Zamantakewa: Yadda mace za ta kyautata zamantakewarta da uwar mijinta

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda za ki zamantakewarki da uwar miji
An wallafa

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na biyar ɗin, shirin ya yi duba ne kan Yadda mace za ta kyautata zamantakewarta da uwar mijinta.

Lale maraba da bude shirin zamantakewa na wannan mako.

Kamar na yadda na ce muku a makon da ya gabata, yau za mu bude babin surukuta ne.

Idan aka dauke sabani da ake yawan samu tsakanin mata da miji da kuma tsakanin kishiyoyi, gagarumar matsala ta gaba a fannin zamantakewa ita ce ta surukuta.

A wannan makon za mu fara duba matsalolin iyayen miji kan fuskanta daga matar ɗansu.

Da a ce ana bincike da adana bayanai da na tabbata za a samu miliyoyin matsaloli na matalar zamantakewar surukuta, musamman tsakanin uwar miji da matar ɗa, wanda shi ne ya fi zama ruwan dare gama duniya.

A matakin farko dai a ganina, dukkan iyayen da suka haifar miki mijin da suka yi wa tarbiyya har kika amince da aurensa, to sun fi gaban wulakanci ko raini.

A wannan zamanin da muke ciki za ku ga cewa don rashin kirki wasu har kiran uwar miji suke da sunan cancer ko hawan jini.

Wasu ma za a ga suna fatan su auri maraya, ma'ana wanda uwarsa ta mutu.

B sa tuna cewa su ma sun haifa ko kuma za ki haifa, ba sa tuna yadda za su ji idan matar ɗansu ta ambace su da cancer.

Sannan ba sa tuna yadda za su ji ida matar yayansu ko ƙaninsu ta ringa fatan Allah ya kashe mahaifiyarsu don ta sakata ta wala.

Wannan lamari ne da sam babu daraja a ciki.

Kina da iyaye don haka idan dai har kin san darajarsu to ya kamata ki san darajar na mijinki.

Wannan layi ne

Wasu na baya da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Wata ma sau da dama za a aga cewa a gidan mijin ta samu duk wata alfarma da ɗaukaka da take taƙama da ita, amma ita ba ta da matsala sai hana mijinta ya yi wa mahaifiyarsa alkhairi.

Mutanen da muka tattauna da su a wannan shiri su ne Fatima Fu'ad Hashim mai shafin Open Diaries a Facebook da Instagram da Hajiya Sadiya Datti mai shafin Perals of The North a Facebook da kuma fitaccen malamin Musulunci Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Dukkansu bakinsu ya zo ɗaya wajen cewa idan dai har da gaske mace na son mijinta tsakani da Allah, to ta haɗa shi tare da iyayensa ta so su.

"Ya kamata ta girmama iyayensa ta kyautata musu, ban da rashin kunya da tijara," kamar yadda Sheikh Daurawa ya ce.

Fatima Fu'ad ta shaida min cewa lamarin wasu matan kan ba ta mamaki musamman a zamanin nan.

Ta ce a kowace rana ta kan samu ƙorafe-ƙorafe daga mata da dama inda wasu ke mitar su ba sa son zama da uwar miji, ko su ce ba sa son yadda mazajensu ke nuna kulawa sosai ga iyayen.

"A ganinsu kamar yin hakan tauye nasu haƙƙin ne. Kuma agaskiya ba haka ba ne, ai dole namiji ya kula da mahaifiyarsa.

"Yawanci idan na tambayimatan nan shin mijin ba ya sauke haƙƙoƙinku ne yadda ya kamata, sai su ce a'a yana mana komai da muke so, kawai dai kula mahaifiyarsa da yake da ba ta muhimmanci ne ya yi yawa," a cewar Fatima.

Wannan layi ne

Ƙarin labarai masu alaƙa

Wannan layi ne

Hajiya Sadiya ma cewa ta yi, "ni abin na ban mamaki shi ne yadda kawai su wasu matan so suke su ga mijin ya ɗauki duk wata ƙauna da kulawa da tattali ya ɗora musu su kaɗai da ƴaƴansu, wato iyayensa ma so suke ya manata da su."

"Na san a wasu lokutan a kan samu fitinanun iyayen miji, amma duk da haka na gaba da kai na gaba da kai ne, sai ka bi su cikin lallami da siyasa da juriya.

"Idan takurawar ta yi yawa sai ki yi wa mijinki magana cikin nutsuwa ko ki sako waliyyai a ciki a warware matsalar cikin lumana ba tare da zubar da ƙima ba" a cewar Hajiya Sadiya.

Sannan akwai wani abu ɗaya da wasu matan ke mantawa, masu iya magana kan ce alheri yana rage gaba.

Da za ki daure ki zama mai kawar da kai da yawaita yin alheri ko mai ƙanƙantarsa, da ko uwar mijin mai takurawa ce to haƙiƙa za ta dinga ɗaga miki ƙafa a abubuwa da yawa.

A mako na gaba za mu taɓa batun iyaye miji masu takurawa matan ƴaƴansu ba dalili, da yadda za a magance abin.