Soyayya da kuɗi: Zafin rabuwa da masoya

    • Marubuci, Daga Esyllt Carr
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan kasuwanci
  • An wallafa

Bill da Melinda Gates suna daga cikin ma'aurata attajirai da suka rabu a bana - amma ba su kaɗai ba ne tunanin raba dukiya ya kasance wani babban ƙalubale bayan annobar korona.

Duk da ba za su fuskanci matsala wajen biyan kuɗin da aka ƙayyade ba, amma ga yawanci raba dukiya bayan rabuwa babban ƙalubale ne.

A 2019, sama da ma'aurata 100,000 ne suka rabu a Birtaniya - kuma tun lokacin, annobar korona ta jefa tarayyar ma'aurata cikin matsala.

Kashi ɗaya bisa huɗu na mutanen sun ce zamantakewar aurensu ta shiga wani hali zamanin korona, kamar yadda sakamakon binciken da Jami'ar London ta yi kan mutum 70,000 ya nuna.

Wata cibiyar da ke ba ma'aurata shawara a Birtaniya ta ce an ziyarci ɓangaren shafinta na intanet kan sakin aure sau 419,359 tsakanin watan Yulin 2020 zuwa Yulin 2021 - kashi 14 fiye da shekarar da ta gabata.

Ana sassauta matakan kullen korona, adadin ya ƙara ƙaruwa na masu ziyartar shafin ɓangaren sakin aure - musamman kan yadda za a biya kuɗin sakin.

Matsalolin kuɗi

Yayin da kuɗin sakin ya bambanta, farawa ma ya haramta ga wasu. Kuɗin neman buƙatar shi ne fan 550 - wanda duk wanda ke neman yin saki dole sai ya biya.

"Mun tattauna da mutane waɗanda dole ta sa sai sun ɗauki watanni ko shekaru kafin su samu fan 550," in ji Farfesa Liz Trinder, wacce ta jagoranci binciken a gidauniyar Nuffield kan kuɗin sakin aure.

Akwai haraji kan kuɗaɗen farko ga ma'auratan waɗanda "ke cikin hali na rashi", in ji Farfesa Trinder wadda ta ce ainihin kuɗin bai kai fan 550 kuma zai sauka yayin da aka sauya tsarin zuwa na intanet.

Ko da yake akwai taimako da aka yi tanadi ga masu ƙaramin ƙarfi, amma damuwar ga wasunsu da dama shi ne ƙaruwar kuɗaden zai hana su neman shawarar da ta dace.

"Mutane da yawa na shakkun zuwa ofishin lauya mai bayar da shawara, domin suna damuwa da tsadar kuɗin," in ji Mena Ruparel.

"Lauyoyin suna caji a ƙari na mintuna shida - don haka aika saƙon imel da samun amsa na iya ƙara hauhawar farashin cikin sauri."

Amma rashin yin magana da lauya kan iya ƙara tsadar kuɗin, in ji Misis Ruparel, idan har mutane ba su nemi shawara ba kan yadda za su kauce wa kotu ta hanyar sasanci ko kuma samun sauƙin rabuwa cikin sauƙi.

Matan da ke fuskantar rabuwa ana barinsu cikin wani matsayi mai rauni, domin kuɗin da za su samu kaɗan ne na ajiya da kuma fansho.

Rita, wadda ba ta son a bayyana sunanta, tana ƴar shekara 50 ta rabu da mijinta mai shekara 30, bayan ta haƙura da aiki don ta kula da ƴaƴansu.

Tana ganin lauya a matsayin wata hanyar "cin kuɗin banza" maimakon haka ta mayar da hankali kan kula da gida ba tare da tana da dama ga kuɗaɗen tsohon mijinta na fansho ba.

Amma Martin Bell daga masu kula da ƙuɗaɗen fansho, wanda ya shawarci Rita da kada ta kasance ba tare da lauya ba, ya ce yin watsi da tanadi na fansho kan sa mata cikin talauci.

Mata da yawa suna yanke shawarar dakatar da yin aiki domin ba da fifiko ga iyalinsu ba tare mayar da hankali kan fansho ba a tsarinsu, kuma wannan wani abin da ya kamata a dinga la'akari da shi ne, in ji shi.

Sakin aure

Duk da haka, ƙarin mutane suna yanke shawarar yin komi da kansu.

Bincike kan mutum 1,000 da aurensu ya mutu da wata ƙungiya ta yi mai da'awar ganin iyali sun samu shawarar lauya, ya gano kashi 57 na waɗanda suka yi saki a cikin shekaru biyar da suka gabata ba su nemi taimakon doka ko kaɗan ba.

Duk da cewa rashin neman shawara ba zai buƙaci kashe kuɗi masu yawa ba, amma lauyoyi sun ya fi dacewa ga ma'auratan da suka rabu kuma ba su da ƙadarorin da za su raba - saboda batutuwa kamar fansho da ƴaƴa da ƙadara na da sarƙaƙiya.

Rage yawan kuɗaɗen tallafi na shari'a da aka samar a 2013 ya nuna yawancin iyali da suka ƙunshi har da waɗanda aurensu ya mutu, yanzu ba su cancanci samun tallafin ba.

Ƙungiyar Resolution, da ke wakiltar lauyoyin iyali 6,500, na son a sake dawo da tallafin ga duk wanda ke neman shawara ta farko game da mutuwar aure.

"Mun san cewa samun shawara yana taimakawa ma'aurata yanke shawarar da ta fi dacewa da yadda za su rabu," a cewar Juliet Harvey, shugabar lauyoyin ta Resolution.

Ma'aikatar shari'a ta ce tana kashe miliyoyin kuɗi don taimaka wa ma'aurata don kaucewa biyan kuɗaɗe masu tsada, da kuma tallafin sasanci ga waɗanda ba su da ƙarfi.

Ya ƙara da cewa cajin ga waɗanda za su iya biya na nufin "tsarin shari'ar yana tafiya daidai, yayin da ake rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa na masu biyan haraji."

Louise, wadda ba ta son a bayyana sunanta, ta ce ba ta da wani zaɓi illa ta gabatar da kanta lokacin da tsohon mijinta ya kwashe kuɗin bankinsa ya kuma sayar da abubuwan da suka mallaka bayan ta rabu da shi.

"Na tattauna da lauya nan take ta gano yawan kuɗaɗen," in ji ta. Ga yara da take kula da su ga shi kuma ba kuɗi ta shiga damuwa har ta sayar da babbar kadararta - gidan da suke ciki - kan kuɗin shari'a domin gabatar da ƙarar a kotu.

Ta ce, "Na fahimci halin da ake ciki sosai," amma ta yarda cewa shekaru takwas da aka ɗauka don kawo ƙarshen rikicin na rabuwa sun kasance masu wahala.

"Har yanzu ba ta karɓi kuɗaɗen da aka umarci tsohon mijinta ya biya ba."

Marubuciya Elizabeth MacBride, wadda ta yi rubutu kan rabuwar aurenta, ta ce duk da mutuwar auren ta yi tsada kuma ta yi sanadin rabuwa da aikinta, da ba ta samun ƙwarin gwiwa ba kan neman shawarar rabuwar aure.

Samun kasancewar ƴaƴanta mata a hannunta shi ne babban burinta, kuma ta yanke shawarar cewa tana buƙatar lauya.

"Tunkarar lamarin ni kaɗai zai yi wahala. Fargabarta shi ne abokin zamanta zai yi jayayya da ita ne kan ƴaƴanta."

Tsari na ci gaba

A cikin waɗannan lokuta mafi ƙalubale, inda ba za a iya cimma yarjejeniya mai fa'ida ba, komi na iya ƙara tsada.

Lucy Davis, wadda ke jagorantar wata ƙungiya kan sakin aure a Birtaniya ta ce, mutane da dama da ta haɗu da su suna fuskantar ƙalubale wajen rabuwa, inda kuɗaɗen za su kai dubbai.

Ta ce matsin lamba ta kuɗi kan sa mutane karɓar rance daga banki ko kuma daga dangi. Ta ce abu ɗaya da yake a bayyana shi ne damuwa kan zama matsala ga yanke hukunci game da batun kuɗi.

"Yana da wahala mutane su iya bambance kuɗi da kuma son rai. Sau da yawa muna tattaunawa kan fa'idar ɗaukar saki kamar ma'amala ta kasuwanci.

Gaba ɗaya abin da ya fi dacewa zai iya zama mai wahala idan wani yana ganin tsohon abokin zamansa dole ya biya kuɗi saboda jin zafin ransa.

Rabuwar aure abu ne mai matukar wahala, amma yadda mutane suke tunkarar saki yana sauyawa.

Yawancin tsarin yanzu yana intanet, za a iya kammala tsarin cikin sauri. Mutane ba za su sake ɗora laifin cin amanar aure ko kuma wasu daɓi'u da ba su dade ba ko ƙauracewa ba a matsayin dalilin saki.

Duk da wannan zai iya zama dalili ga sakin aure amma ba lallai ba ne ya zama cikin sauƙi da rahusa. Kuma ga ma'aurata da yawa, wannan har yanzu ya kasance babban ƙalubale.