Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku san Malamanku tare da Sheikh Abubakar Umar Rijiyar Lemo
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Umar Rijiyar Lemo, wanda aka fi sani da limamin masallacin Kandahar ko masallacin Abdullahi Ibn Abbas na unguwar Rijiyar Lemo da ke birnin Kano, na daya daga cikin manyan fitattun malaman addinin Musulunci a arewacin Najeriya.
A cikin shirinmu na Ku San Malamanku, Shehin Malamin ya bayyana wa BBC cewa goyon bayan da ya samu daga wurin iyayensa ta fannin karatun addini da da'awa ya ba shi kwarin guiwar ci gaba da karantarwa.
Tarihin Rayuwarsa
An haife shi a shekara ta 1959, a unguwar Shar-al-Mansour da ke birnin Makkah.
Sheikh Abubakar Rijiyar Lemo ya fara karatu ne a hannun mahaifinsa wanda yake da makarantar Islamiyya da ake karantar da yara da matasa a birnin Makkah.
Daga baya an mayar da shi wata babbar makaranta ta wani malami mai suna Sheikh Adam Adam, wanda ke da abokai manyan malamai a birnin Makkah.
Ya ce manyan malaman kan zo makarantar lokaci zuwa lokaci don bai wa dalibai masu zurfin fahimtar karatu shawarwari da suka shafi karatu.
Sheikh ya ce a irin haka ne suka zabe shi suka yi masa jagoranci zuwa masallacin Ka'aba a lokacin babban shugaban limaman masallacin Sheikh Abdal Abdal-Ghani Al-Khayyat da mataimakinsa Sheikh Abdallah Abdul-Azeez Al-Khulaify tare da Sheikh Abdallah Muhammad Abdallah As-Suwair.
Su ne wadanda suka rika koyar da Sheikh da sauran dalibai darussa a makarantar ta Masallacin Ka'aba.
Ya ce baya ga nan sai aka bude wata makaranta da ake kira Kulliyatu Ibn Taimiyya inda ya rika daukar darussa.
Daga baya mahaifinsa ya yanke shawarar komawa gida Najeriya amma ya ba shi izinin ci gaba da zama a Makkah don ci gaba da karatu, a shekarar 1978.
Sai dai Sheikh ya biyo mahaifinsa suka komo gida tare.
Daga nan ne ya shiga kungiyar Jama'tu Izalatul Bidi'a wa Ikamatus Sunna da Sheikh Sama'ila Idris bin Zakariyya ya kafa.
Ya ce ya karbi tsarin kungiyar kuma sun fara wa'azi tare da wasu malaman a mataki na unguwa da jiha daga baya kuma suka kai mataki na kasa.
Haka kuma, Sheikh ya bayyana cewa ya je jami'ar A.B.U Zaria inda ya yi wasu kwasa-kwasai na difloma a wani reshensu da suka bude a jihar Kano.
Gwagwarmaya
Malamin ya bayyana cewa a lokacin da suka fara wa'azi a karkashin kungiyar Jama'tu Izalatu Bidi'a wa Ikimatus Sunna, mutane ba su fahimci ayyukan kungiyar ba don haka sun fuskanci kalubale sosai.
"Lokaci ne mai zafi sosai. Wasu unguwannin sai da 'yan sanda muke iya fita mu bar unguwar. Akwai wuraren ma da idan muka je ake ce mana makiya Annabi," a cewarsa.
Ya ce sai dai sun samu goyon bayan iyaye saboda sun fahimci irin karatun da suke yi, ya ce a kofar gida suke da masallaci don haka komai a kan idon iyayensa ya rika yi daga farko-farko.
Sheikh Abubakar Rijiyar Lemo ya ce ranar da ba zai manta da ita ba saboda farin ciki ita ce ranar da abokinsa Alhaji Abdullahi Sarki ya shaida masa cewa ya sayi filin da za a gina babban masallaci da zai iya zama masallacin Juma'a.
Ya ce wannan ya faranta masa rai saboda hakan ya nuna cewa ayyukansu na da'awa da karantarwa sun fadada kuma masallacin zai zama cibiyar yada da'awa.
Rasuwar Mahaifansa
Sheikh ya ce ba zai manta da rasuwar iyayensa ba.
Ya ce rasuwar mahaifinsa na daya daga cikin abubuwan da suke sa shi cikin damuwa da har yanzu idan ya tuna ya kan ji kamar a lokacin abun ya faru.
Ya ce mahaifinsa ya rasu ne bayan sallar asuba kuma ya yi ta sa masa albarka kafin rasuwar tasa.
Iyali
Sheikh ya bayyana cewa yana da matan aure uku da 'ya'ya 28, sannan jikokinsa sun haura 20.
Ya ce babban burinsa shi ne makarantarsu ta sakandire ta Zaid bin Thabit Foundation ta fadada, kuma Allah Ya amsa addu'arsa ta fadada ginin makarantar a wani fili makeke da wani attajiri a jihar Kano ya ba su kyautarsa.
Ya ce yana fata Allah Ya nuna masa kammala ginin ajujuwan makarantar har a fara karatu a ciki.