Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
River Nile dam: Masar na neman sabbin ƙawaye a Afirka kan rikicin Madatsar Ruwa ta Nilu
Masar na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da ƙarfin sojinta a Afirka a yayin da rikici tsakaninta da Habasha kan gina katafariyar madatsar ruwa a wani yankin Kgin Nilu ke ƙara ƙamari, kamar yadda wani mai sharhi ɗan Masar Magdi Abdelhadi ya rubuta.
Ƙungiyar Ilimin Ƙasa ta Masar wato Egyptian Geographic Society, wacce aka ƙirƙira a shekarar 1875, tana da rubutaccen tarihi ajiyayye da ke bayani kan daɗewar da Masar ta yi tana nuna sha'awarta a kan yankin kudu da hamadar Saharar Afirka.
A cikinsu akwai wata tsohuwar taswira da ke nuna iyakokin kudu na Masar a Tafkin Victoria a Gabashin Afirka.
An ƙirƙire ta ne a lokacin da Masar ke hanƙoron ƙarfafa ikon daularta wadda ba ta ɗaɗe ba, lamarin da ya mayar da Sudan ƙarƙashin ikon Masar ta kuma yi ƙoƙarin mayar da Habasha ƙarƙashinta a wani mummunan yaƙi da aka yi daga shekarar 1874 zuwa 1876. Sai dai Masar ta sha mummunan kashi a ƙarshe.
Bayan shekara 70 da lamarin, Masar ta yi wasu sauya-sauye kan matsalolin da ta fuskanta a burin ƙarfafa daularta, a yayin da ta zama kan gaba wajen nuna adawa mulkin mallaka a Afirka da ma sauran yankuna.
Amma a lokacin da ta samu kanta a cikin yaƙin ƙasashen Larabawa da Isar'ila, sai ƙarfin kai-kawonta ya ragu a kudu da hamadar Sahatat Afirka.
A shekaru kaɗan da suka wuce, an ga wani irin sauyi na sake mayar da hankali kan Afirka, musamman da ƙasashen da Kogin Nilu ya ratsa,
Masar ta cimma yarjejeniyar soji da na tattalin arziƙi da Uganda da Kenya da Burundi da Rwanda da Djibouti a watannin baya-bayan nan.
Tuni Alƙahira ta cimma wasu yarjejeniyoyi da Sudan, inda a baya-bayan nan ta gudanar da wasu atisayen soji da suka haɗa da amfani da jiragen yaƙi da dakaru na musamman.
Masar ta haɗa babban layin wutar lantarkinta zuwa Sudan kuma ana shirin haɗa layin dogo ma kamar haka, da kuma babban burin fara jigilar jirgin ƙasa daga birnin Alexandria zuwa Cape Town na Afirka Ta Kudu.
Babban dalilin yin wannan sauyi na manufofin ƙasashen waje shi ne kan gina madatsar ruwan da Habasha ke yi a Kogin Nilu mai cike da ce-ce-ku-ce, wanda aka fi sani da Grand Ethiopian Renaissance Dam (Gerd).
Nael Shama, wani ƙwararre a kan manufofin ƙasashen wajen Masar, ya ce: "Masar ta daɗe tana dogara da diflmasiyya wajen warware bambance-bambancenta da Habasha kan rikicin Gerd.
"Ga dukkan alamu an gama amfani da dukkan matakan sasantawar, ko kuma an kusa."
Tsoron afkuwar fari
Tanzania ma wata abar misalin ce, inda Masar take zuba jari sosai a harkar gina madatsar ruwan da za ta samar da wutar lantarki ta Julius Nyerere a Kogin Rufiji.
A bayyane yake cewa Masar na nuna aikin a matsayin misalin abin da take son yi don taimakon ayyukan ci gaba a ƙasashen da ke yankin Kogin Nilu.
Kuma wannan ne saƙon da Masar - wacce ba ta da sauran hanyoyin samun ruwan sha da na ayyukan gona fiye da Nilu - take ta ƙoƙarin neman goyon bayan ƙasashen duniya.
Ba wai tana adawa da madatsar ruwan Habasha ba ne, amma tana matuƙar taka tsan-tsan kan tasirin da hakan zai yi kan ruwan Nilun idan har Habashar ta ƙi sanya hannu kan yarjejeniyar bisa ƙa'ida, kan yadda za ta dinga gudanar da ayyukanta.
An fargabar madatsar ruwan na iya mummunar illa kan fannin noma na Masar tare da tunkuɗo datti kan ƙasra nomanta, abin da ka iya jawo mummunan fari da rashin aikin yi. Habasha, a hannu guda, na kallon Gerd a matsayin wani muhimmin abu da ke taka rawa kan buƙatunta da ci gabanta, da kuma samar da wutar lantarki ga al'ummarta.
Alaƙar kasuwanci, ba yaƙi ba
Don haka sauya alƙiblar Masar da mayar da hankali kan manufofinta na ƙasashen waje a kudu da hamadar Saharar Afirka abu ne da ya kamata a ce an daɗe da yin sa, amma wasu ƴan ƙasar na cewa, ya yi kaɗan kuma an makara.
"Ƙarfin faɗa a ji a siyasar zamani ba kawai maganar bindigogi da makaman yaƙi ba ne," a cewar Walaa Bakry, wani malami a Jami'ar Westminster da ke Birtaniya.
"Yarjejeniyar tsaro da wasu ƙasashen yankin Kogin Nilu kamar su Burundi da Uganda abu ne mai kyau, amma ba zai bai wa Masar ƙarfin faɗa a jin da take so ba," kamar yadda ya rubuta.
Ƙaƙƙarfar alaƙar kasuwanci za ta iya kawo nasarar fiye da shiga fagen yaƙi, ya ce, yana mai nuni da alaƙar kasuwancin da ke tsakanin Masar da dukkan ƙasashe taran da ke yankin Kogin Nilu.
Sai dai a Masar yanayin yana zama na barazana. Gwamnatin Masar, a taƙaice ma dai shugaban ƙasar da kansa yana fuskantar matsin lamba kan nuna wa Habasha ba sani ba sabo.
Ko magoya bayan Abdel Fattah al-Sisi sun fara guna-guni kan abin da ba a tunanin zai yiwu - cewa gaza kare haƙƙoƙin ruwan Masar na nufin ba zai sake samun damar mulkar ƙasar ba.
Masar dai na fatan samun tawagar ƙawaye kan batun Habasha zai sa kwalliya ta biya kuɗin sabulu idan har aka kasa kauce wa yin fito na fito da Habashar.
Ƙarin labarai kan abin da ya shafi Kogin Nilu:
Tuni Masar da Sudan suka kai batun rikicin madatsar ruwan gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, saboda sun ɗauki hakan a matsayin abin da ke yi wa zaman lafiyar yankin barazana.
Kafin nan dama an taba kai lamarin gaban kwamitin, wanda shi kuma ya miƙa shi ga Ƙungiyar Tarayya Afirka, wacce ta gaza warware shi.
Da Masar da Sudan duk sun zargi Habasha kan hakan, yayin da ita kuma Habashar ta zargi Masar d amfani da sasantawar a matsayin samun damar kankane batun ruwan Nilun.
Atisayen soji da aka yi kwanan nan a Sudan an yi da niyyar tura saƙon garhaɗi ba ga Habasha ba kawai, har ma ga duniya baki ɗaya - cewa ƙasashen biyu ba za su kasa motsa ƙwanjinsu ba idan buƙatar hakan ta taso, a lamari mai muhimmanci na ko a mutu ko a yi rai da ya shafi ruwan sha.
Yarjejeniyar Masar kan haɗin kan soji da Uganda da Kenya da Burundi ya bayyanar da wancan saƙon, duk da cewa da wahala waɗannan ƙasashen su yarda su shiga cikin yaƙin yankin inda nasu buƙatun suka sha bamban.
Idan dukkan matakan diflomasiyya suka gaza yin aiki, akwai shakku cewa ra'ayoyin mutane a Masar zai nuna goyon bayan amfani da ƙarfin soji idan akwai buƙatar hakan.
Kamar a Sudan, inda babu tsayyayyen ra'ayi, ba wai don ba kamar Masar ba, Sudan za ta iya cin moriyar madatar ruwan, wacce zat arage ambaliayr ruwa da bata damar samun lanatrki cikin rahusa.
Amma masu sa ido sun yi ittifaƙin cewa, duk da yake Masar da Sudan suna da muradu na siyasa da ƙarfin soji da ma dabaru, wani abu da a yanzu ake son amfani da shi game da kawo tsaiko wajen gina madatsar ruwan nan da shekaru ba zai wareware matsalar ba.
A maimakon haka, zai ƙara rashin yarda da rura wutar tsohuwar gaba da alfaharin ƙasashen da kuma son ramuwar gayya.