Ana ce-ce-ku-ce kan Fatawar Mufti Shawki Allam cewa Sahabbai sun ƙayyade iyali don rage yawan jama'a

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Sanarwar da hukumomin Masar suka fitar game da karuwar yawan jama'a da kuma fatawar babban shehin malamin ƙasar Mufti Shawki Allam sun janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar musamman a kafofin sada zumunta musamman kan kalaman malamin wanda ya ce sahabbai sun yi amfani da hanyoyin hana ɗaukar ciki.

Allam ya ce "ƙididdiga na da mahimmanci kuma ya zama dole don fahimtar haƙiƙanin gaskiya da kuma fahimtar haɗarin yawan jama'a."

Ya kuma jaddada cewa "ba mu fuskantar matsalar addini wanda zai iya kawo cikas ga fuskantar ƙaruwar jama'a, amma bayani da fahimtar zahirin gaskiya da zai ba mu damar ci gaba a hanyoyi daban daban. "

Shehin malamin na Masar ya kafa hujja da Hadisin Imam Abu Hamid Al-Ghazali kan batun, yana mai nuni da cewa "Sahabbai sun yi amfani da hanyoyin da suke da su don hana ɗaukar ciki lokacin kwanciya da iyali, ta hanyar azalo, kuma hakan ya faru a zamanin Annabi Muhammad SAW da kuma yardarsa."

Kalaman Mufti Allam na zuwa ne a yayin da gwamnati ke wayar da kan mutane game da manufar taƙaita haihuwa a Masar da kuma ƙaruwar yawan jama'a a ƙasar.

A cikin wata sanarwar daga tashar "Echo of the Country", shugaban Masar Abdel Fattah El-Sisi ya ce: "Ƴan ƙasar ba za su ci moriyar rayuwarsu ba, matsawar ana samun yawan karuwar jama'a ta wannan hanyar."

Ministan tsare-tsare da raya tattalin arzikin Masar, Hala Al-Saeed, ta yi kiran "rage yawan haihuwa a kasar," tana mai cewa "a kowa ce dakika ɗaya ana haihuwar jarirai 14 a Masar."

Ce-ce-ku-ce

Kalaman shehin malamin na Masar da kuma bayanan hukumomin Masar sun tayar da ƙura a shafukan sada zumunta.

Wasu sun zargi malamin da "bayar da fatawa don faranta ran manufofin siyasar ƙasar."

Wasu kuma sun kafa hujja da maganganun malamai da hadisan da ke ƙarfafa haihuwa.

Rifai al-Bitar ya nuna cewa "Idan gwamnati za ta ɗauki mataki, ya kamata ta zama abin koyi ga jama'a," kuma ya yi tambayar cewar: "Yara nawa ne shugaban kasa da Firaminista da ministoci da gwamnoni ke da su?"

Nabil ya soki yadda ake amfani da gazawa inda ya ce an ci gajiyar yawan jama'a a fannoni da dama na ci gaban ƙasar kamar gina madatsun ruwa da mashigin Suez da kuma dalar Masar.

Wasu sun ƙi mayar da hankali kan da'awar batun yawan jama'a tare da yin watsi da batutuwan "cin hanci da rashawa da amfani da albarkatun ƙasa."

A gefe guda kuma, da yawa sun nuna goyon bayansu ga abin da jami'an Masar suka faɗa. Iman ta ce ƙaruwar yawan jama'a a halin yanzu bala'i ne.

Dan jarida Ahmed Moussa ya bayyana ƙaruwar yawan jama'a a matsayin "bom wanda zai iya tashi da kowa."

Ahmed Fathi ya ce duk abin da gwamnati ta faɗa "yana da inganci kuma yana bisa hanya, amma bai isa ba, kuma dole ne a samu tsari da hanyoyin ci gaban ƙasa tare da ƙarfafa gwiwar mazaje.