Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afghanistan: Nawa Amurka da ƙawayenta suka kashe a yaƙin ƙasar
- Marubuci, Daga ɓangaren bincike
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Daga ficewar dakarun ƙasashen yammaci a Afghanistan zuwa ga ƙwace ƙasar da Taliban ta yi, mun yi nazari kan yawan abin da Amurka da ƙawayenta suka kashe a yaƙin ƙasar na shekaru 20.
Dakaru nawa aka tura?
A 2001 Amurka ta yi mamaya a Afghanistan domin kawar da Taliban, wadda ta ce ta taimakawa Osama Bin Laden da sauran shugabannin al-Qaeda da take zargi suna da alaƙa da harin 9/11.
Dakarun Amurka sun ƙara yawa inda gwamnatin ƙasar ta saki biliyoyin daloli domin yaƙar Taliban da kuma sake gina Afghanistan.
A bara, dakarun Amurka 4,000 ne kawai.
Amma alƙalumman hukuma ba su haɗa har da dakaru na musamman ba da sauran ɓangarori.
Akwai kuma dakarun wasu ƙasashea ƙasar, da suka haɗa da na wasu mambobin Nato.
Amma Amurka ce kan gaba a Afghanistan.
A watan Disamban 2014 ƙungiyar Nato ta sanar da kawo ƙarshen yaƙinta a Afghanistan amma ta bar dakaru 13,000 domin bayar da horon yaƙi da ta'addanci ga sojojin Afghanistan
Akwai kuma wasu ƙarin wasu jami'an tsaro masu zaman kansu da ke aiki a Afghanistan. Wannan ya ƙunshi ƴan asalin Amurka 7,800 a zangon ƙarshe na shekarar 2020, kamar yadda binciken majalisar dattijan Amurka ya nuna.
Nawa aka kashe?
Amurka ce ta fi kashe kuɗi a yakin Afghanistan
Tsakanin 2010 zuwa 2012, lokacin da Amurka ke da yawan sojoji 100,000 a ƙasar, kuɗin da Amurka ta kashe ya ƙaru kusan dala biliyan 100 a shekara, kamar yadda alƙalumman gwamnatin Amurka suna nuna.
Amurka ta rage kashe kuɗi bayan mayar da hankali kan bayar da horo ga dakarun Afghanistan inda Amurka ta rage yawan dakarunta.
A 2018 yawan kuɗin ya kai dala biliyan 45, kamar yadda wani babban jami'in tsaron Amurka ya shaida wa majalisar dattijan Amurka a shekarar.
A cewar ma'aikatar tsaron Amurka, yawan kuɗin da ƙasar ke kashewa kan hidimar Afghanistan (daga Oktoban 2001 zuwa Satumban 2019) ya kai dala biliyan 778.
Haka kuma, ma'aikatar harakokin wajen Amurka haɗi da hukumar raya ƙasashe ta USAID da sauran hukumomin Amurka - sun kashe dala biliyan 44 wajen gudanar da ayyukan sake gina ƙasar.
Idan aka haɗa jimillar kuɗin - bisa alƙalumman hukuma - ya kai dala biliyan 822 tsakanin 2001 zuwa 2019, amma bai ƙunshi kuɗaɗen da aka kashe ba a Pakistan.
Wani binciken Jami'ar Brown a 2019, wanda ya yi nazari kan kuɗaɗen da aka kashe a Afghanistan da Pakistan, ya nuna cewa Amurka ta kashe kusan dala biliyan 978.
Binciken ya nuna cewa yana da wahala a gano jimillar kuɗin saboda yadda tsarin tattara alƙalumma ya bambanta tsakanin ma'ikatun Amurka, kuma yana canzawa lokaci zuwa lokaci.
Birtaniya da Jamus - waɗanda ke da yawan dakaru a Afghanistan bayan Amurka - sun kashe aƙalla dala biliyan 49 a yaƙin Afghanistan.
Duk da sun janye dakarunsu, Amurka da Nato sun yi alƙawalin dala biliyan huɗu zuwa 2024 domin tallafawa dakarun Afghanistan.
A wannan shekarar, Nato ta kashe dala biliyan 72 na shigar da kayayyaki da makamai a Afghanistan.
Ina kuɗin suka shiga?
Yawan kuɗaɗen da aka kashe a Afghanistan an ware su ne domin yaƙin ƙasar da kuma samar da buƙatu kamar abinci da magani da alawus ga dakaru.
Alƙalumma sun nuna cewa tun 2002, Amurka ta kuma kashe kusan dala 143.27 na gudanar da ayyuka a Afghanistan.
An kashe sama da dala biliyan 88 wajen gina dakaru a Afghanistan, da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda.
An kuma ware kusan dala biliyan 36 na tafiyar da gwamnati da ci gaba, yayin da kuma aka ware wani kaso na ayyukan jin-ƙai
Wasu daga cikin kuɗin nan sun ɓata ta hanyar zamba da sama da faɗi a tsawon shekaru.
A cikin wani rahoto ga Majalisar Amurka a watan Oktoban 2020, kungiyar da ke da alhakin sa ido kan ayyukan sake gina Afghanistan ta kiyasta kusan dala biliyan 19 aka rasa ta wannan hanyar tsakanin Mayun 2009 da 31 ga Disamban 2019.
Asarar rayuka fa?
Tun lokacin da aka fara yaƙin Taliban a shekara ta 2001, an samu mutuwar sama da mutum 3,500, wanda sama da 2,300 sojojin Amurka ne.
Sama da sojojin Birtaniya 450 suka mutu
Wasu ƙarin sojojin Amurka 20,660 suka jikkata a fagen daga.
Amma waɗannan alkaluman ba su kai yawan asarar rayukan jami'an tsaron Afghanistan da fararen hula ba.
Shugaba Ghani a 2019 ya ce dama da dakarun Afghanistan 45,000 aka kashe tun zamansa shugaban ƙasa shekaru biyar.
Binciken Jami'an Brown a 2019 ya ƙiyasta cewa hasarar rayukan da aka yi na sojoji da ƴan sanda a Afghanistan ya kai sama da 64,100 tun Oktoban 2001 lokacin da yaƙin ya ɓarke
Alƙalumman hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya a Afghanistan ta ce sama da fararen hula 111,000 aka kashe ko suka ji rauni tun da ta fara ƙidayar waɗanda rikicin ya shafa a 2009.