin cewa ita mace, dole akwai nauyin kula da iyali a kanta.
Hakan na nufin idan tana aiki, wani sabon nauyin ya karu a kan wanda dama can yake wuyanta na kula da gida da miji da 'ya'ya.

Wasu na baya da za ku so ku karanta

Batun samun daidaito a rayuwar aiki da sauran hidimomi ya bambanta daga mutum zuwa mutum.
Ba wai an nufin ki raba lokacinki biyu ba ne don daidaita al'amuran, a'a, so ake ki zama mai tsari ta yadda babu bangaren da zai cutu.
Kula da iyalanki da gidanki babban al'amari ne na saisaita rayuwarki, yayin da shi ma aikinki amana ce da kika karba za ki yi kuma ake biyanki.
Daidato mai tsari na nufin:
- Ki sauke nauyin duk aikin da aka ba ki a ofis ta hanyar yin sa a kan lokacin da ya dace, yayin da a lokaci guda kuma ki tsara yadda za ki kula da sauran al'amuarn tayuwa kamar kula da gida da kawaye da dangi
- Ki dinga samun isasshen barci mai inganci
- Ki manta da harkar ofis a lokacin da kike gida, ki mayar da kai kan hidimar gidan kawai, sai dai idan ana miki neman gaggawa
- Ki dinga ware lokaci na musamman don hira da maigida da 'ya'yanki ko da minti 30 ne ko awa daya, amma ki tabbatar kin ajiye komai a gefe a lokacin
- Ba tsawon lokacin hirar ne damuwar ba, inganci lokacin hirar ne abin so
- Ki daure da sada zumunci duk da kurda-kurdar aiki amma a wasu lokutan irin biki da suna idan ba dama gara ki aika gudunmowa
- Ki dinga rage wani abu a albashinki don zuwa dan yawon bude ido wasu kasashen
- Kar ki zama mai mammako ki yi duk abin da ranki ke bukata da kudin amma ya kasance ban da almubazzaranci
- Ki tsara kalandar yadda ayyukan gida da na ofis za su dinga kasancewa, sai kuma ki guji shiga lokacin daya.

Ta yaya zan gane tsarin rayuwar aiki da na kula da gidana ba sa tafiya daidai?
Zai iya kasancewa abu mai sauki yin sabo da dogwayen awannin aiki ko kasancewa cikin matukar gajiya, musamman idan mun dade muna hakan har ma ya zame mana jiki mu da sauran abokan aikinmu.
Zace-zacenmu da dabi'unmu ta fannin aiki na iya yin kamari har sai mun sake salo.
Kar ku manta cewa ku kan shafe sa'a a kalla bakwai zuwa takwas a duk rana a wajen aiki, hakan na nufin kun ma fi dadewa a can idan dai ana maganar ido biyu ne ban da lokacin barci.
Kenan ya kamata ki kyautata mu'amalarki da abokan aiki don ki samu irin nutsuwa da kwanciyar hankalin da kike bukata.
Yawan daga hankali da shiga damuwa na iya shafar lafiyar kwakwalwarki, abin da ka iya hargitsa ki har ki dinga sauke fushinki na ofis a kan iyalanki. Hakan kuma ba abu ne mai kyau ba.

Wane irin goyon baya ya kamata miji ya bai wa matarsa mai aiki?
Duk matar auren da kika ga tana aiki, to tabbaci hakika maslaha ce aka samu tsakaninta da mijinta.
Ya yarda ne ya amince ta yi, don haka kenan ya shirya kau da ido kan wasu kananan abubuwa da ka iya tasowa musamman na kula da gida 100 bisa 100.
Alhaji Aminu Gwani da matansa biyu duk suke aiki ya shaida min cewa, kamar yadda macen ke neman tallafin mijinta a yayin da take aiki, to shi ma yana bukatar wasu abubuwa daga gare ta.
"Ya zama wajibi ta kare mutuncinta da martabarta saboda ba don ba ma kishinsu ne muka bar su suna aiki ba.
"Sannan ya kamat mu kuma maza mu dinga goya mata baya, idan ta samu matsala a wajen aiki mu taya ta warwarewa.
"A gida kuma mu nemo msasu taimaka musu da ayyuukan gida. Sannan a lokutan da aiki ya yi mana sauki, ita kuma tana da aikin ofis mai yawa, to ma iya zama a gidan ma mu kula da yaran," in ji shi.
Ya nanata cewa dole ne duk a kare hakkokin juna a kowane lokaci.
Kazalika ya ce ko da matarka tana aiki a matsayinka na namiji dole ka ci gaba da sauke hakkokinka da Allah Ya dora maka.
"Ya kasance duk abin da za ta yi da albashinta to wasu bukatu ne na kashin kanta, ba wai ka sakar mata nauyin abinci da sutura da sauran hakkokin iyali ba," a cewar Alhaji Aminu Gwani.

Ƙarin wasu da za ku so













