Gobarar daji ta raba dubbai da gidajensu a Amurka

Gobarar dajin ta kone gidajen mutane da dama a Oregon

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Gobarar dajin ta kone gidajen mutane da dama a Oregon
An wallafa

Dubban mutane a yammacin kasar Amurka na shafe karshen makon nan a sansanonin wucin-gadi yayin da wutar daji ke ci gaba da barna a fadin yankin.

A California, wutar mafi girma, wadda ke ci a arewa da Sacramento, ta kone dajin da ke da itatuwa, mai fadin murabba'in sama mil 200, inda yanayin kwarin wurin ke haifar da tarnaki ga kokarin kashe wutar

Can kuwa a Oregon barkewar cutar korona ta tilasta killace akalla ma'aikatan kashe gobara tara.

A cikin makwannin nan sama da ganga-gangar wutar daji 80 a jihohin Amurka 13, ta kona dajin da ya kai eka miliyan daya da dubu 300.

Gagarumar wutar dajin da ke ci ganga-ganga a Arewacin California, tana bazuwa ne cikin hanzari, ba kakkautawa.

Sayyid Bey na jimamin yadda wutar da kone masa gida krmus a garin Bly na Oregon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sayyid Bey na jimamin yadda wutar da kone masa gida krmus a garin Bly na Oregon

'Yan kwana-kwana sun tashi tsaye aiki ba ji ba gani dare da rana domin kasheta, amma kamar ba ta san ana yi ba, domin har ya kai ta sauya yanayin inda take mamaya.

Duk da cewa masu kashe wutar sun samu nasarar shawo kan kashi daya bisa biyar na fadin inda ta mamaye, to amma jami'ai sun ce yanayin wuta na tsanani hadi da rashin raba sosai, na haifar da matsala ga kokarin kashe ta.

An kwashe mutane daga gidajensu a yankuna da dama na kusa.

Wutar ta haifar hadari da ya game sama, wanda ke sa walkiya a fadin yankin. Hayakin wutar ma har yana kaiwa makwabciyar jihar ta California, Oregon, inda a can 'yan kawan-kwana suka yi nasarar kashe wutar daji mafi girma a Amurkar, a kudu da Portland.

A wutar ta yanzu ana ganin yanda hayaki ya kai har ya rufe hasken rana, kuma hakan ya sa yanayi mai sanyi, da ya saukaka wa 'yan kwana-kwana aiki suke samun nasarar shawo kanta.

'Yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar daji daga kan jirgin kasa

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, 'Yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar daji daga kan jirgin kasa

To amma kuma hakan da ake kallo kamar wata inuwa ko rumfar hadari, ba abu ne da ake gani za a iya hasashe a kansa ba, wanda ya sa ake fargaba cewa yanayi mai zafi da iska ka iya bayyana nan gaba, da ka iya kara rura wutar dajin ta ci gaba da mamaya da barna.

Kokarin ganin bayan wannan wutar daji dai ya gamu da karin cikas, da barkewar cutar korona a tsakanin ma'aikatan kawana-kwana.

Wadanda aka yi wa gwaji aka ga sun kamu da ita, suna killace kai.

Yadda har yanzu ake da tsawon lokaci na bazara mai zafi, ana ganin wutar dajin za ta zama kalubale ga yawancin yankin yammacin Amurka a makonni da daya masu zuwa.