Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ke faruwa a Tunisia? Dalilai hudu kan tashin hankalin da ake ciki
Shekaru 10 bayan nan, kasar da ta kasance cibiyar guguwar sauyin, da ake yi wa kallon mai nasara ta sake fadawa cikin wani mummunan yanayin.
A ranar 24 ga watan Yuli, shugaba Kais Saied ya dauke wani mataki mai cike da cece-kuce na sauke Firai Minista
Hichem Mechichi daga muƙaminsa, tare da rusa majalisar ministocinsa, matakin da 'yan adawar siyasa musamman jam'iyyar Islamist ke kallo da juyin mulki mai cike da hadari.
Shugaba Saied ya ce matakin wani bangare ne na kawo daidaito da magance matsalolin da suka taso da suka janyo zazzafar zanga-zanga.
"Wannan mataki ne da ya janyo mummunan tashin hankali, da rikicin siyasa da ya dabaibaye Tunusia tun shekarar 2011 lokacin juyin-juya hali," in ji Ricardo Fabbiani, ƙwararre a cibiyar bincike kan rike-rikice ta duniya da ke arewacin Amurka.
"Babu wanda ya san makomar kasar ko abin da zai faru, kuma matakin da shugaban kasar ya dauka ya sake jefa Tunusia cikin halin rashin tabbas."
Halin da Tunusia ke ciki dai ya jefata cikin rikice-rikice daban-daban, masu nasaba da siyasa da suka janyo damuwa da bacin ran 'yan kasar ya karu, za mu duba abubuwan da suka haddasa hakan.
A shekarar 2011, Tunisia ta zama tushe kuma tsatson inda guguwar sauyi ta faro daga kasashen Larabawa.
An yi ta zanga-zangar kokarin kafa mulkin dimukradiyya da ya watsu tamkar wutar daji a kusan daukacin kasashen Larabawa, tare da kawo karshen mulkin wasu daga cikin shugabannin da suka kwashe gwamman shekaru su na mulki.
Alkawarin da ba a cika ba
Wani dan jarida kuma marubuci Akram Belkaid, sannan ƙwararre kan harkokin yankin Gabas Ta Tsakiya da harkokin Afirka, ya yi bayanin yayin da ake kallon Tunusia a matsayin wadda ta sanya don ba kan juyin-juya, ba ita ce kadai ta taka wannan rawa ba.
Ana dai ma ta kallon mai bada kwarin gwiwar kafa mulkin dumukradiyya a kasashen Larabawa.
Mista Belkaid ya shaidawa BBC cewa; "Tunisia ce kadai kasar Larabawa da ta ke da alamun dimukradiyya.
"Ana zabe mai cike da adalci, mutane na zanga-zanga ba tare da tsoron za a garkame su a gidan kaso ba."
"Kawai ka alakanta su da sauran kasashen da ke yankin da suka samu kansu cikin mulkin mulaka'u ko yakin."
Ya kara da cewa wasu daga cikin matsalolin sun faru ne sakamakon rashin cika alkawari gabannin lokacin juyin-juya halin.
Ya kara da cewa, "ana kallon Tunisia a matsayin wadda ta yi nasara a juyin-juya halin, amma maganar gaskiya akwai aiki ja a gaban ta."
Mista Belkaid ya yi amanna da cewa matakin da shugaba Saied ya dauka na korar firai minista Hichem Mechichi, da rusa majalisar ministocinsa bai dace ba.
"Amfani da karfi bai taba tasiri kan dimukradiyya ba, da zarar ka yi haka, za ka ci gaba da yi har akai matsayin da lamura za su lalace."
Rikita-rikitar Siyasa
Matakin korar Mechichi, ya biyo bayan zanga-zangar da aka dinga yi a biranen Tunusia, sakamakon ƙaruwar masu cutar korona.
Masu zanga-zangar na buƙatar rusa majalisa da sauke firaminista.
Wakiliyar BBC a arewacin Afirka Rana Jawad, ta ce: "Ga yawancinsu, suna ganin tamkar za a faro daga farko, wato suna da kyakkyawan fata kan sabuwar gwamnati.
"Ga wadansu kuma, su na ganin matakin abin darsa ayar tambayar, sannan matakin zai kara dagula lamura, ta yadda kafin a shawo kan lamarin sai an ji jiki."
Rikicin siyasar Tunusia ya samu asali ne tun lokacin guguwar sauyin yankin Gabas Ta Tsakiya, lokacin zanga-zangar watan Junairun shekarar 2011.
"Ita ta yi sanadin hamɓarar da mulkin Shugaba Zine El Abidine Ben Ali, da ya daɗe kan karagar mulki, tun daga lokacin Tunusia ta yi gwamnatoci Tara da suke yin watanni kan mulki su sauka.
Saied, sananne ne, kuma farfesa kan dokokin kundin tsarin mulki, ba kuma tare da masaniyar siyasa ba, ya yi nasarar zabe ba karkashin kowacce jam'iyya ba a shekarar 2019, inda ya yi nasara da gagarumin rinjaye.
Tawagar BBC mai sa a ido a yankin Gabas Ta Tsakiya da arewacin Afirka, ƙarƙashin Samia Hosny da Amira Fathalia, sun bayyana cewa har yanzu shugaban na da tarin magoya baya.
"Saied ya zama shugaban kasa da gagarumin rinjaye, inda ya lashe kashi 72 cikin 100 na ƙuri'un da aka kada, hakan ya nuna yadda 'yan Tunusia suka damu a kafa gwamnati tsayayya."
Sun ƙara da cewa; "Yana da tarin magoya baya, musamman cikin matasan kasar, wadanda su ke ganin ana hana su shiga a dama da su a fagen siyasa."
Shugaba Kais Saied ya nada firaminista Mechichi a watan Yulin 2020, bayan murabus din takwaransa Elyes Fakhfakh, wanda ya rike kumamin na watanni biyar kacal.
Sabon firai ministan da shugaban sun sha banban. Wani batu da ya shafi siyasar Tunusia shi ne dukkan shugaban kasa da 'yan majalisa ana zabensu ne da gagarumin rinjaye.
An gaza samun jam'iyyar da ta yi rinjaye a zaben 'yan majalisu da aka yi na shekarar 2019.
Cikin kwanakin da suka gabata, Shugaba Saied ya rattaba hannu kan dokar shugaban kasa da za ta ba shi damar rusa majalisar ministocinsa, ciki har da ministan cikin gida, da ministan tsaro, na shari'a.
Ya kuma nada shugaban tsaron fadar shugaban kasa a matsayin wanda zai sa ido kan ma'aikatar cikin gida da a baya Mista Mechichi ke jagoranta.
Ya kuma gargadi duk wanda ke daukar nauyin masu yi masa bore, wanda ka iya rikiɗewa tashin hankali, inda ya ce sojoji za su maida martani da albarusai.
Ricardo Fabbiani ya ƙara da cewa: "Yayin da akai taho mu gama da magoya baya, babu tabbaci kan girman kara barkewar tashin hankali, da lokacin da za a dauki wajen shawo kan lamarin."
Tabarɓarewar tattalin arziki
Tattalin arzikin Tunisia ya dade da faɗa wa halin ni 'ya su, tun ma kafin ɓarkewar annobar korona, sai dai tasirin annobar ya kara kassara kanana da matsakaitan 'yan kasuwa.
Rashin aikin yi ya ƙaru da kashi 18 cikin 100, kamar yadda ƙididdiga ta nuna, kuma rashin aiki ga matasa ya ƙaru da kashi 36 cikin 100 a ƙarshen shekarar 2020.
Daya faga cikin manyan matsalolin da aka samu na koma bayan tattalin arziki shi ne durƙushewar fannin yawon bude ido, saboda ɓarkewar annobar korona.
Haka nan fanin masana'antu shi ma ya durƙushe. A shekarar da ta gabata tattalin arzikin Tunusia ya samu koma baya da kashi 9 cikin 100.
Akram Belkaid ya yi ƙarin bayani. "Halin da tattalin arzikin ke ciki ya munana cikin watannin da suka gabata."
"Mutane sun dade su na jiran a sama musu ayyukan yi, tun lokacin da aka yi juyin-juya hali, kuma tun wancan lokacin babu wani batu da aka yi kan tattalin arikin," in ji masu sharhi kan harkokin yau da kullum.
Barkewar annoba
'Yan Tunusia na cikin damuwa kan halin da gwamnati ta sanya su a ciki kan barkewar cutar korona.
Kasar na daga cikin wadanda korona ta kashewa mutane a Afirka da yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda Hukumar Lafiya WHO ta bayyana.
Haka kuma wasu masana kimiyya da ke wallafa binciken su a mujallar duniya, da suke bibiyar aikin riga-kafin cutar corona a duniya, sun yi kiyasin zuwa 25 ga watan Yuli, kashi 8 cikin 100 na 'yan Tunusia miliyan 11.1 aka yi wa cikakkiyar allurar riga-kafin korona.
Mako guda gabannin nan, Tunusia ta yi rijistar wadanda suka kamu da cutar, kuma adadi mafi yawa tun bayan ɓarkewarta.
"Muna cikin matsanancin hali… fannin lafiya ya durƙushe, dakar muke samun gadon kwantar da maras lafiya," in ji mai magana da yawun ma'aikatar lafiya Nisaf Ben Alaya.
Ta kara da cewa; "Muna fadi tashin samawa marasa lafiya iskar shaka ta Oxygen, likitoci na matukar shan wahalar yadda za su kula da tarin marasa lafiya."