Tsaka mai wuyar da ake ciki wajen sake gina Gaza ba tare da ƙarfafa Hamas ba

Yaran Palsdinawa zaune a kusa da buraguzan gine-gine a Gaza da hare-haren Isra'ila ta sama suka lalata a ranar 9 ga watan Yunin shekarar 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubban Palasdinawa ne suka shaida yadda aka lalata ko kuma rushe gidajensu
    • Marubuci, Daga Yolande Knell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
  • An wallafa

Dauke da makaman roka masu cin dogon zango da jirage marasa matuka, mayakan Hamas sanye da kakin soji sun yi ta sintiri a Zirin Gaza tun bayan barkewar mummunan fada da Isra'ila.

A ziyararsa ta baya-bayan nan zuwa birnin Kudus da Gabar Yamma ta Kogin Jordan, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Dominic Raab, ya shaida min cewa ''yana da matukar muhimmnaci'' a tabbatar da cewa tallafin kudade sun kai ga ''Palasdinawa don sukaka halin kuncin da suka shiga, kama ba su fada aljihun mayakan Hamas ba''

Kungiyar masu kaifin ra'ayin addinin Islama wacce ke rike da ikon yankin na Gaza bata yadda da 'yancin wanzuwar Isra'ila ba.

Mayaka Paladinawan Hamas na baje kolin makaman harba rokoki lokacin gangamin nuna kin jinin Isra'ila a kudancin Zirin Gaza (27 ga watan Mayu, shekarar 2021)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sojojin Hamas na gudanar da fareti a Gaza bayan yarjejeniyar tsagaitar wutar da kasar Masar ta shiga tsakani

Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, a Gaza wannan rikici ya lalata ko kuma rushe gidaje fiye da 16,000, tare da makarantu 58 da cibiyoyin horarwa daasibitoci tara da dakunan shan magani 19 da sauran muhimman gine-gine.

Isra'ila ta ce ta kai hari kan wurare fiye da 1,000 na mayakan Hamas.

Iyalan Khalidi a birnin Gaza na cikin dubban da suka rasa gidajensu. Lokacin da jiragen Isra'ila suka kai hari kan gine-ginen makwabtansu, gidan su ya kama da wuta a lokacin fashewar.

1px transparent line

"Na samu wasu gilasai a warwatse a kan kayan wasan da na. Na yi kuka sosai a lokacin da na ga barnar,'' in ji Waad al-Khalidi, wacce yanzu yake zaune a gidan 'yanuwansu tare da mijinta da jaririn su.

"An kawo karshen yakin amma bamu da kudin yin wani gyara. Ina son in ga na sake ganin gidanmu mai kyau.''

Mutane akalla 256 ne suka hallaka a Gaza, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, kana 13 suka hallaka a Isra'ila a yayin fadan.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce cikin mutane da suka mutu a Gaza akalla 128 fararen hula ne. Rundunar sojin Isra'ila ta ce 200 daga ciki mayakan Hamas ne; Jagoran kungiyar Hamas Yahya Sinwar, ya kiyasata adadin mayakan da suka mutu cewa 80 ne.

Bayanan bidiyo, Kananan yara biyu daga birnin Gaza da Isra'ila abubuwan da suka shaida a rikicin Israel da Gaza

Toshe hanyoyin kasa da na ruwa a Gaza, wanda kasashen Isar'ila da Masar suka yi da alamu zai haifar da tsaiko wajen ayyukan sake gina Gaza.

Sun yi hakan ne bayan da kungiyar Hamas ta karbe daukacin ikon wani karamin yanki daga hukumomin Palasdinu a wani mummunan artabu a shekarar 2007, shekara daya bayan ta samu galabar lashe babban zaben da aka gudanar.

Hakan ya durkusar da tattalin arzikin amma ta samu galaba kadan ne a yunkurinta kan batun tsaro: da sauran baubuwa da suka hada da samun kai kaya ga mayakan.

A cikin wanaki 11 da aka shafe ana yakin a cikin watan Mayu, rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki fiye da 4,300 daga Gaza zuwa garuruwa da biranen Isra'ila, tare da lalata da kuma rushe gidaje da sauran gine-gine.

Karfin yadda aka harba su da kuma irin girman barnar da suka haddasa sun fi na mummunan barkear fadan da aka samu a rikicin shekarar 2014.

"Sun ƙara ɗaura ɗamara kana suka kara makaman rokoki masu cin dogon zango kadan a rumbun ajiyar makaman su, da alamu sun kara wa kan su karfi,'' in ji Michael Herzog, wani tsohon babban soja a cibiyar Washington Institute for Near East Policy.

Iyalan gidan Vaizel zaune a dakin dafa abinci na gidansu da makamin rokar da aka harbo daga Gaza ya abka wa a birnin Ashkelon, Isra'ila (20 ga watan Mayu, shekarar 2021)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rokokin da aka harba daga Gaza sun fada kan gidaje a kudanci da tsakiyar Isra'ila

A shekarar 2014, kasar Masar takammala lalata hanyoyin karkashin kasar da ake fasa-kwaurin makami dake kan iyakarta da Gaza, tare da dakatar da shigo da makamai masu linzami daga kasar Iran.

Amma kuma, mayakan Hamas masu da'awar jihadi sun cigaba da amfani da kwarewar kasar Iran wajen kera nasu makaman rokar a wata masana'antarsu a asirce.

A shekarar da ta gabata, wani rahoto na musamman na kafar yada labarai ta Al Jazeera ya nuna kwamandojin kungiyar Hamas na ikirarin sun kere makamai masu linzami daga bututan ruwa na matsugunan Isra'ila da aka bari a Gaza, da kuma wasu ababan fashewa da Isra'ila ta harbo da ba su fashe ba dakuma wani jirgin ruwan yaki na Birtaniya da ya nutse a cikin tekun lokacin yakin duniya na daya.

Palestinians sit near destroyed houses in the northern Gaza Strip (1 June 2021)
REUTERS
Damage to housing and services in Gaza

  • 16,250housing units sustained some degree of damage

  • 1,165destroyed housing and commercial units in 331 buildings

  • 58education facilities damaged

  • 9hospitals partially damaged

  • 19clinics damaged

  • 400,000people with no regular access to safe piped water

Source: UN OCHA
1px transparent line

"Kamar yadda masu iya magana ke cewa, dole kanwar na ki,'' in ji cewar Michael Herzog wanda ya kalli rahoton, '' amma bayan nan, ina ga abinda ba a bayyana ba shi ne cewa kungiyar Hamas ta amgfana da abubuwa biyu daga kayyakin kana ta yi amfani da su wajen ayyukan sojin ta.

Isra'ila ta tsaurara matakan hana shigo da gwanjon kayyaki - da suka hada da bututai, da siminti da karafuna - da ka iya yin amfani a bangaren ayyukan soji ko na fararen hula. Kasar Masar ta amince shigowa da kayyakin gini kadan.

Amma duk da haka, Isra'ila ta ce a hare-haren bama-baman da ta kai na baya bayan nan a Gaza, talalata fiye da kilomita 100 na hanyoyin karkashin kasa da ta ke kira ''the Metro'' fiye da mayakan Hamas suka gina a kan miliyoyin daloli.

Wata babbar motar daukan kaya na wucewa ta shinge bayan da Isra'ila ta sake bude tsallaken Kerem Shalom da Zirin Gaza (25 ga watan Mayu, shekarar 2021)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Majalisar Dinkin Duniya ce ya kamata ta duba kayyakin ginin da ke shiga Gaza

Majalisar Dinkin Duniya na fuskanra matsin lamba kan ta yi garanbawul kan yadda za a rike duba shiga da kayayykin gini zuwa Gaza bayan rikicin shekarar 2014.

"Yanzu haka muna kan aiki game da wannan tare da mahukuntan Palasdinu da na Isra'ila don gano yadda zamu iya mu yi aikin cikin sauri,'' in ji Lynne Hastings, babbar jami'ar tsare-tsare na Majalisar Dinkin Duniya kan matsugunan Palasdinawa da aka mamaye.

Ta shaida wa manema labari cewa an kuma gudanar da binciken kwawaf ''don gano ko akwai kurai-kurai da wani bangare suka tafka a shekaru masu yawa da suka gabata ko kuma babu, don tabbatar da cewa ba a karkata akalar kayan tallafin ba''.

Ya kamata a ce masu shigo da kayan da aka amince da su ne da na'urorin bincike za su lura da wajen ajiyar duka kayan tallafin da ke shiga da su cikin Gaza, yayin da masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya su duba ko ana amfani da su ta hanyar da ta dace.

Wani yaro Bapalasdine dauke da wata katifa yayin da yake tafiya a kan buraguzan gine-ginen da suka rushe a birnin Gaza (2 ga watan Yuni, shekarar 2021)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mahukuntan Palasdinu sun yi kiyasin cewa akwai bukatar kwashe kusan tan 270,000 na buraguzan a Gaza

Amurka da sauran kungiyoyin bayar da agaji na kasashen waje sun jaddada cewa dole hukumar Palasdinu da kasashen duniya suka san da zaman ta ce kawai za ta kasance abokiyar huddar su wajen sake gina Gaza.

Akwai kuma bukatar ga tallafin kudade na kasar Qatar - wanda a baya ke zuwa kai tsaye yankunan Palasdinawa - abinda kungiyar Hamas ta fito ta nuna adawa a kai.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas ya yi magana damanema labari a birnin Ramallah, in Ramallah, da Gabar Yamma ta Kogin Jordan (25 ga watan Mayu, shekarar 2021)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Amurka na bukatar aiki tare da hukumar Palasdinu don tabbatar da cewa kungiyar Hamas bata amfana daga tallafin sake gina Gaza ba

Wasu masu lura da al'amuran da ake tafiya su nuna damuwa kan yanayin yadda ake amfani da kayan tallafin a matsyin wani makami na diplomasiyya wajen kara halarta shugabancin hukumar Palasdinu.

Jim kadan kafin rikicin na Gaza, shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ya dage zaben farko na majalisar dokoko a cikin shekaru 15. Ya bayyana cewa saboda bangaren sa na jam'iyar Fatah ta nuna alamun rasa kuri'unta a kan kungiyar Hamas.

"Babbar matsala ce," in ji lauyar Palasdinu, Diana Butto.

"Tana kokarin amfani da sakamkon zaben ba tare da yin zaben ba. Suna fada wa mutanen Gaza: muddin kuna son a sake gina abubuwa, ba za mu matsa kan gudanar da zabe ba, amma za mu yi kokarin ganin wadannan mutanen da mu ke so sun kasance jagorori.''

Alkahira na cigaba da shiga tsakani a tattaunawar game da tallafin a tsakanin bangaren Palasdinu da na Isra'ila. A wani yunkuri na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza.

Tawagar kasar Masar na aikin kawseh buraguzan gine-gine a birni Gaza City (5 ga watan Yuni, shekarar 2021)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kasar Masar ta aike da injiniyoyi zuwa Gaza don taimaka wa wajen kwashe buraguzn gine-ginen da suka rushe

Akwai wasu bukatu daga Isra'ila game da batun bacewar fararen hula biyu 'yan Isra'ila da gawawwakin sojojin Isra'ila biyu da kungiyar Hamas ta cafke da a dawo da su gida.

Yayin da ake cikin wannna damuwa, shugabannin kungiyar Hamas sun tabbatar wa da Palasdinawa cewa duka gidajen da ke bukatar faskwarima z a a gyara su.

Amma a birnin Gaza , Miss Khalidi ta san cewa tana da sauran jira.

"Ban damu sosai game da batun siyasa na, kuma ban damu da ko wane ne zai biya ba,'' ta ce, '' amma ina son kungiyar Hamas ta cika alkawarin da ta yi.''