Jiya da yau: Bala'in gobarar dajin da ke addabar duniya

wutar daji

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Mark Kinver
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environment reporter
  • An wallafa

A makalarmu ta wata-wata mai taken A jiya da yau, mun yi bayanin yadda duniya ke sauyawa daga yanayi mai ɗumi.

A shekarun da suka gabata, ɓarnar da wutar daji ke haddasawa ta karaɗe manyan labaran kasashen duniya.

Duk da cewa gobarar wani bangare ne na tarihin dan adam, masana kimiyya na daga muryar nuna damuwa kan gobarar da ke tashi a dan tsakanin nan, mai matukar muni da ɗaga hankali.

A shekarun da suka gabata, ɓarnar da wutar daji ke haddasawa ta karade manyan labaran kasashen duniya, yayin da miliyoyin eka ke ƙonewa ƙurmus, dubun-dubatar mutane kuma na rasa muhallansu.

Gobara a yammacin Amurka da Australia na daga cikin mafi muni da aka gani a dan tsakanin nan.

A farkon sa'o'in shekarar 2020, wata mummunar gobarar daji ta tashi a kauyen Cobargo da ke yankin New South Wales.

'Yan sa'o'i kadan, gobarar ta mamaye babar hanyar kauyen, ba abin da ake gani sai hayaƙi da kuma burbushin ɓarnar da ta yi.

Bayanan bidiyo, Wani bidiyo da ke nuna yadda gobara ke ci

Kauyen da gobarar ta lalata ya zamo wata alama ta irin ɓarna da halin da Austarlia ta samu kan ta da kuma aka yi wa lakabi da ''Bakar bazara,''wadda akalla mutum 34 suka mutu, tare da dabbobi biliyan uku da eka miliyan 46.

Duk da cewa gobarar daji ta dade da zama wani bangare na rayuwa, amma tashinta akai-akai, da yaduwarta na kara tada hankali.

Wata dabba na neman abinci a Kangaroo Valley watan Junairun 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dabbobin daji na fadi tashin neman abinci, da inda za su fake bayan an kashe gobarar

A kowacce bazara, duniya na ganin sauyi, da yadda tartsatsin wuta ke tafiya tare da sauri tare da mamaye titin Pamplona na Sifaniya.

A wannan yanayi zai yi matukar wuya a kashe wutar dajin, ko shawo kan yaduwarta, da kare gidaje da dukiya cikin ƙanƙanin lokaci.

Sake rubuta tarihi

Sai dai, daman can gobarar daji wani fanni ne na tarihi, da ta ke rutsawa da dabbobi da tsirrai da bil'adama. Idan babu irin wannan gobarar ba za mu wurare haka ba.

Akwai bishiyoyin da suke bukatar wuta, domin su girma su kuma mamaye dazuka.

Misali bishiyar da ake samun danƙo daga jikinta, tana da 'ya'ya da suke bukatar wutar da za ta narkar da su domin fitar da ƙwallayen da ke ciki.

Akwai wasu karin bishiyoyin da suke buƙatar wuta, misali itacen sapwood, wanda ta jikinsa ruwa ke tsassafowa, shi ma yake bukatar wuta.

Idan da babu wutar, yawancin bishiyoyin da suka dogara da ita ba za su tasa ba. Sannan akwai wasu halittun da su ma suka dogara da ita da za su ta fadi tashin girma.

Jin tsananin zafi

Haka kuma, akwai matukar damuwa kan wutar da ke taimakawa halittu da tsirran ka iya janyo musu matsala idan aka dinga fuskantarta akai-akai.

Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon wata gobarar daji a birnin California

A shekarar 2017, rahoton da cibiyar da ke nazari kan sauyin yanayi da ke Amurka ta fitar, ta nuna damuwa kan karuwar gobarar daji a shekarun da suka gabata.

Ta ambato ɗumamar yanayi, da karuwar fari na daga cikin abubuwan da suka kara habbaka tashin gobarar daji.

Wani abun da ya ƙara tashin gobara shi ne ɓullar sababbin cututtuka da ke kashe tsirrai da bishiyoyi.

Misali ɓullar ƙwaron ash borer mai tashi sama, ya kashe miliyoyin bishiyoyi a Amurka.

Wannan ya janyo mutuwar katako mai yawa, daga bisani wannan katakon shi ya zama kamar kiraren da ke ƙara iza gobarar da shi a duk lokacin da ta kama.

A rahoton bincike na hudu da hukumar kasa da kasa kan sauyin yanayi ta fitar, ta ce: "Damuwar da ake samu idan an samu gobarar daji na da yawa, misali bazuwar ƙwari, da ta yiwu su ƙaru a lokacin da ake fama da zafi, da bushewar ƙasa da janyo koma baya a kakar shuka."

Rahoton ya ƙara da cewa: "A lokutan bazara, yanayi na sauyawa da tsakanin zafi ko tsaka-tsaki, ana ƙiyasin za su ƙaru matuka da kara hadari a duk shekara da kashi 10 zuwa 30 cikin 100.

Yayin da wasu wutar dajin tsawa ce ke haddasa su, an yi amanna da cewa kaso mafi tsoka bil'adama ne ke haddasawa ko dai bisa kuskure ko sakaci.

Masana kimiyya sun ce abu ne mai muhimmanci a dauki matakai tun daga matakan garuruwan, ta yadda za a hana faruwar lamarin ko rage hadarin hakan.

Sannan da gabatar da shirye-shirye da za su wayar da kai mutane muhimmanci da hadarin tashin gobara.

Shirin duniyar mu A jiya da yau zai ci gaba da zuwa mu ku a kowanne wata, da hadin gwiwar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a Glasgow, wanda za a fara a watan Nuwamban 2021.