Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku Tare da Sheikh Bashir Tahir Usman Bauchi
Babu shakka haddar Al-Kur'ani mai girma abu ne da sai wanda Allah ya zaɓa yake bai wa, Malam Bashir Tahir na daga cikin wadanda aka zaɓa.
Kuma a lokacin da ya haddace al-Kur'ani an cika da mamaki domin kuwa yana ɗan shekara 11 da haihuwa ya samu nasarar hakan a shekarar 1986.
A Maiduguri a Jihar Borno da ke arewacin Najeriya ya yi karatunsa a tsangayar Gwani ɗan kyallori, shi ne dan auta cikin jerin mutanen da suka je wannan tsangaya a lokacin.
Mutumin Bauchi ne Malam, amma ya yi rayuwarsa mai yawa a Kano domin kuwa anan ya haddace al-Kur'ani tare da tajweedi.
Mahaifinsu ya mayar da su Bauchi daga Kano inda a can ne shi da yayyansa biyu suka rubuta al-Kur'ani, kafin daga bisani a mayar da shi Jihar Kebbi domin yin karatun zaure.
Ya yi karatun ne a hannun marigayi Malam Umaru Ika, wato shugaban malaman yankin Gwandu na wannan lokacin.
Duka littatafan Malikiyya irinsu Iziyya da Ahlari da Ishmawi su Risala da Askari da su Awwali da Thani kamar yadda ake kiransu.
A farkon 1992 aka mayar da shi gida Bauchi a nan ne ya rabu da yayansa wanda aka kai shi Masar domin ci gaba da karatu, shi kuma sai ya shiga Kwalejin Arabiyya ta Alhaji Usman.
Ya fara daga aji biyu na sakandire wanda wannan ne mafarin karatunsa na zamani.
"Dakta Shehul-Hadi yayanmu ne wurinsa muka yi karatun Hadithi da Balaga da Nahwu da karatin duka mazhabobin da ake bi a duniya irinsu Malikiyya da Shafi'iyya da Hambaliyya da dai sauransu, kamar yadda ya bayyana a hirarsa ta musamman da BBC.
Tun yana shekara 23, wato a 1998 ya fara Tafsirin al-Kur'ani mai girma a Jihar Kaduna, wannan kuwa ya biyo bayan maye gurbin Sheik - Hadi da ya yi, wanda aka mayar Abuja domin ci gab da koyar da ilimi.
Karatunsa na Hadithi
Duk da cewa mun tattauna kan gwagwarmayar da ya yi a farkon rayuwarsa har zuwa kusan shekara 23, to amma Malam ya fara karatun Hadithi na ruwaya a hannun Sheik Sharif Saleh.
"A kasar Morocco mahaifina ya haɗa ni da Sheik Sharif Saleh ya ce ga Bashir a sanar da shi ilimin Hadithi, sai Sheik ya ce in je in yi alwala, kuma take aka fara karatun Hadithin."
"Ya fara ne da bayyana mani yadda salsalar hadisan take, daga malamansa da ya karɓa daga hannunsu wadanda cikinsu har da Sheik Maulana Ibrahimu Inyas Rahimahullah, har zuwa kan su Bukhari har tikewa ga Annabi Alaihissalam," in ji Malam Bashir.
Ya fara ne da koyar Hadithin da ke cewa "ku tausayawa waɗanda ke ban ƙasa kuma sai Allah ya tausaya muku".
Tun daga lokacin muke karatun Bukhari, kuma har gobe muna yi.
Ilimin zamani
Ya dauke Malam shekara guda a sakandire domin neman takardun da za su ba shi damar sauya darasi daga bangaren larabci zuwa na turanci, wannan kuma ya faru ne a farkon shekarun 2000.
A 2004 ya samu nasarar shiga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya samu gurbin karatu a sashen nazarin kimiyyar siyasa da huldar diflomasiyya.
A 2008 na kammala digirina na farko kuma na koma gida.
Ba da shi Malam ya ci gaba da gwagwarmayar rayuwa ba, ci gaba ya yi da koyarwa a makarantar Shehinsa, 2008 har zuwa 2013/14 shekarun da ya kwashe kenan yana wannan koyarwa.
A shekarar 2014/15 ne ya tafi Nigerian Defennce Academy ya yi Diflomar gaba da digiri a Public Administration, daga nan kuma ya koma Ahmadu Bello Zaria ya yi digiri na biyu a fannina sashen nazarin kimiyyar siyasa da huldar diflomasiyya, ya sake koma wa ya yi wani digirin a Art of International Studies a NDA.
Na je Malesiya na yi digirin digirgir na kuma fara rubutuna akai, har yanzu ban gama rubutun ba amma ina daf da gamawa.
Rai da buri
Shehi ya ce ya fi son shinkafa a haɗa ta da wake da miya wannan shi ne abincin da ya fi so yaga yana ci.
A wajen wasanni kuwa Shehi ya ce ba shi da farin jini saboda bai iya ba, yayi wasan kwallo ya yi na ninkaya a ruwa da dai sauran wasanni, amma yana da matukar rauni wanda ya ja ake barin shi a baya lokacin wasannin.
Rashin kwarewa a wasannin ya janyo ya koyi rayuwar kaɗaitaka, wanda kuma ya rika amfani da wannan dama yana karatun litattafai da wannan lokaci.
Amma lokacin da ya fi yi wa malam dadi a rayuwarsa lokacin da ya gayawa mahifinsa ya haddace Kur'ani ya dauke shi ya daga shi ya rungume shi sannan ya ba shi kudi kyauta.
Da aka tambaye shi a loakcin da yake karatun Kur'ani wace Sura ce ta fi wahalar da shi sai ya ce "ayar rabon gado ta cikin Suratu Nisa'i. Sai da na san fassarar ayar na iya haddace ta.
Amma na fi jin dadin Suratul Yusufa, saboda na riga sanin ma'anarta.
A hadithi kuma, Hadithin da aka ce "mutum yana tare da abin da yake so".
Sayyadi Bashir ya "Mummunan lokaci a wurina shi ne lokacin da yayanmu Shehul-Hadi ya rasu.
Bani da wani takaici a rayuwa sai dai da zan samu damar komawa rayuwar baya da na ƙara karatu mai matukar yawa."
Iyali
Shehi ya ce yana da iyali da suka kai mata uku da yara goma sha tara 19.
Burin Shehi dai dai yake da na ko wanne musulmi wato ya cika da imani. Ya ce yana fatan ya cika da imani da kuma soyayyar fiyayyen halitta.