Yadda masu kaurin murya suka fi jan hankalin mutane

A woman holds her hand near her mouth

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga William Park
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa

Ƴan Faransa na kiransa "voix de chambre à coucher". Murya ce mai nauyi, mai ɗaukar hankali da ke bai wa wasu mutane ikon jan hankali. Akwai cikakken bayani kan wannan.

Wasu na da murya mai daɗi fiye da wasu, kuma tun da kusan duka ƙasashen duniya sun amince da haka, wannan na nuna cewa wannan na da muhimmanci ga tarihin ɗan Adam.

Karin harshe hanya ce ta gane mutane. Ana ganin masu magana da muryoyi masu daɗi a matsayin mutanen da suka san abin da suke yi kuma masu tausayi da riƙon amana.

Wannan na sanya wa a yi masu kallon mutane masu ban sha'awa. Don haka, me ya sa wasu karin harshe ke da ɗaukar hankali?

Akwai wani abu na musamman game da murya da kowa ke da shi. "Duk al'adarka, duk macen da ta fito daga Japan ko Amurka ko Faransa ko ma wace ƙasa ce a duniya - sun fi son maza masu kaurin murya," in ji Melissa Barkat-Defradas, wata mai bincike kan harsuna a Jami'ar Montpellier.

An gano cewa son kasancewa da maza masu kaurin murya a ko in ane kama daga dajin Amazon zuwa Tanzania da daruruwan wasu ƙasashen na Yamma da waɗanda ba na Yamma ba.

Mutane na alaƙanta kaurin murya da iya farauta da nasara a wurin aiki da ƙarfi.

Muna ganin ƴan siyasa masu kaurin murya a matsayin masu mayar da hankali kuma waɗanda za mu iya zaɓa, ko mace ko namiji.

A woman sits opposite a man

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ko murya mai kauri na iya sama muku aikin da kuke so?

Mata da maza masu neman aiki da ke da kaurin murya sun fi saurin samun aiki.

Me wannan ke nufi kan yadda muke kallon halayyar mutum?

Hawan sautin muryar maza da mata na raguwa a lokacin balaga. Amma kana iya gane yadda hawan sautin muryar namiji zai kasance dangane da yadda take a lokacin da yake shekara bakwai.

Sautin murya ya danganta ne da yawan sinadarin testosterone a jiki, wanda ke taka muhimmiyar rawa a zaɓen wanda za a yi tarayya da shi.

A woman listens to a man speaking with a slightly sceptical face

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sauyi a muryar mutane na iya gaya mana wani abu dangane da lafiyarsu da arziƙinsu da aikin da suke yi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci

Yawan sinadarin testosterone ga maza manya ya danganta da yawan sinadren androgens da suka samu daga mahaifiyarsu a makonnin takwas zuwa 24 na ciki.

Wannan na nufin cewa wani abu da ka iya taka rawa a yawan ƴaƴanmu ya samo asali ne tun daga kuruciya kuma yana da alaƙa da sinadrin hormones da iyayenmu mata ke da su kafin a haife mu.

Sai dai irin muryoyin da maza su ka fi so a mata sun sha banbam. Tsawon lokaci an yi tunnain cewa maza sun fi son mata masu zaƙin murya.

Sai dai kallon da ake yi wa mata masu kaurin murya a matsayin masu jajircewa ya janyo wani tunani mai zurfi daga masana Pisanki da Barkat-Defradas: Shin muna iya sauka sautin muryarmu zuwa yadda muke so?

Bincike ya gano cewa muna sauya sautin muryarmu ta zo dai-dai da wanda muke magana da shi, kuma idan muna so mu nuna soyayyarmu ko kulawarmu ga wanda muke tare da shi a lokacin, sai mu karya sautin muryarmu ta yi kama da nasu, a cewar Pisanki.

Haka kuma, saukewa ko ɗaga sautin muryarmu na iya zama alama ta yadda mu ke son mutum, kuma yana jan hankalin wanda mu ke tare da shi.

Muna amfani da muryarmu wajen karkatar da tunanin wasu mutane.

A woman laughs as she talks to a man at a speed dating event

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan muna tare da wanda muke so muna sauya muryar mu

Idan muna hira mai daɗi da wani, mu na sauya muryarmu. Amma idan muna hira da wanda ya ɗauki hankalinmu, lamarin na sauyawa.

Ga maza, sai muryarsu ta ƙara yin ƙasa yayin da a mata kuma, sai muryarsu ta ƙara sama.

Wani bincike da aka yi kan wasu ƴan Faransa, ya nuna cewa maza sun fi son mata masu kaurin murya - abin da Pisanki ya ce hakan na iya nuna cewa abubuwan da maza ke so a mata na sauyawa, wato sun fi son mata masu son mata masu cike da buri kuma masu son yin aiki sosai.

"Babu mamaki mata na so ne su mayar da muryarsu kamar ta maza - mai hazaƙa. Mata yanzu sun fara magana a hankali," a cewar Pisanki.

"Kuma babu mamaki, a wasu al'adun maza na son matan da ke nuna girma da hazaƙa."

A man and a woman sit at a table talking and laughing.

Asalin hoton, Getty Images

Idan kuna neman wani dalilin da zai hana ku karya harshe, akwai shaidar cewa idan ba ku yi ba ya fi.

Ana ganin mutanen da ba su cika kyau ba kuma ba su fiye muni ba kuma muryoyinsu ma haka suna da wasu ƙwayoyin halitta da ke taimaka wa garkuwar jikin da ke gano waɗanne ƙwayoyin halittar ne na jikinmu kuma waɗanne ne ba namu ba.

Yin hakan na nufin saurin gano ƙwayoyin cuta da kashe su.

Two men gaze into each others' eyes lying on a bed

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mafi yawan binciken ya mayar da hankali ne kan mutanen da ke son jinsin da ba nasu ba.

Da aka tambayi Pisanki, ta amince akwai wariya da ake nuna wa wajen bincike kan muryar maza.

Waɗannan bincike-binciken sun kafu ne kan yadda jikinmu ke aiki da abin da muke so.

Don haka, ga mu sauran mutane, watakil kawai mu samu gamsuwa a wanda ya iya hira.

A man and a woman walk away from the camera down a city street

Asalin hoton, Getty Images