Ku San Malamanku tare da Sheikh Ahmad Kanoma

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da Sheikh Ahmad Kanoma:

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan a Najeriya Sheikh Ahmad Ibn Umar Kanomo, ya ce ya taɓa jingine harkarsa ta kasuwancinsa, bayan da ya lura zai masa cikas a kudurinsa na yin da'awa da kuma karantar da jama'a.

Malamin ya ce har ya kama rumfa yana ciniki yana samun kudi sosai, amma ya cefanar da rumfarsa ya je ya bude makaranta, wato burin da ya jima da shi a ransa.

A cewar malamin, "sai naga cewa anya kuwa yanzu abun nan na iya haduwa biyu?, to sai na canja shawara na bude makaranta a lafiyar barebari, wadda na bude tun shekaru 39 da suka gabata."

Ya ƙara da cewa a halin da ake ciki makarantar ta bunkasa har ta kai ga shiga jihohi daban-daban na arewacin Najeriya, kuma ana ci gaba da ilimantar da jama'a a cikinsu.

Tarihin rayuwarsa

Malamin ya shaida wa BBC cewa an haife shi ne a shekarar 1962, kuma asalin mahaifinsa mutumin Gurbadu ne, da ke karamar hukumar Mafara, a jihar Zamfara, sannan mahaifiyarsa yar asalin Kanoma ce, diyar babban limamin garin Kanoma.

Ya ce a garin Kanoma ya tashi tun da aka haife shi har lokacin da ya fara dalibta, sannan ya fara karatun kur;'ani ne a makarantar kakansu liman Abubakar Kanoma, a nan ya sauke kur'ani, kuma daga nan aka kai su makaranta garin Gusau, a jihar Zamfara tun yana shekara 9.

Sai dai ya ce duk yawancin malamansa na garin Gusau ne, tun daga malaminsa na farko har zuwa wani babban malaminsa Liman Isah Shuraihu, wanda babban malamin Nahawu ne da tafsriri, sannan yana da manyan malaman balaga da mandiki irinsu Sheikh Muhammadu Nakarimu Jibiya.

''Ya ce ya kuma bibiyi karatun Shekh Mahmud Gumi sosai, da irinsu Sheikh Abubakar Tureta wanda shi ya ma yi karatu a wajen shi.

Gwagwarmaya

Ya shaida wa BBC cewa ya taba zama mamba a kwaitin dabbaka shari'ar musulunci a jihar Zamfara, sannan ya taba zama mamba a wani kwamitin dabbaka shari;'a a Tudun Wada Gusau, kana an sanya shi a mambobin hukumar Zakka ta jihar Zamfara, inda ya kwashe kusan shekara 19, abun da ya bashi dama zuwa kasashe da dama ciki har da Sudan.

Kazalika an sanya shi a majalisar shura ta malaman jihar Zamfara, da kuma wani kwamitin tsara lokutan sallah a jihar Zamfara, kana shine ya shugabanci kwamitin yaki da jefa kur'anai shadda, wata matsala da aka yi fama da ita a jihar Zamfara.

Na fi son tuwo

Shehun malamin ya shaida wa BBC cewa ya fi son tuwo cikin dukkan abinci, musamman tuwo, kuma ya ce ko ana azumi babu abuanda ke hana shi cin tuwo, kuma yakan ci shi ne da miyar kuka ko kuma kowacce iri ma.

''Akwai lokacinda tafiya ta kama ni zuwa Misra, kwananmu bakwai ban ci tuwo ba, gaskiya sai dai yunwa ta kamani, amma daga baya aka ce in sun ce Askandariyya za a sa a dafa musu tuwo.''

Ya kara da cewa matsawar zai yi tafiya zuwa wata kasa da ba tuwo, shi kansa ya san cewa lallai zai sha wahala.

Ina son motsa jiki.

Sheikh Ahmad Ibn Umar Kanomo, ya bayyana cewa yana matukar son motsa jiki, har ta kai yakan kalli wasannin motsa jiki a kafafen talabijin domin matukar sha'awar da hakan ke bashi.

''Ina sha'awar inga ana motsa jiki, saboda har kayan motsa jiki nakan siyo nima ina yi, sannan ina zuwa wurin yi nima in yi, kuma ina kallon yadda sojoji ke motsa jiki''

Iyali

Malamin na da mata hudu, amma da ya ce mata biyu zai sai daga baya al'amari ya sauya, kuma yana da 'ya'ya 28, 14 maza yayin da 14 suke mata.

Ya ce babban fatansa shi ne cikawa da imani, domin a cewar ba farkon ba karshen, wato karshen ake tsoro