Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afghanistan: Manyan kamfanonin Amurka waɗanda suka wadata kansu da yaƙin ƙasar
Yakin Afghanistan, wanda aka kawo karshensa a ranar 30 ga watan Agusta wannan shekara bayan da sojojin Amurka suka bar Kabul, ya ci wa Amurka dala biliyan 2.3, kamar yadda jami'ar Brown da ke tsibirin Rhode ta shaida.
Komawar mulki karkashin Taliban a Afghanistan da ficewar sojojin Amurka daga kasar yanayi ne da manazarta da dama ke ganin cewa yakin da Amurka ta yi a kasar bai yi nasara ba.
Ga mutane da dama kamar yaƙin bai yi nasara ba, amma ga wasu dama ce ta samun babbar riba.
Daga cikin dala tiriliyan 2.3 da aka kashe a yakin tsakanin 2001 zuwa 2021, kusan tiriliyan 1.05 an yi amfani da su ne domin tallafawa aiki da ayyukan rundunar tsaron Amurka a Afghanistan.
An yi amfani da mafi yawan kuɗin don biyan ayyukan kamfanoni masu zaman kansu waɗanda ke tallafa wa Amurka a Afghanistan.
Linda Bilmes, farfesa a Jami'ar Harvard ta ce "Yaƙin yana da ƙarancin sojojin Amurka - kusan duk masu aikin sa-kai ne - an ƙara su a matsayin 'yan kwangilar soja.
"Saboda kasancewar akwai ayyuka da yawa da za a yi, hakan na nufin wasu ma'aikata suna taimakawa wajen sanya mai a cikin jirgin, tukin manyan motoci, girki, aikin goge-goge, jirage masu saukar ungulu da jigilar abubuwa daban-daban. Wasu kuma an yi amfani da su wajen gina sansanin sojoji, kananan da manyan filayen saukar jiragen.", a cewarta.
Kamfanoni biyar sun biya makudan kudade
Daruruwan kamfanoni daga ciki da wajen Amurka sun samu kwangilar yin aiki tare da sojojin Amurka don ayyuka daban-daban ga sojoji a Afghanistan, na biliyoyin daloli.
Ko da yake babu jadawalin da ke nuna sunayen kamfanonin da aka fi biyan kudade, Farfesa Heidi Peltier, daga Jami'ar Boston - ya shaida wa BBC abin da ya kimanta. Waɗannan ƙididdigar sun haɗa da bayanan da ake samu daga shafin gwamnati a intanet.
Kamfanonin da ke da manyan kwangiloli a Afghanistan
- Dala biliyan 14.4 na Dyncorp International
- Kamfanin Fluor na da dala biliyan 13.5
- Dala biliyan 3.6 na Kellogg Brown Root (KBR)
- Dala biliyan 2.5 na Raytheon Technologies
- Dala biliyan 1.2 na Aegis LLC
"Waɗannan alkaluman na tsakanin shekarun 2008 zuwa 2021 ne, ko da yake wasu kwangilolin da aka haɗa na iya komawa zuwa 2008, don haka adadi na daidai zai iya zarce haka idan muna da duk bayanan daga 2001.
An kiyasata cewa, kamfanonin Amurka guda uku da suka kulla kwangiloli masu fa'ida a Afghanistan su ne: Dyncorp da Fluor da Kellogg Brown da kuma Root (KBR).
A cewar Peltier, Kamfanin Dyncorp - ya lashe kwangilar dala biliyan 14.4.
"Tun shekarar 2002, Dyncorp yana aiki kafada da kafada da gwamnati da abokan huldar ta a Afghanistan. Muna ba da ayyuka da dama," kamar yadda wani mai magana da yawun kamfanin ya shaida wa BBC.
Ya kara da cewa kamfanin mai zaman kansa ba zai iya ba da ƙarin cikakkun bayanai ba game da kwangilarsu da sojojin Amurka da kuma kuɗin da suka samu.
Fluor, wani kamfani ne da ke Texas, shi ne ke da alhakin gina sansanonin sojan Amurka a kudancin Afghanistan.
A cewar shafin intanet din kamfanin ya taimaka wa sojoji sama da 100,000 da hidima ta hanyar samar da abinci ga mutane fiye da 191,000 a rana.
Gaba ɗaya, kamfanin Fluor ya samu kwangilar dala biliyan 13.5.
Sashin BBC Mundo ya tambayi Fluor game da ayyukansa a lokacin yakin Afghanistan, amma har zuwa lokacin wallafa wannan labarin, BBC ba ta samu amsa ba.
Kellogg Brown Root (KBR), a nasa ɓangaren, ya shiga hidindimun da suka shafi injiniya da dabaru don tallafa wa sojojin Amurka dangane da masauki, abinci da sauran ayyukan yau da kullum.
A cewar ƙididdigar Peltier, KBR ya sanya hannu kan kwangilar dala biliyan 3.6.
Kamfanin na huɗu shi ne Raytheon, ɗaya daga cikin manyan kamfanoni jiragen sama da tsaro na Amurka, wanda ya lashe kwangilar dala biliyan 2.5.
Aegis LLC, kamfanin tsaro na Virginia, shi ne kamfani na biyar mafi girma da ake biyan albashi tare da ayyukan soji a Afghanistan, inda aka samu kwangilar dala biliyan 1.2.
Daya daga cikin manyan ayyukansa shi ne samar da ayyukan tsaro ga ofishin jakadancin Amurka da ke birinin Kabul.
BBC Mundo ta kuma tuntube su don jin karin bayani dangane da ayyukansu, amma har muka buga wannan rahoton, ba su amsa ba.
Me ake ciki game da kamfanonin Tsaro?
Kwararru sun shaida wa BBC cewa sun yarda cewa manyan kamfanonin tsaro na Amurka kamar Boeing, Raytheon, Lockheed Martin, General Dynamics da Northrop Grumman su ma sun amfana sosai daga yakin Afghanistan.
Linda Bilmes ta ce "Sun samu kudi mai yawa daga yakin."
Yana da wuya a faɗi adadin kuɗin da waɗannan kamfanoni suka samu saboda ba su da alaka kai tsaye da ayyukan a Afghanistan.
Peltier ya ce "Duk sun yi yarjejeniya don yin abubuwan da Amurka ke amfani da su a Afghanistan."
An kiyasta cewa tsakanin shekarar 2001 zuwa ta 2020, gaba daya waɗannan kamfanoni sun samu dala tiriliyan 2.1.
BBC Mundo ta kuma bukaci wadannan kamfanoni don jin ta bakinsu kan yadda yakin Afghanistan ya amfane su, amma ba su bayar da amsa ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.
Haka kuma, Boeing ya kera jiragen F-15 da F-18 wanda Linda Bilmes ta bayyana a matsayin kayan aikin sojan Amurka a Afghanistan.
Amma ba a sa Boeing a jerin manyan 'yan kwangila ba ko Lockheed Martin ba, wani babban kamfanin tsaro a Amurka, wanda ya kera helikwafta, wadanda ake amfani da su sosai a kasar.
Masana sun nuna cewa waɗannan kamfanonin tsaro suna da yawa kuma sun samu kuɗi da yawa ta hanyar yin abubuwan da suka danganci yakin.
Mai magana da yawun rundunar sojan Amurka Jessica Maxwell ta shaida wa BBC cewa yana da wuya a fadi adadin kudin da wadannan manyan kamfanonin tsaro biyar suka karba na kayan aiki da ayyukan da aka yi amfani da su a yakin Afghanistan.
"Yana da wahala a samu waɗannan ƙididdigar," in ji ta.
'An bayar da kwangila a boye'
Bilmes ya yi ishara da wani abu yayin yaƙin Afghanistan wanda masu neman izini ke da 'yancin sa farashin da suke ganin ya dace da ayyukansu.
"Yawancin kwangiloli an bayar da su a boye ne kuma ga kamfanoni 'yar kalilan.
Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da a lokacin su kadai ne ke iya yin wannan aikin, kuma ba manyan kamfanoni da yawa da za su iya yin aikin da ake so. Don haka sun ambaci farashin da suke so.
Bilmes ta kara da cewa "Manufar Ma'aikatar Tsaro ita ce ta samar da ayyukan yi ta hanyar masu fafatawa. Duk da cewa an sanya tsarin makamai da yawa a cikin takardun neman kwangilar, a zahiri galibi ana samun kamfani daya ne kawai ke samarwa," in ji Bilmes.
Haka nan an ambaci biliyoyin daloli, an ba su cin hanci yayin wannan yaƙin kuma akwai lokutan da aka ɗaga farashin kaya da gangan.
"Akwai lokutan da za ku iya yin fenti a gini amma sai a biya ku sau 20 na ainihin kudin. Akwai cin hanci da abin da zan kira kasafin kudi na bogi," in ji ta.
Jaridar New York Times ta taba ruwaito cewa tsakanin shekarar 2008 zuwa 2017, Ma'aikatar Tsaron Amurka ta bayar da rahoton almundahanar dala biliyan 15.5 da ake zargin an yi sama da fadin su a lokacin da ake kokarin aikin sake gina Afghanistan.