Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Yadda cutar korona ta jawo ƙarancin iskar oxygen a ƙasashe masu tasowa
- Marubuci, Daga Pablo Uchoa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Kafin iskar oxygen ta ƙare a asibitin, Maria Auxiliadora da Cruz ta yi ta nuna alamun ƙrfin gwiwa na cin galabar cutar korona.
A ranar 14 ga watan Janairu sai yawan iskar da take shaƙa ya haura yadda ake so na kashi 95 cikin 100 - amma cikin sa'o'i kaɗan sai ya sauƙa zuwa kashi 35 cikin 100, kuma hakan na iya haifar mata da illa.
A wannan gaɓar, marasa lafiya yawanci sai dai a taimaka musu da iskar oxygen ta inji. A maimakon haka, sai Maria wacce ma'aikaciyar jinya ce ta mutu.
"Abin na da ban tsoro," in ji surukarta Thalita Rocha. "Babban bala'i ne. Marasa lafiya da dama masu yawan shekaru sun shiga wani yanayi."
A wani bidiyo mai ban tausayi da ya yaɗau a shafukan sada zumunta kamar wutar daji, ta bayyana abin da ya faru a Policlínica Redenção a birnbin Manaus da ke yankin arewacin Brazil.
"Muna cikin wani yanayi na tashin hankali. Babu iskar oxygen ko kaɗan a kafatnin ɓangaren gaggawa... Mutane da dama na mutuwa."
Ta shaida wa sahen BBC Brazil cewa mutum 10 ne suka mutu a rana ɗaya a ɗakin asibiti ɗaya, kuma ta yi amannar cewa da surukarta na iya tsira.
"Ba cutar korona ce ta kashe ta ba. Abin taƙaici, ta mutu ne sakamakon rashin iskar oxygen.
Brazil ce ƙasar da ta fi yawan masu cutar korona a duniya inda fiye da mutum 219,000 suka mutu.
A Manaus, tsarin lafiyar birnin ya taɓarɓare har sau biyu a lokacin annobar cutar korona, sannan yawan mace-mace ya ruɓanya daga tsakanin watan Disamba zuwa Janairu, abin da ya sa ƙaramar hukumar ta sanar da shirin samar da sabbin ƙaburbura har 22,000.
Amma kuma asibitoci da dakunan shan maganin kasar ba su kadai ne ke fuskantar matsalar karancin samun iskar ta oxygen ba.
A kasar Mexico, inda mutane fiye da 152,000 suka mutu a annobar, akwai rahotannin cewa ɓarayi na sace tukwanen iskar ta oxygen din daga asibitoci da dakunan shan magani.
Ga misali, an cafke wasu mutane biyu bayan sace wata babbar motar daukar kaya maƙare da tukwanen iskar ta oxygen din da aka sace a arewacin birnin Mexico.
A baya cikin wannan watan, wasu faya-fayen bidiyo da suka bayyana, sun musanta ƙarancin isakar ta oxygen a aƙalla asibitoci biyu a kasar Masar.
A daya daga ciki, wani mutum ya naɗi faifen bidiyon wasu gadaje da aka lulluɓe da barguna a asibitin al-Husseiniya a arewa maso gabashin yankin mulki na Sharqia, kana ya yi ikirarin cewa ''duk waɗanda ke sashen lura da marasa lafiya na gaggawa a asibitin sun mutu''.
Mahukuntan kasar Masar sun ce marasa lafiya hudu ne suka mutu saboda tsananin kamuwa da cutar - ba saboda karancin iskar ta oxygen ba - kana sun musanta cewa akwai matsaloli wajen samarwa.
Amma kuma rahotanni masu kama da haka a kasashe da dama sun yi nuni da matsin lamba kan gwamnatoci su samar da wannan muhimmiyar hanya ta ceton rayuka.
'Matsalar karancin iskar oxygen'
Kamar yadda kungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana, daya a cikin mutane biyar da suka kamu da cutar korona na bukatar iskar oxygen.
A yanayi matsananci, yana kai wa har mutane uku cikin biyar.
Hukumar ta ce ba ta da cikakkun bayanai da aka tattara daga kasashe, amma ta ce wasu asibitoci sun shaida karuwar bukatar samun karin iskar ta oxygen a tsakanin sau biyar zuwa bakwai saboda karuwar wadanda suka kamu da cutar mai tsanani.
Kungiyar PATH, mai taimaka wa gwamnatoci wajen yaki da annobar, ta gano cewa bukatar isakar ta oxygen ''ta karu matuka'' a shekarar 2020, saboda karuwar yawan adadin wadanda suka kamu da matsanancin sarkewar numfashi - karancin oxygen a cikin jininsu - saboda cutar ta korona.
"Muna bukatar yin tunani game da iskar oxygen kamar yadda muke tunani game da samar da wutar lantarki, da ruwa da sauran abubuwa na buƙatu,'' in ji Lisa Smith, ta kungiyar ta PATH.
"Wannan ba zai zama abu da za mu damu da shi idan abubuwa suka ɓaci ba, saboda lokacin da abubuwa da suka ɓaci, mutane za su mutu.''
Yanzu haka, ana bukatar tukwanen iskar ta oxyegen kusan miliyan daya da rabi a kullum a fadin kasashe matsakaita da matalauta, don bukatun da suka shafi matsalolin da annobar ta haifar kamar yadda na'urar bin diddigin kan yadda al'amuran samar da iskar ta oxygen din ta nuna.
Na'urar ta shafin intanet, wacce ke taimaka wa wajen ƙididdigar ma'aunin ƙalubalen da ke gaban mahukunta, cibiyar lura da cututtukan da suka shafi numfashi mai alaƙa da cutar korona da hadin gwiwa da kungiyar PATH da ta 'Every Breath Counts', da ke fafutikar ganin kasashe masu ƙaramin ƙarfi sun samu iskar ta oxygen ne suka ƙirƙiro ta.
"Akwai matsalar samun iskar oxygen a fadin yankin Kudu da Saharar Afirka da Asia da Latin Amurka,'' in ji Leith Greenslade, daga kungiyar 'Every Breath Counts'."
Kasashen ba sa nuna muhimmanci kan ko iskar oxygen nawa wadanda suka kamu da cutar korona ke bukata: wasu na bukatar goma, sau 20 fiye da yadda sauran marasa lafiyar da ke bukatar oxygen din za su nema."
Kamar yadda na'urar bin diddigin ta gano, ƙasar Brazil ta kasance daya daga cikin kasashen mafi fuskantar ƙaruwar buƙatar iskar ta oxygen tun a cikin watan Nuwamba - tana buƙatar tukwanen iskar oxygen aƙalla 340,000 a kowace rana don masu fama da cutar da korona.
Bayan da matsala a jihar Manaus ta kai maƙura, an aike da gudumawar iskar oxygen daga sauran jihohin da tsallaken kan iyakar kasar Venezuela.
Amma a jihar Jesem Orellana,wani kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa a kungiyar Oswaldo Cruz Foundation, ya shaida wa BBC hadarin karancin zai ci gaba, kuma karuwar mabukatan ce ta haifar da haka.
A sauran kasashe masu tasowa, kamar Indiya, akwai ƙaruwar kashi 60 bisa 100 na bukatar iskar ta oxygen tsakanin watan Afrilu zuwa Yuli, kana ƙaruwar kashi 84 bisa dari tsakanin watan Yuli zuwa Satumba.
Adamu Isah daga kungiya Save the Children a Najeriya - inda ake buƙatar karin tukwanen iskar oxyegen 10,000 a ko wace rana - ya bayyana ''"buƙatar ƙarin oxygen din da cewa ƙarancin ya karaɗe kusan duka sassan kasar''.
A Afirka Ta Kudu, na'urar bin diddigin ta ƙididdiga cewa kasar na buƙatar ƙarin tukwanen iskar oxygen 100,000 a kowace rana.
Ministan lafiya Zweli Mkhize y ace gwamnati ''na iya bakin kokarinta ta tabbatar an samar da isassun tukwanen iskar oxygen din'' kana ta nemi ƙari daga kamfanoni.
Daga ina ake samun iskar oxygen ta marasa lafiya?
Kamar yadda kungiyar PATH ta bayyana, iskar oxyegen ta marasa lafiya na samar da kashi 5 zuwa 10 bisar dari kacal na iskar oxygen din da ake samarwa a duniya. Ana amfani da sauran ne a masana'antu da dama, kamar na haƙar ma'adinai, da na hada sinadarai da na magunguna.
Ana samar da ita da daman gaske a masana'antu kuma ana samar wa da asibitoci ta hanyoyi biyu: ko a cikin tankunan iskar mai ruwa, ko kuma a cikin tukwanen iskar gas da ke ɗaukar adadi marar yawa.
Oxygen mai ruwa ita ce ta fi saukin kudi da kuma hanyar fasaha mafi inganci, amma kuma asibitoci na buƙatar su samu kayan aikin da suka dace ta yadda za su iya tura iskar ta cikin bututai zuwa gefen gadon marar lafiya.
An fi samun irin wannan a kasashen da suka ci gaba kamar Amurka da Turai.
Tukwanen na da buƙatar bututai kuma za a iya kai wa dakunan shan magani ba tare da wasu kayan aiki masu wahala ba.
Amma kuma, rarraba su kadan-kadan na nufin babu kashe kudi sosau, haka kuma kasancewa masu nauyi wajen tafiya da su ko dauka, wanda kuma ke tattare da hadarin gurabcewa.
"Wasu kasashen sun dogara kacokan kan shigowa da iskar oxygen daga waje zuwa asibitoci ta hanyar amfani da tukwanen a kan hanyoyi masu gargada da kuma dogon zango,'' in ji Farfesa Mike English, wanda ya taimaka wajen jagorantar sashen ayyukan kiwon lafiya a cibiyar bincike ta KEMRI-Wellcome a birnin Nairobi, wadda ke da hadin gwiwa da Jami'ar Oxford a Birtaniya.
"Wannan babbar matsala ce kuma adadin da ake bukata na da wahala wajen samarwa.''
Ya ce samar da iskar ta oxygen matsala ce a Afirka kafin barkewar annobar.
"Kafin annobar Covid, akwai lokuta da dama da ko da a manyan asibitoci karamin yaro marar lafiya, ko jariri ko kuma wani wanda ke bukatar taimakon gaggawa, ba za su iya samun iskar oxygen din da suke bukata ba,'' ya bayyana.
"Korona ta kara fito da matsalar a fili saboda yanzu tana shafar manya su ma.''
Iskar oxygen 'bayan tunani'
Tun a shekarar 2017 ne kungiyar lafiya ta duniya WHO na daukar iskar oxygen a matsayin muhimmin magani.
Amma kuma Ms Smith ta ce ana daukar samar da ita a matsayin ''bayan tunani'' - tare da bayyana matsalar da cewa '' batun bangaren kiwon lafiya ne'' mai kunshe da da ''abubuwa da dama''da ake bukata su yi daidai wajen shawo kan matsalar.
Kowane ƙwararre da ya yi hira da BBC ya fadi abu iri daya, da suka hada da bukatar kayan aiki, horarwa da kuma shawo kan matsaloli na tsawon lokaci a sharhinsu.
Asibitoci ga misali, za su iya gina masana'antar samar da iskar ta oxygen da za a iya samu a ko da yaushe.
Amma kuma suna da tsada, suna bukatar wadatuwar wutar lantarki da kuma ƙwarewa da kuma ƙwararrun injiniyoyi masu lura, wanda da lallai ba ne a samu in ji Farfesa English.
"Kamar sauran bayyanannun abubuwa 'masu sauƙin kafawa', masana'antun sarrafa iskar oxygen na bukatar duk wani bangare na kiwon lafiya ya zamanto yana aiki,'' ya kara cewa.
A kasar Malawi, akwai irin wadannan masana'antu uku - a babban asibiti na Blantyre Queen Elizabeth, da asibitin Nkhata Bay da kuma babban asibitin Kamuzu a birnin Lilongwe.
Saboda gina su, kasar ta bukaci shigo da kayayyaki daga Afirka Ta Kudu, in ji Grycian Mussa, babban injiniya a asibitin.
"Lokacin kullen korona, ya kasance matsala babba, saboda komai na zuwa ne daga Afirka Ta Kudu, kuma Afirka Ta Kudu na cikin kullen korona, kana Malawi ma na cikin kullen,'' ya bayyana.
"Ina ga lokaci ya yi da kasashen Afirka za su horar da injiniyoyi a kasashenmu, kana mu duba yadda za mu riƙe kanmu. In ba haka ba, haka za mu ci gaba da dogara da wasu kasashen wajen neman taimako a tsakiyar wannan annoba."
Bukatar horar da injiniyoyin an taɓa yin shi a baya a Najeriya daga wani kwamitin samar da iskar oxygen da aka kafa tare da tallafi kungiyoyi masu zaman kansu da wasu hukumomi don bayar da shawarwari kan amfani da isakar oxygen din, in ji Malam Isah.
"Ko da ka kawo duka iskar oxygen din dake duniya, idan ba ka horar da mutane kan yadda za su yi amfani da it aba, kana bata lokacinka ne,'' ya ce.
Na'urorin auna mitocin oxygen din, da ke maƙale a jikin yatsa don auna yawan iskar da ke cikin jini, hanya ce mai sauƙi ta lura da marasa lafiyar idan aka horar da mutane yadda za a iya amfani da su. Amma har yanzu akwai batun matsalar samar da oxygen din.
"Ko da irin wannan, da mafi sauƙi ce wajen sarrafawa da kuma samarwa, ba a cika samu a kasashe masu ƙananan ƙarfi ba a Afirka," in ji Farfesa English.
Kungiyar Lafiya Ta Duniya WHO, ta rarraba wasu kimanin 16,000 a kasashen duniya lokacin ɓarkewar annobar amma ta yi gargaɗin cewa "ba su wadata ba ga marasa lafiyar da cutar ta yi musu tsanani da ke bukatar karin oxyegen din''.
Ko kafin ɓarkewar annobar, hukumomi kamar su UNICEF sun yi ta rarraba iskar ta oxygen tare da zuba jari a masana'antun sarrafa isakar ta oxygen a asibitoci a kasashen da suka ci gaba don yaƙar cututtuka irin su sarƙewar numfashi kamar 'pneumonia' - "mai kisan mummuke" da aka ƙiyasta na kashe yara kimanin 800,000 a kowace shekara.
Yanzu akwai damuwa, da kungiyoyi kamar Save the Children da ƙwararru irin Farfesa English suka yi la'akari cewa matsalar da cutar korona ta haifar kan samar da iskar ta oxygen ka iya yin nakasu ga lura da sauran cututtuka.
"Oxygen na taimakawa kan matsaloli da dama, daga jarirai da ke buƙatar oxygen zuwa wani wanda ke da matsanancinin ciwon huhu a tsakanin masu yawan shekaru,'' in ji Ms Greenslade.
"Cutar korona ta nuna mana muhimmancin da ke tattare a kasashen da babu alluran rigakafi, babu magani. Ya kuma kai ga cewa ko mun samu oxygen ko bamu samu ba, ko mu mutu ko mu rayi.''
*Karin rahoto daga Vinicius Lemos a Sao Paulo