Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Siyasar Amurka: Me zai faru a wajen zaman tsige Trump?
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar shari'a daga ƴan majalisa bisa zarginsa da haddasa zanga-zanga a majalisar dokokin kasar.
A watan jiya ne Mr Trump ya kafa tarihi a matsayin shugaban ƙasa na farko a Amurka da ya taɓa fuskantar tsigewa har sau biyu.
Yan majalisar wakilai daga ɓangarorin Republicans and Democrats ne suka jefa ƙuri'ar amincewa da tsige Trump saboda laifin tunzura jama'a.
Daftarin da suka rubuta ya yi zargin cewa tsohon shugaban ya yi zantukan da ba su da tushe balle makama game da cewa an yi masa magudi a zaben shugaban ƙasa, kuma ya fake da hakan wurin zuga magoya bayan shi suka aukawa majalisa a ranar 6 ga watan Janairu.
A yanzu hankali ya koma kan matakin da majalisar dattawa za ta dauka na tsigewa ko kuma wanke shi.
Wannan al'amari zai shiga kundin tarihin Amurka, cewa a karon farko a tarihi an tsige shugaba bayan da tuni ya bar ofis.
Me muke tunanin zai iya faruwa?
Da farko dai shari'ar da za a yi a majalisar dattawan na da alaƙa da siyasa a maimakon ta'addanci.
A ƙarshen zaman za a jefa ƙur'ar da za ta nuna cewa Trump na da laifi ko kuma an wanke shi.
Kuma sai a na samu kashi biyu-bisa-uku na sanatocin da suka aminta da ya aikata laifin kafin tsigewar ta tabbata.
Amma idan har aka samu adadin da ake bukata wurin tsige shi, to yan majalisar na iya jefa ƙuri'ar haramta Mr Trump sake riƙe ko wane irin ofis a Amurka.
Yaya zaman zai gudana?
Za a fara zama a majalisar dattawa kan shari'a ranar Talata inda za a soma da shafe awa hudu ana tattaunawa kan ko kundin tsarin mulki ya aminta da ayi wa tsohon shugaba shari'a bayan ya bar ofis.
A ranar Laraba kuma za a bai wa masu goyon bayan ƙudurin da masu adawa da shi awa 16 sun faɗi dalilansu.
Bugu da kari za a tafka muhawarar neman amincewa da gabatar da shaidu.
Ba a bayyyana ko yaushe za a kai ana shari'ar ba a majalisar dattawan, amma dai ƴan Democrats na buƙatar a kammala da gaggawa.
Babban dalilinsu kuwa shi ne don majalisar ta samu maida hankali ga kudurin shugaba Joe Biden kan tallafin Korona.
Mai masu gabatar da ƙara suka suka ce?
Mr Trump ne ke da alhakin zanga zangar da ta afku a majalisa kuma dole ne ya fuskanci hukunci, a cewar ƴan Democrats.
A wani zama da suka yi kafin jefa kuriar tsige shi sun jaddada cewa ƙin amincewa da cewa ya sha kaye a zaben da aka yi "ya tunzura wasu ƴan ƙasar har suka boren".
Sun kuma ce ya "ta'zzara lamarin" a ranar 6 ga watan Janairu, bayan da ya umurci magoya bayansa da su nufi ginin majalisar wato Capitol.
Bugu da ƙari sun kuma rubuta cewa "duk da cewa ya bar ofis dole ne ya fuskanci hukunci saboda ya aikata laifin ne kafin ya sauka."
Akan haka suke neman a hana Mr Trump sake tsayawa takara har abada.
Shin ko Trump na da wata kariya?
Tun a lokacin da ƴan Demokrats suka furta batun tsige Trump ne lauyoyinsa suka yi watsi da yunƙurin.
A cewar lauyoyin abin da Trump din ya faɗa bai kai ya haddasa zanga-zanga ba.
Suka ƙara da cewa kalmar da tsohon shugaban ya yi amfani da ita cewa "ku yi fada" bai dace a fassara ta kai tsaye ba.
Lauyoyin sun kuma ƙara da cewa magoya bayan Trump ɗin sun shirya zanga-zanga ta ƙashin kansu tun kafin jawabin Mr Trump.
A kan haka suka ce tunda kuma ya riga ya sauka, babu dalilin da zai sa a yanke masa hukuncin da ya hau kan shugaba mai ci.
A don haka suka bayyana shari'ar a matsayin wani batun siyasa da nufin "hana ƴan adawa cewa uffan."
Ko ya halasta ayi masa sharia duk da baya kan mulki?
Wannan abu ne da ba a taɓa yi ba saboda abune mai wahala a iya yankewa kai tsaye cewa kundin tsarin mulki bai zo da shi ba.
Bambancin shariar da wadda aka yi wa tsohon shugaban Richard Nixon shine ya yi murabus ne kafin a kammala shari'arsa a shekarr 1974.
Akan haka Mr Trump zai iya ɗaukaka kara cewa an yi masa shari'a a lokacin da baya kan mulki duk da ba shi ba murabus ya yi ba.
Amma dama an taɓa tsige wasu masu riƙe da muƙamai a Amurka duk da cewa ba na shugaban ƙasa ba ne.
Ko Trump na da abinda zai gabatar a matsayin shaida?
Dama abinda masu shigar da ƙara ke nema kenan. A makon da ya gabata sun gayyace shi da ya zo ya rantse a wuri da kuma lokacin da ya zaɓa.
Masu shigar da ƙarar sun ce yin shurunsa ƙarin wata shaida ce cewa abin da ake tuhumarsa gaskiya ne.
To sai dai ƴan awanni da gayyatar lauyoyin Mr Trump suka yi watsi da buƙatar masu shigar da ƙarar.
Suka kuma bayyana cewa ba ba zai taɓa yin magana kan batun ba kamar yadda masu shigar da ƙarar ke bukata.
Su waye za su jagorancin shari'ar?
Alƙalin alƙalan kotun ƙoli John Roberts ne ya jagoranci zaman tsige Donald Trump na farko amma yanzu ba shi zai jagoranci zaman ba.
Sanata Patrick Leahy na jam'iyyar Deomkrats wanda kuma shine mutun na uku da ka iya karɓar shugabancin ƙasa ne zai gudanar da shari'ar.
Mutane tara ne da suka haɗa da Mr Leahy za su jagoranci zaman, kuma ana musu inkiya da 'manajojin tsige shugaba'
A ɗaya ɓangaren Lauyoyi Bruce Castor da David Shoen ne za su tsayawa Mr Trump.
To amma har yanzu babu tabbacin ko zai ƙara yawan lauyoyin da za su tsaya masa.
Tun kuma an rsantsar da sanatocin Amurka su 100 da za su jefa ƙuri'a kan tirka-tirkar.
Ko za a iya kama Trump da laifi a majalisar dattawan?
Ƴan Democrats na da kujera 50 daga cikin 100, saboda haka suna bukatar ƙarin 17 daga ɓangaren Republican kafin su samu kashi biyu-bisa-uku.
Kuma wannan abu ne mai wuya, lura da goyon bayan da Mr Trump ya samu daga ƴan majalisar Republican.
To amma fa a majalisar wakilai 10 daga cikinsu sun jefa ƙuri'ar amincewa a tsige shi, kuma take-taken wasu sanatoci ya nuna cewa a shirye suke su ma su yi hakan.
Duk da haka a makon da ya gabata 45 daga cikin 50 na ƴan Republican ɗin sun jefa ƙuri'ar bukatar a yi watsi da shari'ar kwata-kwata.
Ko Trump zai iya sake yin takara idan aka kama shi da laifi?
Matsawar aka kama shi da laifi a majalisar Dattawa, hakan na nufin akwai bukatar ƴan majalisa su sake jefa wata ƙuri'ar neman hana shi sake tsayawa takara, don wataƙila ya iya sake neman takarar a 2024.
Wannan shi ne babban ƙalubalen da zai iya fuskanta.
Kuma ƙu'ri'ar masu rinjaye kawai ake bukata a hana shi neman takara ko kuma samun wani haƙƙi da yakamata tsohon shugaba ya samu kamar fansho ko kuma wata alfarma.
Saboda haka anan sanatoci 50 da ƙuri'ar mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris ya isa ya dakushe duk wata dama da Trump ke da ita ta sake neman wani muƙamin gwamnati.
Kuma hakan zai buɗe hanya ga masu son tsayawa takara anan gaba, da kuma faranta ran wadanda ba sa ga maciji da Trump a jam'iyyar Republican.
Laifin me Trump ya yi ake tsige shi a karon farko?
An tsige shi ne kan zargin aikata ba daidai ba kan hulɗa tsakanin Amurka da Ukraine, to amma tuni ya musanta zargin.
A lokacin an zarge shi ne da matsawa shugaban Ukraine lamba da ya binciki hulɗoɗin da Mr Biden da ɗansa Hunter ke yi a ƙasar.
Kuma an tuhume shi da yi wa Ukraine din barazanar dakatar da taimakon da Amurka ta saba ba ta idan har shugaban bai aikata hakan ba.
A ƙarshe kuma majalisar wakilai ta tsige shi a kan wannan zargi, takwararta ta majalisar dattawa da ƴan Republican ke da rinjaye a lokacin kuma ta wanke shi.